Connect with us

MAKALAR YAU

Samar Da Jari Da Rarraba Arziki

Published

on

Har a ka gama cece-kuce game da sake nadin Emefele a amatsayin Gwamnan Babban bankin Nigeria ban ce komai ba, sai a yanzu da kura ta fara lafawa. Dalili kuwa shine sakamakon yadda na bibiyi halin tattalin arzikin Nigeria daga shekarar 2015 kafin zabe, wanda ya kasance tattare da matsaloli kama daga cin hanci da rashawa, rikicin Boko Haram da babakere da handamar yan siyasa wanda ya jefa tattalin arzikin kasar cikin koma baya.
Zuwan Buhari tare da tsarin tattalin arzikinsa karkashin kulawar Emefele sun yi kememe tare da watsi da shawarwarin shahararrun masana tattalin arziki irinsu Legarde, shugabar bankin duniya da tsoffin gwamnonin bankin Nigeria wato Sunusi Lamido da Charles Soludo na cewa a rage darajar Naira. Babban bankin Nigeria ya fito da tsarin sakin dala duk sati cikin tattalin arzikin kasar domin tallafawa darajar Naira, wanda hakan ya kawo daidaiton canji a kasuwar kudaden waje. Tsarin da a cikin shekara guda ya fitar da kasar daga koma bayan tattalin arziki. Watakila da an bi shawarar masanan na rage darajar Naira, da yanzu ta kai Naira 1000 a kan dala 1. Wannan dalili kadai ya isa a kalli Emefele a matsayin gwarzo.
Bankuna su ne kashin-bayan tattalin arziki irin na zamani, kuma an fara harkar bankuna a kasashen turai lokacin zaburar canji a Italiya. Amma dai tsarin banki irin na yanzu ya faro ne a kasar Ingila a karni na 17th. Masu hada-hadar zinare wadanda ke da asusun ajiya a shagunansu a wancan lokaci, su ne su ka fara karbar ajiyar kayayyakin zinare daga mutane wadanda ke biyan wasu kudade na ajiya. Sannu a hankali sai aka fara bada takardar shaidar cewa ka bada ajiyar zinare wanda daga baya ta zama wata shaida da ake iya amfani da ita tamkar kudi. Banki Ingila shine ya fara bada takardar kudi a shekarar 1695.
Babban aikin banki, bayan ajiyar kudade shine bada lamuni ga manya da kananan yan kasuwa. Cajin ruwa da ake sakawa irin wannan bashi shi ke nuna yadda akalar tattalin arziki ke bunkasa domin idan cajin ya kasance kasa sosai, sai ka ga harkokin kasuwanci na bunkasa wanda akasin haka ke kawo koma baya.
Abin takaici, a nan Nigeria maimakon bankuna su kasance ja-gaba wajen kawo habakar tattalin arziki sai ga shi su ne su ka kawo rushewarsa. Dalili kuwa shine yan kasuwa, musamman kanana, ba sa iya samun bashi cikin sauki saboda tarnaki da dama. Cikin tarnaki da ake fuskanta shine na tsawwala kudin ruwa wanda a kasashe da su ka ci gaba ba ya wuce kashi 1-3% amma a Nigeria har kashi 30% ya na kaiwa. Sannan wani tarnakin shine na abin jingina da zaka bayar kafin a ba ka bashi da kuma takure lokacin biya, yadda ko ka samu bashin da wahala ka iya cika ka’idar a lokaci.
Dalilin da ya sa bankunan mu ba su damu da samar da basussuka ga yan kasuwa ba shine saboda samun kudin banza na ajiya da su ke samu daga barayin yan siyasa da kuma gwamnatoci. Saboda irin yawan wannan kudi da ake baiwa bankuna wanda su na kwance ba tare da wani aiki ba su ke samun gwaggwabar riba, shi ya sa su ke biris da baiwa yan kasuwa bashi.
Amma zuwan wannan gwamnati tare da fara aiki da tsarin TSA wanda gwamnati Jonathan ta kirkiro ya jawo debe kudaden gwamnati daga bankuna kasuwanci zuwa ga Babban bankin kasa, sannan kuma sa ido na hukumomi da ke yaki da cin hanci da rashawa ya sa ba’a samun kudade na barayin gwamnati. Wannan tsari ya jefa bankuna cikin matsi yadda a ka wayi gari a yanzu su na neman abokan hurda da su zo su karbi bashi a ruwan sanyi.
