Connect with us

KASUWANCI

OPEC Ta Yi Gargadi Kan Kiyaye Ka’idar Yarjejeniyar Rage Hakar Mai

Published

on

Kungiyar kasashen dake fitar da mai zuwa kasar waje OPEC, ta yi kira ga kasashen da suke yayan kungiyar da kuma sauran kasashen da basa cikin kungiyar dasu ci gaba da kiyaye yarjejeniyar da kungiyar ta gindaya na rage yawan sarrafa man don a samar sa daidaiton man a kasuwar duniya.
Acewar kungiyar ta OPEC, an cimma wannan matsayar ta rage yawan sarrafa man ne a karkashin yarjejeniyar DoC, harda sauran kasa kasashen da basa cikin kungiyar, inda aka yanke shawrar hakar kashi 168 bisa dari a watan Afirilun shekarar 2019, inda kuma ya bin ka’idar ta kai 120 bisa dari tun a watan a Janairun shekarar 2019.
Sai dai, Ministan Makamashi da albarkatun man fetir na kasar Saudiyya Khalid Al-Falih ya sanar da cewar, a taron kwanan baya na hadaka karo na 14 na ministocin dake JMMC da aka gudanar Jeddah, yayan kungiyar sun bayyana cewar, ya kamata kasashen da suma rattaba hannu akan yarjejeniyar suci gaba da kiyaye ta.
Ya bayyana jin dadin sa akan yadda kasashen da suka rattana hannu akan yarjejeniyar suke ci gaba da kiyaye ta, inda ya yi nuni da cewa, hakan ya nuna cewar, ko wannen su akwai muhimmiyar rawar da zai taka akan yarjejeniyar.
Ya sanar da cewar, sai idan an kiyaye yarjejeniyar ce, sannan za’a samu cin nasarar da ake bukata a fanin.
Ministan na kasar Saudiyya ya kuma sanar da cewar, kungiyar ta OPEC da sauran magoya bayan ta bazasu yi gaggawar daukar mataki ba game da DoC a taron da zasu yi a nan gaba ba.
Ya yi nuni da cewar, di gaban a kasuwar akwai bukatar ayi nazari akanta a hankali.
Acewar sa, idan aka hada dukkan wadannan a guri guda, muna son mu yanke shawara ba tare.da jin wani tsoro ba amma bamu son muyi hakan a cikin gaggawa don gudun kada a samu bayanai masu cin karo.da juna a yanayi irin wannan.
Ministan yaci gaba da cewa, hakan ne ya sanya muka dage ganawar da mu ka so mu yi a cikin watan Afirilun wannan shekarar, inda yanzu aka shirya za’a gudanar a Bienna a cikin watan Yuni mai zuwa, kuma a lokacin ganawar, muna sa ran samun bayanai da dama.
Ya kara da cewa, dan lokacin da muka kara dauka.zai taimaka wajen samun bayanai don yin amfani dasu a ganawar da yayan kungiyar OPEC zasu yi a cikin watan Yuni, musamman don daukar matakai na gaba.
Acewar sa, kungiyar ta, OPEC da sauran yayanta baza su gajiya ba wajen yin dukkan abin da ya dace ba.
Al-Falih ya yi nuni da cewar, karuwar rikicin kasuwanci a tsakani manyan kasashe biyu masu karfin tattalin arzikin a duniya yana kara jefa firgice a tattalin arzikin duniya.
Ya yi nuni da cewa, hakan zai iya shafar tattalin arzikin wasu kasashen da kuma karya kaifin bukatar mai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!