Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Soja Da Farar Hula Uku Sun Shiga Hannu Bisa Laifin Yin Garkuwa Da Mutane

Published

on

Rundunar ’yan sandar Jihar Anambra ta samu nasarar cafke wani sojan Nijeriya tare da wasu mutum uku, bisa zagin su da a ke yi na yin garkuwa da wani saurayi a yankin Ekwulobia cikin karamar hukumar Aguata ta jihar. A cewar rundunar ‘yan sanda sojan mai suna Ojiegbe Obinna, yana gudanar da aiki ne a cikin bataliyar ta 101 na sojin Nijeriya da ke Maiduguri ta Jihar Borno. An bayyana cewa, sojan tare da mutum biyu, Obasi Peter da kuma Benjamin Nicholas, sun yi garkuwa da wani matashi mai suna Uchenna Ezeonu da ke kauyen Omeke cikin yankin Ekwulobia, inda su ka kai shi wani boyayyan wuri.
Majiyarmu ta ruwato cewa, ‘yan sanda sun samu nasarar cafke wadanda a ke zargi ne a wani daji kusa da kasuwar Uyo-Eke, a wani sintirin hadin gwiwa ‘Operation Puff Adder’.
Da ya ke tabbatar da kamen, kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Haruna Mohammed, ya bayyana cewa, an samu nasarar kobotar da wanda su ka yi garkuwa da shi mai suna Ezeonu. Kakakin rundunar ‘yan sanda ya ce, “ an kira ’yan sanda zuwa a hanyar Isuofia da ke cikin karamar hukumar Aguata ta Jihar Anambra, ranar 24 ga watan Mayu, 2019 da misalin karfe 11 na safe cewa, mutum uku sanye da inifon din sojoji sun yi garkuwa da wani matashi mai suna Uchenna Ezeon, da ke kauyen Omeke cikin yankin Ekwulobia, a mahadar hanya da ke Ekwulobia, inda su ka gudu da shi zuwa wani boyayyan wuri.
“Bayan samun wannan kira, nan take gamayyar tawagar ‘yan sanda sun isa wurin da lamarin ya auku, inda su ka mamaye yankin tare da bincika dajin da ke kusa da kasuwar Uyo-eke. A wannan lamari ne, a ka samu nasarar cafke mutum uku wadanda a ke zargin sun yi garkuwa da matashin, wadanda a ke zargi dai su ne, Ojiegbe Obinna, Obasi Peter, Benjamin Nicholas da kuma Okoye Ugochukwu, dukkan su sanye da inifon din soja.”
Mohammed ya kara da cewa, “bincike ya bayyana cewa, daya daga cikin wadanda a ke zargin mai suna Ojiegbe Obinna, sojan Nijeriya ne da ke gudanar da aiki a bataliyar na 101 a Maiduguri cikin Jihar Borno.” Ya ce, an mika Ojiedbe ga rundunar sojin Nijeriya da ke garin Onitsha, domin gudanar da bincike, yayin da sauran mutum biyun wadanda a ka cafke sanye da inifon din soja, sojojin bogi ne.
Kakakin rundunar ‘yan sandar ya ce, ana cigaba da gudanar da bincike ta yadda za a samu nasarar cafke sauran wadanda a ke zargin, za a gurfanar da wadanda a ke zargin a gaban kuliya idan an kammala bincike.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: