Connect with us

KASUWANCI

Share Dagwalon Yankin Ogoni: Gwamnatin Tarayya Ta Kara Bai Wa ’Yan Kwangila Hudu Aikin

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewar, ta kara mikawa yan kwangila hudu aikin share dagawalon dake a cikin wasu alumomin dake a yankin Ogoni.
Jami’in aikin Daka Marbin Dekil HYPREP dake a karkashin Ma’aikatar kula da muhalli ne ya sanar da hakan a lokacin taron karin mika ragara aikina yankunan Alode Eleme da Eleme dake a cikin jihar Ribas.
Ya zayyana kamfanonin da suka hadada, R.D.K Enbironmental Ecological Solutions, Abondale Serbices and Supplies Ltd, Giolee Global Resources da kuma kamfanin New Line West African.
A cewarsa, Kimanin hurare 21 da dagwalo ya shafa aka migawa yan kwangilar a kashin farko na share dagwalon.
Ya ci gaba da cewa, sai da aka tantance yan kwangilar sosai don a tabbatar da kwarewar su kafin a basu kwangilar.
Ya kara da cewa, “Muna jiran muga yan kwangilar sun yi amfani da kwarewar su don gudanar da aikin na share dagwalon a yankin na Ogoni.”
A cewarsa,“ Kamfanoni biyar Majalisar zantarwa ta amince dasu a yankin Eleme, inda ya kara da cewa, akwai lots 4, 7, 8 da 16.”
Ya sanar da cewa, sai na yanki na biyar da Majalisar zartarwa ta amince dashi wanda daga baya za’a mikawa wani dan kwangilar.
Ya kara da cewa, amincewa da aikin gurare biyar da Gwamnatin Tarayyar hakan ya nuna jajircewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na son gaggauta wanzar da rahoton UNEP.
Ya kara da cewa, dukkan kayan da ake bukata don gudanar da aikin an tanade su don a tabbatar da cin nasarar wanzar da aikin na share dagwalon na yankin na Ogoni.
A cewarsa, aikin zai samar da damarmaki ga tattalin arzikin alumomin yankin na Ogoni.
Ya kara da cewa, “Muna kira ga alummar yankin na Ogoni dasu yi amfani da wannan damar don su ci gaba da zama a cikin zaman lafiya.”
Shi ma daya daga cikin wakilan masu zantarwa na HYPREP Dakta Peter Medee, yaja kunnen masu hana ruwa gudu su guji yin donkan wani kokarin yiwa aikin zagon kasa, inda ya ce domin Gwamnatin Tarayya bazata lamunci hakan ba, inda ya kuma jaddada cewar, ana son a kammala aikin a bisa nauyin da aka dorawa HYPREP.
A cewar Dakta Peter Medee, an ware isassun kudi don gunarda aikin na share dagwalon na yankin Ogoni, inda ya bukaci da aci gaba da basu goyon baya don a cimma nasarar aikin.
Shi ma a nasa jawabin, Sarki Godwin Gininwa, kuma Shugaban Majalisar koli ta sarakunan gargajiya dake yankin na Ogoni ya baiwa yan kwangilar tabbacin basu goyon bayan da ya dace da kuma hadin kan alummar dake yankin na Ogoni.
A karshe Sarki Godwin Gininwa, kuma Shugaban Majalisar koli ta sarakunan gargajiya dake yankin ya kuma yi kira ga yan kwangilar dasu daukin yan yankin a ayyukan da za’a yi a yankin kamar yadda rahoton UNEP.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!