Connect with us

KASUWANCI

Shell Ya Lashi Takobin Kin Kara Koma Wa Yankin Ogoni Hakar Mai

Published

on

Daga Abubakar Abba

Kamfanin Shell da ake aikinsa a Nijeriya ya sanar da cewar, baida wani shirin sake dawo yankin Ogoni don ci gaba da hakara danyen mai.
Janar Manaja na kamfanin Shell Mista Igo Weli ne ya sanar da hakana a ranar Juam’ar data gabata a a garin Fatakwal a lokacin kaddamar da shirin gasara kamfanin ta shekarar 2019.
Acewar Janar Manaja na kamfanin Shell Mista Igo Weli, irin barazanar da ake yiwa kamfannin a yankin ta isa skamfanin ya dakatar da dukkan ayyukansa a yankin na Ogoni.
Yaci gaba da cewa, tun loakcin da kamfanin na Shell ya dakatar da sarrafa danyen mai a yankin na Ogoni tun a shekarar 1993.
Manaja na kamfanin Shell Mista Igo Weli ya jadda da cewar, kamfanin na Shell ba zai kara komawa yankin na Ogni don gudanar da ayyukan sa ba.
Ya kuma karayata cewar da ake yi kamfanin na Sheal ya dauki nauyin wani kamfani don ci gaba da hakara man a yankin na Ogoni, ida yace, ci gaba da hakara man a yankin na Ogoni hukumar NPDC ce ta cigaba da yi tun a shekarar a shekarar 2012.
Manaja na kamfanin Shell Mista Igo Weli yaci gaba da cewa, kamfanin na Shell baiuda wata kara sha’awara sake komawa yankin na Ognoi don ci gaba da hakara man, inda yace bamu gudanar da wani aikinsa a yankin na Ogoni shekarar 1993.
Acewar sa, kamfanin na Shell ya tafka asara iri-iri a yankin na Ogoni wacce kusan ba ta misalatuwa.
Manaja na kamfanin Shell Mista Igo Weli yace, babu wani kamfanin mai daga kasar waje dai da ke da ra’ayin yin kasuwanci a yankin na Ogni.
A cewarsa, “ Babu wani gaskiya da ake cewa mun dauki nauyin wani kamfani don ya dinga hakara mai a yankin na Ogoni da sunna kamfanin mu na Shell.”
Manaja na kamfanin Shell Mista Igo Weli yace tun a shakarar 2012, aikin na hakara mai a yankin na Ogoni aka dorawa NPDC ragamar ci gaba da hakara.
A karashe Manaja na kamfanin Shell Mista Igo Weli yace, kamfanin na Shell ba zai taba daukar nauyin wani kamfani don ci gaba da hakara ma a a yankin na Ogoni ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: