Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Sanda Sun Damke ’Yan Ta’adda 43 A Bauchi

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Bauchi ta bayyana cewa, ta samu nasarar damke mutum 43 wadanda a ke zargi da ta’addanci wadanda su ka hada da yin garkuwa da mutane, fashi da makami da dai sauran su, tun lokacin da saban kwamishinan ‘yan sandar jihar Habu Sani ya fara aiki a mako ku da su ka gabata. Kwamishinan ya bayyana hakan ne a cikin bayaninsa na ranar Asabar lokacin da ya ke kaddamar da saban dabarun ‘yan sanda na ‘Sectoral Community Policing’, domin karfafa tsaro a jihar.
Ya bayyana cewa, a cikin mutum 43 wadanda a ke zargin, an yanke wa mutum takwas hukunci, yayin da sauran 35 su ke jiran hukunci. Sani ya kara da cewa, “yana da muhimmanci a samar da wannan sabon tsari, an samu nasarar damke ‘yan ta’adda da dama a cikin wannan jihar. “An damke mutu 26 wadanda a ke zargi da laifuka da dama kamar su sara-suka, kashe-kashe a jihar, mallakar dalar bogi, tuki ba tare da lasisi ba da kuma mallakar muyagun makamai. “An yanke wa mutum takwas hukunci a kotu, yayin da sauran mutum 35 su ke hannun ‘yan sanda ana gudanar da bincike.”
Ya kara da cewa, an samu nasarar kwato karamar bindiga kirar gida guda tare da harsasa guda shida, adduna guda 15, babur guda, daurin tabar wiwi guda 40, fakitin muyagun kwaya guda 196, kwalban kodin 903 da kuma jabun dala 100 daga hannun wadanda a ke zargi. Kwamishinan ‘yan sandar ya ce, sabun tsarin ‘yan sanda na ‘sectorisation of community policing’ ya na da matukar mahimmanci wajen tabbatar da tsaran mutunen kowani yanki.
A cikin bayanin nasa, basaraken Jihar Bauchi, Nuru Jumba, ya yaba wa Sani da kafa wannan sabon dubarun tsaro, ya bayyana cewa, mutanen kowani yanki su ya kamata su fara tunkarar duk wani aikin ta’addanci.
Da ya ke bayani a madadin shugaban ‘yan kungiyar sa-kai na yankin Nufawa ta Jihar Bauchi, Almustapha Maidawa, ya bayyana cewa kungiyarsa za ta hada kai da ‘yan sanda wajen gudanar da sintiri a kan ‘yan ta’adda a garin Bauchi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: