Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matar Malamin Jami’ar Jihar Neja Delta

Published

on

A ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da matar malamin jami’ar Jihar Neja Delta, a yankin Gbarantoru da ke Yenagoa. Wata majiya daga yankin ta bayyana wa kamfanin dillanci da barai na Nijeriya cewa, lamarin ya afku ne a narar Lahadi, inda ‘yan bindigar su ke ta harbi a sama domin a san da zuwan su. An bayar da rahoton cewa, ‘yan bindigar sun shiga yankin ne ta kogin Nun, inda su ka yi amfani da kwalekwale kafin su ka isa gidan malamin jami’an mai suna Dakta Charles.
Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, sun kuskure wanda su ka hara ne, inda nan ta ke su ka yi awon gaba da matar malamin jami’ar a cikin kwalekwale. Mazaunin yankin ya kara da cewa, bayan wasu lokuta, matasa daga yankin sun yi cincirindo a wurin da lamarin ya faru.
Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Bayelsa, Mista Asinim Butsawat, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya bayyana cewa, rundunarsa ta na sane da lamarin, sanna ta na farautar masu garkuwar. “Gaskiya ne, na samu labarin faruwar lamarin sannan ‘yan sanda su na gudanar da bincike ta yadda za a samu nasarar cafke wadanda su ka aikata lamarin tare da kokarin kubutar da wacce su ka yi garkuwa da ita,” in ji Butswat.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: