Connect with us

KASUWANCI

An Yi Asarar Kashi 2.21 A Kasuwar Sayar Da Hannun Jari

Published

on

Kayan da a ka yi hada-hadarsu a kasuwar sayar ta hanun jari ta kasa NSE a ranar Litinin da ta gabata, an samu faduwa, ganin cewar, wadanda suka zuba jarin su a kasuwar, sunfi nuna bukatar su akan shiya musamman ta kamfanin sadarwa na NTN da ke gudanar da ayyukan sa a Nijeriya.
A ranar ta Litinin, dukkan shiyar da akayi hada-hadar ta a kasuwar an rufe akan naira 30,194.71 da kuma naira tiriliyan 13.302, inda aka samu raguwa ta kashi 2.21 bisa dari, 14 sunci riba sai 19 kuma suka tabka asara.
Har ya zuwa yau, asarar kayan cikin gida da akayi hada-hadar su a kasuwar, ta munana, inda ta kai kashi 3.92 bisa dari daga kashi 1.75 bisa dari, ganin farashin shiya ta kamfanoni kamar na kamfanin MTN, kamfanin Siminti na Dangote, sun kai kashi 7.14 bisa dari da kuma kashi hudu bisa dari, inda kuma hatta kamfanin mai na Oando da kamfanin mai na Forte suka kai kashi 2.27 bisa dari da kuma kashi 1.26 bisa dari.
A bangaren yankuna kuwa, a fannin man fetur da iskar gas, sun kai kashi 2.09 bisa dari da kuma kashi 0.39.
Bugu da kari, yawan kasuwancin da akayi a kasuwar, ya kai shiya miliyan 148, sabanin na na shiya miliyan 294, inda hakan ya kai kashi 49.60 bisa dari, sai kuma wanda ya kai yawan wanda aka samau na naira biliyan 2.22, sabanin naira biliyan 6.63, inda ya kai kashi 66.54 bisa dari na raguwar da aka samau a hada-hadar da akayi a baya.
Sai dai, kwararru sunyi imanin cewar, mai yuwa a hada-hadar da za’a gudanar a kasuwar a sati mai zuwa, asarar zata iya karuwa a sauran fanonin.
Hukumar FIRS Ta Kashe Naira Miliyan 160 Don Sayen Kakin Direbobin Ta Da Naira Miliyan 825 Na Sayen Kayan Tande-Tande- Flower Daga Abubakar Abba
Hukumar tara haraji ta kasa FIRS tayi shelar cewar, ya kashe naira miliyan 160 akan kakin direbobin ta da kuma kashe naira miliyan 825 wajen sayen kayan tande-tande. Shugaban Hukumar ta FIRS Tunde Flower ne ya sanar da hakan, inda ya kara da cewa, Hukumar ta FIRS, ta kuma kebe naira miliyan160 don dinkawa direbobin Hukumar kakin nasu da kashe naira miliyan 825 din sayen kayan tande-tande da kuma naira miliyan 250 na fannin tsaro wanda ta sanya a cikin kasafin kudi na shekarar 2019.
Shugaban Hukumar ta Mista FIRS Tunde Fowler wanda ya sanar da hakan ne lokacin da yake kare kasafin kudin Hukumar tasa a gaban kwamitin hadaka na Majalisar Kasa dake a babban birnin tarayyar Abuja a ranar Litinin data gaba.
Kwamitin ya kuma tambayi Shugaban Hukumar ta FIRS Mista Tunde Fowler akan tsimayin kashi 14.6 bisa dari na karin yawan ma’aikatan Hukumar daga 7, 854 a shekarar 2018 zuwa 9000 a shekarar 2019.
Bugu da kari, kwamitin ya kuma bukaci Shugaban Hukumar ta FIRS Mista Tunde Fowler ya yi masa bayani akan naira miliyan 160 da aka ware don sayen kakin direbobin Hukumar da naira miliyan 825 na sayen kayan tande-tande da kuma naira miliyan 250 na tsaro da sauran su.
Da yake kare kasafin kudin na Hukumar tasa, Shugaban Mista Tunde Fowler ya sanar da cewa, karin ma’aikatan Hukumar da take son yi, tana son ta kara karfafa kuzarin su, wadanda kuma nan bada za’a kara su a cikin shekarar nan ta 2019.
Acewar Shugaban Hukumar ta FIRS Mista Tunde Fowler, Hukumar ta numa kebe naira miliyan 160 don dinka kakin direbobin Hukumar har su 850, inda hakan yana daya daga cikin kokarin da Hukumar take yi na tabbatar da akoda yaushe suna a cikin tsafta.
Shugaban Hukumar ta FIRS Mista Tunde Fowler ya kara da cewa, kudin da aka kebe don tabbatar da tsaro, an kebe su ne don gudanar da wasu tarurruka na Hukumar da suke bukatar a samar da tsaro.
A kwanan baya kwamitin ya bijiro da nuna damuwar sa akan akan adadin da Hukumar ta FIRS ta sanya a cikin kasafin ta na shekarar 2019 da kima kudin da take son tarawa daga harajin da bai shafi man fetur ba da kuma karbo harajin naira biliya 146.54.
Daya daga cikin shugabannin kwamitin na Majalisar Sanata John Enoh da kuma sauran wakilan kwamitin, sun bukaci su san ata ya ya kuma 2018 aka amince da kimanin naira biliyan 153.85 a shekarar, inda kuma na shekarar 2019, ya kai naira 146.54, kusan kashi 4.75 na raguwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!