Connect with us

RIGAR 'YANCI

Na Yi Nadamar Shan Kwatami Don Murnar Zarcewar Buhari, Cewar Ali Gayu

Published

on

Matashin nan da ya tari aradu da ka, ya sha ruwan kwatami gami da yin birgima da shi, saboda murnar zarcewar Shugaban Najeriya Muhammad Buhari a karo na biyu, wato Ali Gayu, ya nuna nadamarsa kan yadda a ka yi wofi da shi duk da ya sadaukar da lafiyarsa da rayuwarsa, don ya burge masoyan Buhari.
Idan za ku iya tunawa dai, daf da ayyana cewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu nasara a zangonsa na biyu, wani matashi mai suna Ali Muhammad Sani ya fada cikin kwata da shan ruwanta duk dai domin murna da zarcewar Buhari, kana matashin ya yi suna a ciki da wajen kasar nan domin an yada cewar a sakamakon shan kwatamin ya ma mutu.
Ali Gayu ya nuna wannan takaicin nasa ne a zantawarsa da wakilinmu, inda ya shaidar da cewar ya kasance matashin da ya tari aradu da ka wajen sallama wa lafiyarsa da lokacinsa don shan kwata dukka domin murnar nasarar Buhari.
Matashin mai shekaru 23 a duniya ce, da gwamnatin Buhari tana damuwa da masoyanta da ta jawo shi ka jika da yi masa goma ta arziki, amma ya ce har zuwa yanzu shiru kake ji kamar an shuka dusa.
A cewar shi, “Ka san dai nine mai suna Muhammad Aliyu Sani wanda aka fi sani da Ali Gayu, daga unguwar Doya a cikin garin Bauchi. nine wanda aka yi ta ce-ce-ku-ce a kaina a lokacin da na sha kwata don murna da zarcewar shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu. Na sha suka da zagi da yabo a lokacin da na sha kwatami da yin burgima a cikin kwatamin nan, na kau da kaina domin soyayyar da nake yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ban damu da matsalar da ta za ta biyu bayan abun da na yi ba.
“Babban abun da ke akwai ma shine na saida raina da lafiyata. A lokacin an yi ta korafin na mutu-na-mutu a sakamakon soyayyar Muhammadu Buhari, na sha kwata wanda kowa ya san kwata najasa ne wanda cuta ka iya kamani, amma cikin ikon Allah babu abun da ya sameni zuwa ga wannan lokacin,”
“Amma abun da ya bani mamaki ya dameni shine har zuwa yanzu wannan gwamnatin da na yi wannan babbar aikin don ita kamar ba ta san yanayin abun da na yi ba, ko ba wanda ya damu da lafiyata domin babu wanda ya tuntubeni ya ji ko ya koshin lafiyata yake ba.
“Wannan abun da muka yi, yau da mun samu wani alheri na tabbatar wasu ma za su mora daga garemu domin akwai matasa sosai wadanda suke zaune basu da aiyukan yi, da ya dace mu a fanninmu mu taimaka musu ba ma sai an je ga wani fanni ba,” A cewar Ali Gayu.
Ya ce, kamar yadda kafafen watsa labarai na cikin kasa da wajen kasa suka tuntubeshi kan wannan babbar aikin da ya yi a wancan lokacin, yana mai shaida musu cewar har zuwa yanzu bai ga ribar aikin da ya yi ba tukun; don haka ne yake mai kokawa gwamnatin Buhari da ta dubi wadanda suka mata hidima da idon basira don kyautata rayuwarsu da lafiyarsu a kowani lokaci.
A cewar Gayu, “Matasa muna neman agaji, muna son a kula da rayuwarmu domin ta inganta,” Kamar yadda ya ce.
Ali Gayu ya shaida cewar har zuwa yanzu shi masoyin Buhari ne, don haka ne ya kirayi shugaban kasa Buhari ya kula da masoyansa na hakika, “Ni abun da na tsammaci gwamnatin Buhari za ta yi min shine ta hadani da shugaban kasa Buhari mu ga juna. A yanzu babban burina na rayuwa shine na kasance na halarci wurin rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu na ganshi ya ganni na tabbatar da cewar hakan ya zama min abun alhafari a rayuwata,” A cewar shi.
Ya ce, idan har bayan kokensa gwamnatin Buhari ba ta kula shi ba; to tabbas zai dauki gwamnatin a matsayin gwamnatin da ta mance da masoyanta, “Idan har aka gama shagulgular bikin rantsar da Buhari ba tare da an ma san muna yi ba; to zan dauki wannan lamarin a matsayin gwamnati ba ta damu da kiwon lafiya da yanayin masoyanta ba, tun da ga wani dan Nijeriya da ya sadaukar da lafiyarsa amma ba ta damu da ta bibiyi lafiyarsa da rayuwarsa ba, nine fa aka ce na mutu, na yi kaza na yi kaza dukka don abun da na yi wa Buhari. Yanzu kamatuwa yayi a har zuwa yanzu a kyale ni? Ka ga dole ne kawo damuwa na sanya a raina,” A cewar Ali Gayu.
LEADERSHIP A YAU ta nakalto cewar Ali Gayu ya jawo zafafan muhawara musamman a kafafen sadarwar zamani tun lokacin da labarin ya sha kwata da yin wanka da kwatami domin zarcewar Buhari, inda wasu suka yi ta zaginsa da daukarsa a matsayin marar hankali, a gefe guda kuma wasu suka yi ta nuna jin dadinsu da yabonsu kan abun da ya yi.
A bisa girman abun da ya yi, kafafen sadarwa da daman gaske sun rawaito wannan aikin da yayi a ranar da ya ji cewar Buhari ya samu nasara akan Atiku Abubakar, a cikin haka har wata kafar sadarwa ta yade cewar ya mutu a samakaon cutar da ya sha a cikin kwatamin.
Matashin dai yanzu ya ce zai zura ido ya ga shin gwamnatin Buhari za ta kuma waiwayeshi ko yaya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: