Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Sanda Sun Cefke ‘Yan Kungiyar Asiri Biyu A Legas

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Legasa ta samu nasarar cafke mutum biyu wadanda a ke kyautata zaton ‘yan kungiyar asiri ne, ma su suna Balogun Oluwadamilare, dan shekara 24 da kuma Badmus Idris mai shekaru 23, a wajen bikin yaye daliban kwalejin kimiyya da ke Yaba. Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Legas, DSP Bala Elkana, shi ya bayyana hakan, inda ya bayyana cewa, a cafke wadanda a ke zargin ne da karamar bindiga guda, harsasai guda hudu da kuma manyan bindigogi guda uku.
“A ranar 21 ga watan Mayu da misalin karfe hudu na yamma ne, ofishin ‘yan sanda da ke garin Yaba ya samu kiran wayar salula cewa, an ga bullowar wasu ‘yan bindiga wadanda a ke kyautata zaton ‘yan kungiyar asiri ne a wajen taron yaye daliban na kwalejin kimiyya da ke Yaba. “Nan ta ke tawagar ‘yan sanda su ka isa harabar makarantar domin gudanar da bincike. “A nan ne mu ka samu nasarar cafke mutum biyu wadanda a ke zargi. An kwato karamar bindiga guda daya tare da harsasai guda uku da kuma manyan bindigogi guda hudu daga hannun wadanda a ke zargi. “Ana cigaba da guda gudanar da bincike, sannan idan a ka kammala za a gurfanar da wadanda a ke zargin a gaban kotu,” in ji shi.
Haka kuma a cikin makon da ta gabata, an samu nasarar cafke wadanda a ke zargin su na yin fashi da cin kosan ababan hawa a Jihar Legas, a wani sintiri na musamman wanda kwamishinan ‘yan sandar jihar Zubair Muazu, ya kaddamar domin dakile ayyukan masu fashi a bakin hanyar jihar. Wannan ya kai ga cafke mutu 10 wadanda a ke zargin ‘yan fashi ne tare da kwato manyan bindigogi da harsasai.
“A ranar 24 ga watan Mayu da misalin karfe 5,30 na yamma, tawagar ‘yan sanda daga Ketu sun dakile yunkurin fashi da makami a tashar Kosofe. “An samu nasarar cafke shugaban ‘yan fashin mai suna Gabazine tare da ‘yan tawagarsa mutum biyu. An gano wayar salula kirar ‘Samsung’ guda daya wanda a ka sace daga hannun maishi, inda a ka mika ma sa wayarsa.
“A ranar 25 ga watan Mayu, tawagar ‘yan sandar ta cafke mutum biyu wadanda a ke zargin masu yin fashi ne a bakin hanya a wannan wuri, lokacin da su ke yunkurin yi wa masu motoci fashi. “An kwato wuka da karamar bindiga daga hannun wadanda a ke zargi. “A wannan rana da misalin karfe 12 na rama, tawagar ‘yan sanda sun gudanar da sintiri a tashar Ketu, inda ya yi samadiyyar cafke mutum biyu wadanda a ke zargin ‘yan fashin kan hanya ne, Ayomide Ayobami da kuma Taye Onofowokan, dukkan su suna zaune ne a yankin Agboyi Ketu.
“An gano karamar bindiga guda daya tare da harsasai guda uku da kuma wuka daga hannun wadanda a ke zargin. “A wannan rana da misalin karfe daya na dare, tagawar ‘yan sanda daga FESTAC ta samu nasarar cafke Bemidee Ogunbanjo dan shekara 30, a rukunin gidaje na Prayer Estate da ke Amuwo Odofin. “An gano karamar bindiga kirar gida guda daya tare da harsashi guda daya daga hannunsa.
“Ana cigaba da bincike, idan a ka kammala kuma za a gurfanar da wadanda a ke zargia gaban kotu,” in ji Elkana.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!