Connect with us

KASUWANCI

Gwamnati Za Ta Yi Wa Kamfanoni Ragin Haraji A Zuba Jari Kan Gina Hanyoyi

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa, zata yiwa  kamfanoni masu zaman kansu dake da burin zuba jarin su akan  ayyukan manyan  hanyoyi dake daukacin shiyyoyi shida na fadin kasar ragin biyan kudin haraji.

Tsohuwar  Ministar Kudi Hajiya Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan a ranar Talatar data gaba a babban birnin tarayyar Abuja a lokacin taron gabatar da kasafin kudi na shekarar  2019.

Hajiya Zainab Ahmed wadda tayi magana akan wasu  hadakar da gwamnati ta yi da kamfanoni masu zaman kansu a karkashin shirin PPP tace, duk wani kamfanin da ya  da ya zuba kudin sa akan aikin manyan hanyoyi dake a shiyyoyi shida na fadin kasar nan, Gwamnatin Tarayya zata yi masa ragin biyan haraji na daidai kudin da ya zuba jari akan aikin na manyan hanyoyi.

Tsohuwar Ministar kudin Hajiya Zainab Ahmed taci gaba da cewa, Gwamnatin Tarayya maici a yanzu, ta samar da shirye-shirye da dama  don yin hadaka da kamfanonin dake kasar nan masu zaman kansu.

Acewar Hajiya Zainab Ahmed, daya daga cikin shirye-shirye shine, ayyukan manyan hanyoyi dake a daukacin fadin kasar nan  a karkashin shirin haraji na ITCS, inda duk kamfani mai zaman kansa ya gina hanya da kudin sa, zasu iya samu zuba jarin su ta hanyar ragin da za’a yi masu na biyan harajin su.

Acewar tsohuwar Ministar Uwargida Zainab Ahmed Gwamnatin Tarayya tana kokarin samar da biyan saukin kudin fito.

Uwargida Zainab Ahmes tace a yanzu, hanyar tana da wahalarwa matuka kuma tana janyo kashe kudade sosai.

Ta kara da cewa, “ A yanzu mun samu ci gaba akan aikin kuma munyi imani idan muka samar da daidaiton da ya dace, hanyar zata kasance ana bin ka’ida kuma za’a yita a cikin sauki.’’

Tsohowar Ministar nudin Uwargida Zainab Ahmed ta kara da cewa, Gwamnatin Tarayya ta kirkiro da dabaru shirin habaka kudin shiga na SRGI  musamman, don a diga tara kudaden shiga daga daukacin fannonin tattalin arzikin kasar nan.

Acewar  Uwargida Zainab Ahmed, manufar shirin itace don a dinga sanya ido wajen habaka judin shiga na Gwamnatin Tarayya da hukumomin gwamnatin suke tarawa.

Har ila yau, a bisa fashin bakin da akayi akan kasafin judin na shekarar 2019 ya nuna cewar, Ma’aikatar cikin gida ta samu kaso mafi tsoka na ayyukan yau da kullum na naira biliyan  564.22, wanda ya hada da albashi  da sauran kudin tafiyar da Ma’aikatar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin data gabata, ya rattaba hannu akan kasafin kudi  na shekarar 2019, inda hakan ya  nuna ana shirin wanzar da kasafin kudin a shekarar kudi ta 2019 .

Bugu da kari, kudin da aka tura ST, ya kai naira biliyan 502,  sai na gibi, ya kai naira tiriliyan 1.92, na dauki na musamman SI ya kai naira biliyan 500, na yau da kullum ya kai RE, ya kai naira tiriliyan 4.07 sai na manyan ayyuka ya kai CE ya kai naira tiriliyan 2.09, inda kuma gibin da aka samu na tattalin arzikin kasa ya kai kashi 1.37 bisa dari.

A bangaren da bai shafi mai ba, ana sa ran tara kumanin kudin shiga naira  naira tiriliyan 3.31 sai kuma a fannin da ya shafi mai, ana sa ran tara kimanin naira tiriliyan 3.69.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: