Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Sanda Sun Damke Wani Mai Gadi Bisa Laifin Kashe Abokin Aikinsa

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Legas ta bayyana cewa, ta damke wani mai gadin kwalijen kimiyya da ke Jihar Legas, bisa laifin kashe abokinsa lokacin da ya ke bakin aiki. Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Legas DSP Bala Elkana, shi ya bayyana hakan a cikin bayaninsa na ranar Lahadi. Elkana ya bayyana cewa, a ranar 24 ga watan Mayu da misalin karfe bakwai na safe ne, ‘ya sanda da ke gudanar da aiki a kan hanyar Shagamu tare hadin gwiwar shugaban masu gadin kwalejen kimiyya ta Jihar Legas da ke Ikorodu, su ka samu nasarar damke wani mai gadin kwalejin kimiyyar mai suna Cletus Williams, bisa laifin kashe abokin aikinsa, Okoro John, sa’ilin da su ke bakin aiki.
“Wanda a ke zargin ya yi amfani da wuka mai kaifi, inda ya yanka makwogoron mamacin tare da wuyar hannunsa. “Tawagar rundunar ‘yan sanda masu binciken laifin kisan kan da ke Yaba, su na gudanar da binciken musabbabin yin kisan. “An gano wukar da ya yi amfani da wajen yi wannan kisa, sannan kuma za a gurfanar da wanda a ke zargin a gaban kotu bisa tuhumar kisan kai,” in ji shi.
’Yan Kungiyar Asiri Sun Tarwatsa Bikin Murnar Haihuwa Tare Da Kashe Mutum Guda A Ogun
An cafke mutum hudu wadanda a ke zargin ‘yan kungiyar asiri ne da su ka kashe wani matashi mai suna Saibu Azeez, a wurin bikin murnar haihuwa wanda ya gudana a yankin Abule Lemode da ke Ijoko cikin karamar hukumar Odo/Ota ta Jihar Ogun. Wadanda a ke zargin dai su ne; Opeyemi Olalekan, Azeez Ologundudu, Emmanuel Omoboriowo da kuma Anigilaje Babatunde, rundunar ‘yan sandar Jihar Ogun da ke Agbado su ne ta samu nasarar cafke wadanda a ke zargin.
Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Abimbola Oyeyemi, shi ya tabbatar da wannan kame a cikin bayaninsa na ranar Lahadi wanda ya gabatar a garin Abeokuta. Oyeyemi ya yi zargin cewa, wadanda a ka cafke kasurguman ‘yan kungiyar asiri ne, kuma an samu nasarar cafke su ne bayan da ‘yan sanda da ke yankin Agbado su ka samu kiran wayar salula.
A cewarsa, lamarin ya afku ne lokacin da wadanda a ke zargin su ka mamaye wajen da a ke gudanar da murnar zagayowar ranar haihuwa, wanda ya gudana a gidan Oluwatoye Ogun, mai lamba 34 da ke kan titin Oyedele kusa cikin yanin Abule Lemode ranar 24 ga watan Mayu, 2019. Oyeyemi wadanda a ke zargin sun tarwatsa mutanen da ke wurin bikin da fashesshen kwalba da misalin karfe biyu na dare.
Ya ce, “Wadanda a ke zargin sun fasa kan mahaifin wanda ke murnar zagayowar shekarar da fashesshan kwalba, sannan su ka caka wa Saibu Azeez fashasshen kwalba a cikinsa. “Lokacin da ‘yan sanda su ka samu kiran wayar, DPO ‘yan sandar Agbado, CSP Aloko Amodu, ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa wurin, inda a nan ne a ka samu nasarar cafke mutum hudu ‘yan kungiyar asirin.”
Kakakin rundunar ‘yan sanda ya cigaba da bayyana cewa, an garzaya da mutum biyu wadanda su ka samu raunika a wannan farmaki zuwa asibitin da ke kusa, cikin har da mahaifin wanda ya ke murnar haihuwar. Oyeyemi ya ce, Azeez ya mutu lokacin da ya ke amsar magani. A cewarsa, bincikin ya nuna cewa, mamacin dan wata kungiyar asiri ne wanda su ke hamayya da wadanda su ka kawo farmakin, sun kawo farmakin ramuwar gayya ne.
Kakaki rundunar ‘yan sanda ya ce, “Duka wadanda a ka cafke sun tabbatar da cewa, su mambobin kungiyar asiri ne da ke hamayya da juna. “An ijiye gawar mamacin a asibiti domin gudanar da bincike.”
Ya ce, kwamishinan ‘yan sandar jihar, Bashir Makama, ya bayar da umurnin a mika wadanda a ke zargin ga sashin rundunar ‘yan sanda masu binciken laifukan kisa da ke jihar, domin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin. Oyeyemi ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sandar ya jaddada cewa, rundunar ‘yan sandar jihar ba za ta huta ba, har sai ta dakile ayyukan ‘yan kungiyar asirin wadanda su ka addabi jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!