Connect with us

KASUWANCI

NCAA Ta Janye Barazanar Rusa Turakun Kamfanonin Sadarwa 7,000

Published

on

Hukumar dake kula da tashi da saukar jiragen sama ta kasa, NCAA ta ce, ta janye barazar data yi na rushe turakun wasu kamfaninonin layin sadarwa sama da 7,000 da ke daukacin fadin kasar nan.
Janar Manaja na Hukumar ta NCAA Mista Sam Adurogboye ne ya sanar da hakan a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa a ranar Litinin da ta gabata a jihar Legas.
Mista Sam Adurogboye ya cigaba da cewa, Hukumar ta NCAA ta yanke shawarar janye barazanar ce ganin yadda kamfanonin sadarwar su ka fara bin umarnin da hukumar ta ba su a kan turakun nasu na sadarwa da abin ya shafa tare da amincewa za su karbi takardar umarninta.
A cewar Mista Sam Adurogboye, “idan za ku iya tunawa, mun tura wasiku ga kamfanonin sadarwa da lamarin ya shafa, inda sakamakon hakan suka yi kokarin magance lamarin da muke magana a kai.”
Ya kara da cewa, hakan ya sanya sunzo gun mahukuntan Hukumar ta NCAA don a tattauna akan yadda zasu biya sauran kudaden da ake binsu.
A cewar Mista Sam Adurogboye,“Ba mu kai matakin fara tuge turakun sadanarwa na kamfanonin da abin ya shafa ba ganin cewar sun kawo kansu kuma ana kan tattaunawa da su.”
Mista Sam Adurogboye ya kara da cewa,” Hukumar ta NCAA ta bude layin sadarwa na kamfanin Global Communications da kuma sauran wasu kuma muna sa ran babu wata bukatar tsaurara wa’adin namu.”
Kamfanin dillacin labarai na kasa ya ruwaito cewar, Hukumar ta NCAA a ranar 23ga watan Afirilu wannan shekarar ta baiwa kamfanonin sadarwa da abin ya shafa wa’adin kwanuka 30 wadanda suka ki mallakar takardsr shedar ta AHC ko kuma ta tuge turakun layin sadarwar su.
Acewar Hukumar ta NCAA, idan ba tare da amincewar takardar shedar ba Hukumar ta yi barazanar tuge turakun sadarwa na na kamfanonin da abin ya shafa, mussaman wadada zasu iya janyo hadari a lokacin tashi ko saukar jiragen sama.
A bisa karkashin dokar tashi da saukar jiragen saman ta shekarar 2006, sashi na 30 (3) da (1) a cikin baka, Hukumar NCAA tana da karfin haramtawa da kuma sanya ido akan kafa turakun kamfanonin sadarwa.
Har ila yau, dokar ta Hukumar ta gindaya 12.1.7.1.3.1 babu wani ko kuma wani kamfani da zai kafa wasu turakuna dindin kona wucin gadi within the da zai iya shafar sananin samaniya na Nijejiya ba tare da wannan mutun ko kmafanin ya ya samo takardar umarni daga gun AHC ba.
Kuma koda Hukumar ta bayar da takardar umarnin, ta umarci AHC ta tabbatar kafa turakun ba’a son tsawon su ya wuce iyaka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!