Connect with us

TARIHI

Tarihin Kasar Bauchi: Asalin Sunan Bauchin Yakubu

Published

on

Kashi Na Daya
Kafin mu ji asalin Bauchi, za mu fara ne da sanin sarkin Bauchi Yakubu wanda sunan sa yafi shahara tare dana Kasar.
An ce a karni na goma sha takwas daf da soma yakin jihadi a kasar Hausa, wasu malamai biyu masu suna Mallam Adamu da Mallam Isyaku suka tashi daga Borno zuwa Ganjuwa, inda suka zauna KarKashin kulawar sarkin garin na wasu dan shekaru.
Bayan nan sai suka tashi suka koma Kufu da zama, daga nan kuma sai suka Karasa Jetar.
A nan Jetar ne Mallam Isyaku yayi abota da wani mutum da ake kiransa da suna Dadi. Shikuwa yana zaune ne a wani wuri da ake kira Tirwin.
Mallam Isyaku ya kan ziyarci abokinsa Dadi a Tirwin, sai rannan Mallam Isyaku ya tafi wirin Dadi inda ya tarar dashi tare da yaron sa mai suna Yakubu.
Bayan sun gaisa sun soma firar duniya, sai Dadi yace masa “Wannan yaro da ka gani da ne gareni, kuma shi ne idanuna, Allah kuwa ya sanya sonsa da yawa cikin zuciyata. Ina da kaka da yawa banda shi amma ina so Allah ya albarkace shi a inda yake duka. Yanzu kuwa na baka shi, ka zama uba da shugaba a gareshi, shi kuma ya zama danka mai-yi-maka hidima, domin ya sami albarkar ka. Inda kake so duka ka tafi dashi, dukkan abinda kake so ya yi maka duka ka sanya shi yayi, domin kuwa danka ne, kai ne mahaifinsa”.
Abinda akayi kenan. Mallam Isyaku ya tafi gidansa tare da Yakubu ya cewa matar sa “Ga danki nan”.
Duk inda Mallam Isyaku zashi Yakubu na tare dashi, suna cikin haka har labarin Shaihu Usmanu dan Hodiyo ya zo musu. Mallam Isyaku ya tafi tare da Yakubu zuwa wurin Shehu Usmanu, ya zauna acan shekara da Shekaru yana karatun ilim.
Rannan sai Mallam Isyaku yayi niyyar tafiya ganawa da iyalinsa, amma baya da niyyar jimawa acan. Don haka ya tsammaci cewar idan ya tafi da Yakubu zai hana shi dawowa da sauri, hakan yasa ya shaidawa Shaihu Usmanu muradinsa tare da barin Yakubu a hannunsa. Daga nan sai yayi wa Yakubu bayani sannan ya tafi..
Allah da ikonsa, sa’ar da Mallam Isyaku ya riski wani gari mai suna Yalwan dan Ziyal dake Kasar Kano, sai cutar ajali ta ka ma shi, anan ya rasu. Don haka sai Yakubu ya cigaba da zama wurin shehu yana karatu, ya zama tamkar da a gidan shehu. Har ma shehu ya aurar masa da diyar abokinsa Mallam Bazamfare watau Yaya.

Kashi Na Biyu
Sa’ar da lamarin Shehu Usmanu ya bayyana, mutane suka taru a wurinsa har suka yi yawa, sai sarakunan Hausa suka fara fushi da hakan, suka zama masu fitinar jama’ar Shehu Usmanu, suna aike musu da hari, suna kisa da kame su gami da siyarwa a matsayin bayi
Da wannan abu ya tsananta sai jama’a suka yiwa Shaihu mubaya’ar yaki, suka soma gina ramin ganuwa da daura tuta.
A nan ne Shehu ya Umarci Yakubu ya koma gidasa Bauchi ya kira jama’ar sa zuwa biyayya ga Shaihu.
Yakubu ya tashi ya tafi ga mutanensa a Bauchi da ake kira Gerawa, ya kiraye su amma basu amsa kira ba. Sai wadansu mutane daban ne suka amsa, acikin su akwai Mallam Adamu, da Ibrahimu, da Abdun-Dumi, da Hassan, da Faruku, da Muhammad Kusu, da Muhammad Yaro, da Hammada, da Mallam Badara, da wadansun su da dama.
Yakubu ya ja taron jama’ar sa zuwa wani wuri da ake kira Warunje ya zauna, sannan ya tashi zuwa Inkel, mutane na ta zuwa wurinsa a hankali suna yi masa mubayi’a.
Daga nan sai ya shirya yaki zuwa wani gari da ake kira da suna Kanyallo, ya yake su yayi galaba akansu, ya Kone gidajensu ya washe dukiyarsu, sannan ya koma wurin zamansa. Wannan kuwa shine farkon yakin sa.
Bayan wannan sai ya kara shirya wani yakin, inda ya sarauta Galadima Faruku a matsayin Sarkin Yaki sannan ya aike su zuwa Miri, da zuwan su kuwa sai suka fada musu da yaki.
A nan ma suka karkashe mutanen Miri, suka kamo dadansu, suka rushe gidajensu, Sarkin su ya gudu, ya tura iyalan gidansa cikin kogon dutse sannan ya karkashe su, daga bisani kuma ya kashe kansa.
Galadima Faruku ya komo wurin Yakubu da ganimar yaki mai yawa cikin murna da farin ciki. Daga nan sai Yakubu ya shirya wani yaki zuwa Gubi.
Su kuwa mutanen Gubi ance Kafirai ne masu girman kai, gasu jaruman gaske masu Karfin rai, babu mai iya samun su.
Haka kuma suna zaune ne a wani wuri mai yawan duwatsu da wuyar shiga saboda santsin wurin shigar da kuma Kafe-Kafe gami da Kayoyi.
Amma duk da haka, sai da Yakubu yaci galaba akan su. Ya kore su suka bar gidajensu zuwa cikin duwatsu, shikuwa ya shiga cikin gidajen nasu, ya kashe na kashewa, ya kama na kamawa. Sannan ya koma gida Inkel cikin aminci da nasara.
Ai kuwa wannan yaki shine ya tsoratar da dukkan kafiran Kasar Bauchi, musamman mazauna saman duwatsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: