Connect with us

KASUWANCI

NNPC Ta Tura Naira Tiriliyan 26 Asusun Tarayya A 2018

Published

on

Kamfanin NNPC yace ya sauke nauyin dake kansa na tura naira tiriliyan 1.26 a cikin Asusun tarayya a shekarar 2018 sabanin naira tiriliyan 1.22 da kamfanin ya yi niyar tsanyawa a cikin kasafin kudi na shekarar 2018, inda aka samu rarar naira biliyan 41.
Manajin Darakta na kamfanin na NNPC Mista Godwin Okonkwo ne ya sanar da hakan a lokacin da ya wakilici Manajin Daraktan rukunonin kamafanin Dakta Maikanti Baru a gaban karamin kwamitin Majalisar Wakilai da yake ci gaba da gudanar da bincike akan kin tura kudi da kwamitin ke zargin kamfanin bai tura a cikin asusun Gwamantin Tarayya ba daga watan Yulin shekarar 2017 zuwa watan Disambar shekarar 2018.
Wannnan bayanin wanda yana kunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawun kamfanin na NNPC Mista Ndu
Ughamadu ya fitar a babban birnin tarayyar Abuja, sanarwar ta ruwaito Dakta Maikanti Baru yace, sai dai gangunan (mbpd) miliyan 2.3 a kullum aka sanya ake kuma tsimayi a cimin kasafin kudin shekarar 2018 ko kuma daga mbpd 1.9 zuwa mbpd 1.89.
Shugaban rukunonin kamfanin na NNPC Dakta Maikanti Baru ya zayyana hanyoyi biyu da kamfanin na NNPC yake tura kudi zuwa cikin asusun na Gwamnatin Tarayya sun hadada, ribar danyen mai da aka sayar ds kudin ds aka karbo na hadakar JB dana danyen mai da aka sayar a cikin Nijeriya wadanda dukkan su an tura su zuwa ga asusun na Gwamnatin Tarayya.
A cewar Dakta Maikanti Baru, mahukuntan kamfanin na NNPC na yanzu, suna tabbatar da bayar da tasu gudunmawar wajen sarrfa danyen mai da iskar gas don gujewa mai-maita aikata kura-kuran da suma auku a baya.
A cewar Dakta Maikati Baru, “ A yanzu muna kara farfadowa ne domin kamfanin na NNPC a yanzu yana kan turbar data dace, musamman wajen tarawa Gwamnatin Tarayya kudin shiga.
Dakata Maikanti Baru yaci gaba da cewa, kamfanin na NNPC baya yin wani jinkiri wajen tura kudi zuwa ga asusun Gwamnatin Tarayya.
Manajin Darakta na Kamfanini rukunonin na NNPC Dakta Maikanti Baru ya kuma yi watsi da zarge-zargen da kwamishinonin kudi na kasar nan sukayi na cewar kamfankn na NNPC bai tura kudi a cikin asusun na Gwamnatin Tarayya ba.
A cewar Dakta Maikanti Baru, jarin da aka zuba a fannin mai da iskar gas, sai ya dauki lokaci sosai sannan yake nuna, inda ya kara da cewa, idan kamfanin na NNPC ya gaza sauke nauyin da aka dora masa na zuba jari a fannin, babu wata sauran shiya da kuma za’a rabar ga dsukacin matakan gwamnati uku dake kasar nan.
Da ya ke bayar da amasa akan tambayar ko kamfanin na NNPC a shekatar 2018 ya yi bincike akan asusun kamfanin, Dakta Maikanti Baru ya sanar da cewa, binciken asusun da akayi a shekarar 2018 zai zama a shirye a wata mai zuwa, inda ya kara da cewa, kamfanin na NNPC, tuni ya kammala yin bincike akan asusun da ba’a gudanar da bincike akan shi ba.
Shugaban rukunonin kamfanin na NNPC Dakta Maikanti Baru ya kuma danganta jinkirin da aka samau akan wasu hadakar ta JB akan jiran su gabatar da kikarin da su ka yi a cikin kasafin kudin su na shekarar 2018.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban karamin kwamitin Majalissr Chukwuka Onyema Wilfred ya jinjinawa Dakta Maikanti Baru akan bayar da amsar da ya yi akan dukkan tambayoyin da kwamitin ya gabatar masa, inda ya yi nuni da cewar, hakan ya taimaka matuka wajen kawar da zarge-zargen kin tura kudin da ake yiwa kamfanin na NNPC.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!