Connect with us

KASUWANCI

Sanya Hannu Kan Kasafin 2019 Zai Habaka Arzikin Nijeriya A Zango Na Biyu – Kwararre

Published

on

Sanannen  mai fashin baki akan fannin tattalin arzikin kasa da hada-hadar kudi Mista Dabid Ibidapo ya yi nuni da cewa, rattaba hannu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi akan kudurin kasafin kudi  na shekarar 2019 da ya zama doka, hakan zai taimaka wajen ciyar da tattalin arzinin kasar nan gaba a zango na biyu.

Mista Dabid Ibidapo ya sanar da hakan ne a hirar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa a babban birnin tarayyar Abuja.

Acewar Mista Dabid Ibidapo, rattaba hannun zai kara kashe kudi da habaka ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba.

In za’a iya tunawa, ranar Litinin ta shekarar 2019 data gabata ce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rattabawa kudurin kasafin kudin na naira   tiriliyan 8.92 ya zamo doka.

Mista Dabid Ibidapo ya kara da cewa, karin da majalisar tarayya ta yi a cikin kasafin kudin, mai yuwua ya shafi wanzar dashi.

Acewar Mista Dabid Ibidapo, kasafin kudin anyi masa karin kimanin naira biliyan 90   zuwa naira tiriliyan 8.83 wanda aka turawa yan majalisar a watan Nuwambar shekarar 2018.

Mista Dabid Ibidapo yaci gaba da cewa, rattaba hannun akan kasafin kudin zai kuma samar da tsari  ga masu zuba jari da kuma kara masu kwarin gwaiwa   wajen wajen hada-hada a ksuwar sayar da hannun jari ta kasa, ganin cewar, masu son zuba jari akoda yaushe suna son a samar masu da alkibla don su samu sukunin zuba jarin su.

Da yake yin tsokaci akan damur da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna akan karin na naira biliyan   90 da yan majalisar tarayya suka sanya a cikin kasafin kudin Mista Dabid Ibidapo ya yi nuni da cewa, ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya samar da mafita ta wanzar da kasafin kudin, musamman don a cimma burin biyan sabon karin albashin kananan ma’aikata da a kwanan baya shugaba Buhari ya rattabawa hannu ta zamo doka.

Acewar Mista Dabid Ibidapo, Gwamnatin Tarayya zata dinga tura kudade masu yawa don a tabbatar da cin nasarar wanzar biyan mafi karancin albashin, ganin cewar har yanzu cimma adadin son tarawa kasar nan kudi shiga, har yanzu nagana ce babba.

Yace, ta hanyar da kawai Shugaban kasa Muhammadu Buhari zaici nasarar wanzar da kasafin kudin a cikin nasara da kuma tabbatar da wanzar da biyan karin sabon albashin na kanan ma’aikata, shine rufe dukkan wata kafa da kuma cire abubuwan da basu da wani amfani kamar tallafin rarar man fetur.

Acewar Mista Dabid Ibidapo, idan Gwamnatin Tarayya ta cire tallafin na rarar man fetur, hakan zai zama babban sauki ga Gwamnatin.

A karshe  Mista Dabid Ibidapo yace, ya zama wajibi Gwamnatin Tarayya tabu dukkan hanyoyin da suka dace wajen habaka kudaden shigar ta idan hakan ya faru, zai kara habaka tattalin arzikin kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!