Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Gurfanar Da Dan Kasuwa A Gaban Kotu Bisa Damfarar Miliyan 56

Published

on

A ranar Talata ne ‘yan sanda su ka gurfanar da wani dan kasuwa mai suna Augustine Oshoke, a gaban babbar kotun tarayya da ke Jihar Legas, bisa zargin sa da damfarar naira miliyan 56. A cewar kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, ana tuhumar Oshoke da laifin hada kai domin aikata laifi da kuma laifin mallakar kudi ba bisa ka’ida ba.

Wanda a ke tuhuma mai dauki lauya ba, amma duk da hakan ya musanta laifin da a ke tuhumar sa da shi guda biyu.

Lauya mai gabatar da kara Misis Gladys Imegwu, ta bukaci kotu ta dage sauraran karan, domin bai wa masu gabatar da kara damar bayyana hujjojinsu. Ta bukaci kotu ta cigaba da tsare wanda a ke hukuma.

Alkali mai shari’a Chukwujekwu Aneke, ya dage shari’ar har sai ranar 4 ga watan Yuli. Aneke ta bayar da umurnin a cigaba da tsare wanda a ke tuhuma a gidan yari a matsayin wanda a kammala shari’ar sa ba.

A bisa tuhumar da a ke yi masa, wanda a ke tuhuma ya aikata wannan laifi ne tun  a ciki watan Disamba, 2017. Ana dai tuhumar sa da hada baki da wasu mutune, inda su ke damfari wani mutum mai suna Mista Hassan, wanda wanna laifi ne da ya sabawa sashi na 1(3) da kuma 5 a dokar damfara ta shekarar 2006.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!