Connect with us

KASUWANCI

Max Air Ya Zayyana Kalubalen Da Yake Fuskanta Na Gudanar Da Zirga-Zirga

Published

on

Mahukuntan kamfanin jirgin sama na Max Air sun sanar da cewar, kamfanin a kwanan baya ya rage gudanar da wasu ayyukan sa don biyan bukatun Fasinjojin sa a bisa ka’idojin sufurin jiragen sama na kasa.
Manajan tashar jiragen sama dake Babban Birnin Tarayyar Abuja Mista Kehinde Ogunyale ne ya sanar da hakan a hirarsa da kamfanin dillancin labarai a ranar Litinin data gabata a Babban Birnin Tarayyar Abuja.
Acewar Mista Kehinde Ogunyale, kamfanin na Max Air, yana yin aiki ne da jirgi guda daya saboda a bi ka’idar kula da jirgin da kuma yawan duba shi, inda ya kara da cewa, a yanzu haka, dayan jirgin mallakar amfanin, yana a ma’ajiyar dake Aero cikin jihar Legas, dayan kuma ana kan duba shi.
Mista Kehinde Ogunyale ne ya sanar da yaci gaba da cewa, kamfanin ya rage yawan gudanar da ayyukan sa daga karfe bakwai zuwa karfe biyar, inda yake zuwa gurare harda garin Fatakwal da jihar Sokoto.
Ya kara da cewa, kamfanin ya kuma rage zirga-zirgar sa zuwa jihohin Legas da Kano, inda ya kuma hade ayyukan Yola da Maiduguri.
Mista Kehinde Ogunyale ne ya sanar da ya sanar da cewa, jirgin da a yanzu ake duba lafiya sa a Aero dake cikin Jihar Legas, mahukuntan kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar nan sun amince da cewar, jirgin zai iya kara komawa bakin aiki a ranar litinin data gabata.
Acewar Mista Kehinde Ogunyale ne “ Muna gudanar da aiki da jirgi daya ne saboda baiwa jirage kula ta dole da ake so a bisa ka’ida, dayan jirgin namu kuma ana kan duba shi.”
Yaci gaba da cewa, “A tsakanin wannan lokacin, mun rage yawan guraren da muke zuwa daga bakwai zuwa biyar dimin a yanzu, mun daina zuwa jihar Sokoto da garin Fatakwal kuma tuni, mun dakatar da sayar da tikiti na zuwa wadannan guraren.”
Mista Kehinde Ogunyale ne ya sanar da cewa, kamfanin Max Air, yana gudanar da ayyukannsa a fannoni hudu ta hanyar yin hadaka da wani kamfanin jirgin sama don ya ragewa kansa nauyin dake kansa ta wannan ranar.
Ya sanar da cewa, “Fasinjojin mu mun sanar dasu, kuma muna yin wasu ayyukan kubutarwa da kamfanin jirgin da muka yi hadaka dashi.”
Ya bayyana cewar, jirgin an gamsu dashi an kuma sako shi, inda aka fara gudanar da aiki dashi a ranar 27 ga watan Mayun shekarar 2019.
Akan zargin cewar kamfanin ya bar fasinjojin sa a yashe har zuwa awowi masu yawa, Mista Kehinde Ogunyale yace, babu wani lokaci da kamfanin Max Air ya yiwa fasinjojin sa haka.
Acewar Mista Kehinde Ogunyale, kalubalen jinkirin da aka samu, ya auku ne saboda canjin yanayi, musamman ganin damina tana kara shigowa.
Ya kara da cewa, “ Domin akwai lokuta uku, musamman da fasinjojin suka shafe awa kusan biyu a lokuta mabanbanta jirgin bai tashi ba saboda canjin yanayi.”
Mista Kehinde Ogunyale ne ya sanar da yaci gaba da cewa.“ Ya yi nuni da cewa, akwai lokacin da jirgin yaje jihar Kano, amma ya kasa sauka saboda canjin yanayi, inda hakan ya sanya dole muka dawo nan garin Abuja don mu jira canjin yanayin ya daidaita sai kuma canjin yanayin na garin Abuja ya kazanta, inda nan ma dole muka kara jira har na wasu awowi 30, ya kara da cewa, akwai abjbuwa da dama kuma bazamu iya yin komai akan canjin yanayi ba.”
Acewar Mista Kehinde Ogunyale, kamfanin na Max Air a yanzu, yana yin amfani da jirgin sa kirar 747 don yin jigilar Umrah, inda a kalla ya yi jigilar fasinjoji kimanin 8000 kasar Saudiyya.
Mista Kehinde Ogunyale yaci gaba da cewa, “Mun samu jinkirin tashin wasu jiragen mu saboda fasinjojin sunzo filin jirgin a makare, inda aka barsu a yashe ko kuma basu samu damar tashi ba kwata-kwata.”
Kamfanin jirhin na Max Air shine na farko a sahun jiragen sama dake gudanar da zirga-zirga a cikin kasar nan kuma mai yin kokari sosai wajen gudanar da ayyukan sa.
Hatta sashen hudda da jama’a na Hukumar NCAA, ya jinjinawa kamfanin jirgin sama na Max Air, Oberland da kuma Azman a matsayin kamfanonin jiragen sama da suke yin jinkiri da soke yin zirga-zirga.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: