Connect with us

ADABI

Daga Littafin Amanna (45)

Published

on

Alh. Jibrin ya zabura a fusace ya katse shit un bai karasa magana ba ya ce “Abbas dan me zaka bata bakinka wajen tambayar gaskiya? Ba wani ba ne ya baka labari ga abu muna gani baro-baro. Allah Ya tona asairinka Iziddin, ina ganin ma ka dade kana cuta ta a ofis ganewa ne kadai ban yi ba. Idan da gaske ka dauko kanjamau ka sakawa ‘yata wallahi sai na yi kararka a kotu, mutumin banza mayaudari.”

Iziddin ya girgiza kai dan takaici, bai iya daga idanuwansa ya kalle su ba, balle ya yi magana .

Idanuwan Alh. Jibrin suka yi jajajwur muryarsa na rawa saboda tashin hankalin da ya shiga, ya ci gaba da cewa “Iziddin ka sani ba mu ka zalunta ba kanka ka yiwa.”

Alh. Abbas ya ce “ Na’if! Ko da shi ku ka raba dalolin da ka satowa Daddy ka?”

Iziddin ya dago da kai da sauri ya dubi mai magana sannan ya juya ya kalli Na’if, yana jira ya ji amsar da zai bayar.

Na’if ma ya tsare Iziddin da ido, ya cije baki ba kunya ba tsoron Allah ya ce “ Eh mana! Da shi muke rabawa, na bashi.”

Wannan sharri ya fi batawa Iziddin rai, ya ji kamar ya fito ya shake shi sai ya hakura ya ci gaba da sauraron yadda Allah Zai yi dashi. Wannan bala’ai da ske ta rikito masa ya san wata babbar jarabawa ce daga Allah. Ya na addu’a Allah Ya bashi nasarar tsallake ta.

Alh. Jibrin ya dauko wayarsa hannunsa na karkarwa ya kira lambar Nauwara.

A lokacin da Amatullah ta shiga dakin Nauwara tana rokarta ta yi hakuri ta daina hada kayanta kada ta  tafi daidai lokacin wayar ta shigo sai gaba dayansu suka tsurawa wayar ido cike da fargaba. Cikin sanyin jiki Nauwara ta dauko wayar a tunaninta zata ga lambar Iziddin.

Sai ta ga lambar babanta, ta zabura ta amsa, a firgice ta tambaya, “Daddy mutuwa aka yi ka kira ni da tsakar dare?”

Ya bude muryar a fili (hand’s free) yadda Iziddin zai ji komai, ya ce “ a’a ba mutuwa aka yi ba. ina mijinki?”

Sai ta jawo Amatullah ta bude muryar (hand’s free) suka durkushe a kasa suka saka waya a tsakiya suna karkarwa hade da zafafan hawaye.

Nauwara ta dora hannu a kai ta rusa kuka, ta ce “baya gida. Me ya faru da shi?”

Alh. Jibrin ya ce “gashi nan ina tare dashi, lafiyarsa kalau. Amma ina so ki hada kayanki kakaf gobe da safe zan zo in dauke ki.”

Ta sake fasa kuka ta ce “A club ka ganshi ko?”

Mamaki ya kama Alh.Jibrin ya ce “ashe ma kin san a club yake kwana amma baki taba fada min ba. Gashi nan tare da Na’if na zo na rutsa su. Tun jiya a garin nan nake neman Na’if  bam u gan shi ba sai yau, ya sace min daloli sama da bandir goma. Na sami labarin a club yake kwana shine muka biyo dare muka zo muka cafke shi, ya kasha kudin saura kadan aka samu a wajensa, shine yake fada min bashi kadai ba ne mai zuwa club har da Iziddin. Da ya fada min ban yarda ba har da hotunan Iziddin ya nuna min da ya dauke shi bai sani ba a club, ya saka gashi ya canja kama na ce karya ne ba hoton Iziddin ba ne dan Iziddin ba zai taba aikata wannan badalar ba, ba halinsa ba ne. Allah cikin ikonsa sai ya nuno mana motar Iziddin, muna karasowa muka tarar shine din ne shi da gashin da yake sakawa hard a wata . . . ga su nan dai abin sai addu’a kawai.”

Nauwara ta fashe da kuka ta ce “wallahi zaman da shi ya kare, Daddy ni tafiya zan yi.”

Ya ce “ki ma daina ratsuwa ni ne fan a kira kin a ce zan zo in dauke ki, ki yi hakuri har zuwa gobe da safe zan zo gidan naku da kaina, karki damu komai ya zo karshe.”

Su ka kashe waya, Iziddin ya runtse ido sai hawaye ya surnano daga idanuwansa, ya girgiza kai.

Tunda Amatullah ta dora hannu akai ta tsugunna bata kara mikewa tsaye ba har ta gama jin abinda suke fada a waya. Nauwara ta kare mata tsiya ta fito daga dakin tana sanda ta fito babban falo ta zauna, zazzabi ne ya rufe tad a ciwon kirji, Nauwara kuwa da karfin gwaiwarta ta ci gaba da hada kayanta har  da labulen dakin sai da ta sauke su kasa.

Alh. Abbas da Na’if suka gama cashewa Iziddin suka kara gaba daman Alh.Jibrin bai sake cewa komai ba tunda ya kashe waya ya yi gaba. Su ka tafi suka bar shi a zaune kamar gunki. Aljanna tana ta makerketa kuka ya tunkaro mata, tsoro ya hana ta rusa, tasa hannu ta toshe baki dan kada ta barke.

Iziddin ya yi shiru ya kasa daga hannuwansa balle ya yi tuki, ya kara gyara zama ya rike kai, bakinsa ne kawai yake motsi da alama addu’a yake yi. Aljanna ta laluba murfin mota ta bude ta fasa kuka ta yunkura zata fice da gudu sai ya damko gashin kanta, nan da nan tayi cara kai kace rai zai cire mata.

Ta fada  a gigice “ka rabu da ni, in tafi ko halaka kaina ma in yi. Ina zan saka raina?”

Ya daka mata tsawa ya ce “ko ki zauna ko in tsinka miki mari kuma idan kika kara fita daga cikin motar nan sai na fasa miki baki.”




Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!