Connect with us

KASUWANCI

NNPC Ya Bayar Da Tabbacin Bin Ka’idar Zabo Masu Dako Da Sayar Da Gas

Published

on

Kamfanin  NNPC ya bayyana yace, za’a bi ka’ida wajen zar masu neman  dako da sayar da gundarin gas.

Manajan Darakta na rukunonin kamfanin Dakta Maikanti Baru ne ya bayar da wannan tabbacin a gundarin gas na 2019 da aka gudanar a  Abuja a ranar  Talatar data gaba.

Yaci gaba da cewa,“A matsayin kamfanin a yanzu, yana ci gaba da  samar da wadataccen gas don yin amfani dashi a cikin kasar nan.”

Ya kara da cewa,“ Dabarun mu shine, mayar da hankali akan watanni masu zuwa don kara fadada wadata gida da Gas samfarin LPG daga namu na cikin gida tare da baiwa masu zuba jari kwarin gwaiwa.”

Acewar sa,“Ta hanyar bin ka’idar wajen zabowar da kuma aunawa, muna shirin mu sanya kamfanoni wadanda fitattu ne a wajen zuba jari a fannin tattalin gas adana shi, rabar dashi da kuma rabar dashi.”

Baru wanda Jami’i a sashen gas da wuta na kamfanin NNPC Saidu Mohammed ya wakilce shi a gurin taron yaci gaba da cewa, taron ya tabbatar da fara bude wani sabon faifai na kokarin da ake yi na tattalin  gundarin gas     dake kasar nan don amfanin yan Nijeriya.

Yace, manufar bayar da damar ta 2019 din a janyo kamfanonin dake a fannin na dakon gas na cikin gida.       

Acewar sa, za kuma a tabbatar kamfanonin da za’a zabo zasu kasance masu bin ka’ida, masu amana don abi doka ta yin amfani da kayan cikin gida.

Yace, samar samfarin gas na  LPG da akafi sani da  gas din girki, zai wuce iyakar wanda ake bukata a cikin kasar nan.

Ya danganta karancin samar dashi a lunguna da sakunan fadin kasar nan akan rashin rabar dashi.

Acewar sa, shirin da akayi na kara yawan     gas din girki  zai taimaka wajen shirin da akeyi na dakon na gas.

Yace,“ A wannan lokacin, bawai muna mayar da hanakali ne   akan daukowa da tura gas din ba, muna numa mayar da hankali na wadatar dashi a cikin kasar nan.”

Acewar sa, “ Ta wani bangaren kuma, muna son muyi amfani da wannan cinikayyar  ta kasuwar LPG a daukacin fadin kasar nan zuwa ga matsayin da ya dace.

Yace, “ Yau  Nijeriya ta kasance daya daga wadda take da mafi karanci na yin amfani da LPG, saboda baza mu iya karade ko ina ba.”

Ya yi nuni da cewa, “Ta hanyar da zamu iya karadewar kawai ita ce, da farko  daukacin wadataccen gas da ake dashi, mutane zasu zo sannan su zuba jari ta hanyar tara shi, rabar dashi da kuma jigilar.”

Ya sanar da cewa, “Mafi mahimmanci, muna son muyi hakan a bisa bin ka’ida din tabbatar da an zabo masu hadakar da suka dace wadanda kuma suke da yakinin zuba jarin su da kuma samun karade kunguna da sakunan kasuwannin dake cikin kasar nan.”

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewar, kimanin  kamfanoni 223  auka ayyana bukatar neman dakon na gundarin gas.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!