Daya daga cikin hobbasa da Emefele ya kawo shine a yanzu ya fara aiwatar da tsare-tsare na bayar da basuka iri-iri domin habaka kasuwanci a kasar. Daya daga cikin wadannan tsare-tsare shine na hukumar NIRSAL, wadda ita ma gwamnatin baya ta kawo. Aikin wannan hukuma shine na tabbatar da samar da kudade ga manoma manya da kanana domin noma, kiwo, kasuwanci da ma samar da manyan injuna da turaktoci na noma.
Abinda ke damun al’ummar mu ta arewa shine yawanci irin wadannan tsare-tsare mutanen da ya cancanci su ci moriyarsa ba sa sani saboda karanci wayar da kai. Sakamakon haka wata kungiya a Kano me suna K-PEAK ta dauki aniyar sanar da mutane yadda tsarin ya ke tare da daukar nauyin koya wa mutane yadda za su iya samun wadannan basuka.
Wannan kungiya ta samar da lauyoyi da akantoci kwararru wadanda ke ofishinta kuma su sanar da mutane ta hanyar hirarraki a rediyo da kiran jama’a su zo ofishinsu domin kwararru su nuna musu yadda za su cike fom din bashin da tsara musu tsarin yadda za su yi amfani da bashin, sannan kuma su za su bibiyi bashin a NIRSAL ba tare da cajin ko sisi ba har sai idan bashin ya fito sannan za a cire musu dan kudin aikin da su ka yi.
Idan da a ce kungiyoyi za su bi irin wannan hanya ta K-PEAK a sauran jihohin arewa, lallai da mutanenmu da dama za su iya samun cin moriyar wannan bashi mai karanci ruwa na kaso 5% kacal. Wannan bashi kowanne mataki na noma zai iya cin gajiyarsa, kama daga masu noma, kasuwanci ko kayan aiki irinsu turakta da iri da magunguna.
Sannan kuma Babban bankin na Nigeria, tare da kwamitin bankunan kasar, a kokarin samar da jari ga mata da matasa ya fito da sabuwar hanyar tallafi ga sashen fasaha (Creatibe Industry Financing Initiatibe). A karkashin wannan tsari an ware sassa hudu da za’a tallafawa da bashi wadanda su ka hada da: Sashen fasahar sutura (Fashion) da na Fasahar zamani (Information Technology) da Fina-Finai (Mobie) da kuma Wakoki (Music).
Tsarin da a ka yi shine da zarar ka iya samar da tsarin kasuwanci (Business proposal) wadda ke da bayanin irin kudaden da kake bukata da hanyar da za ka yi amfani da su (har da kudin hayar ofis ko shago da albashin ma’aikata da sauransu) sai ka kai bankin ka, wadanda CBN da kwamitin bankuna su ka umarci kowanne banki ya tabbatar ya samarwa mutane kudaden. A wannan tsari an ware a bawa dalibai bashin Naira miliyan 3 wanda za su biya a shekaru 3 kan kashi 9%.
Sai kuma masu harkar fim wadanda za su iya neman bashin Naira miliyan 30 wanda za su biya a tsawon shekaru 10 shi ma a kan kashi 9%. Ga wadanda ke da tsarin samar da harkar kasuwancin rarraba kayayyaki kuma za su iya neman har Naira Miliyan 500 wanda za su biya a shekaru 10 a kan kashi 9% shi ma.
A lokacin da yankin mu ke dada tsunduma cikin masifun satar mutane da ta’addanci wanda kowa ya san cewa dalilin rashin aikin yi da bude harkokin kasuwanci da rarraba arziki tsakanin al’ummar mu shi ya jawo haka, dole mu tashi tsaye wajen samar da ayyuka da yada ilimi idan mu na son zama lafiya. Shugabanni na al’umma a unguwanni wajibi su rika lalubo irin wadannan hanyoyi da sanar da matasa da ma tallafa musu yadda za su ci gajiyar irin wadannan basuka da tallafi.
Duk abubuwan da ke faruwa a yanzu ba komai ba ne ga abinda zai zo nan gaba matukar ba’a samar wa wadannan yara ayyukan yi da ilimi ba. Duk jihohin arewa tamkar wani bam ne wanda dakikokinsa ke bugawa kuma zai iya tashi kowanne lokaci kamar yadda mu ka gani a Borno da Zamfara. Allah ya kiyaye.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: