Connect with us

TASKIRA

Kar Ki Bari Rudin Shaidan Ya Sa Ki Bar Kishiya Ta Kwashi Garabasa

Published

on

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah.

Da fatan kowa da komai duk lafiya in sha Allah.

Yau kuma za mu duba shin wai meye dalilin da yake sawa yawancin mu mata muke kauce hanya da yi wa junan mu mugunta domin Allah ya hada mu auren miji daya?

Na farko dai, ako da yaushe ina so ki dinga tunatar da kanki cewa da ni da ke, da mijin, da bokan, ko Malamin, ko kuma dan tsubbun, da mugwayen kawaye, duk zukatan mu a hannun Allah Subhanahu Wa Ta’ala suke. Shi kadai ne yake da dama da izinin juyata yadda yake so.

Na biyu: Tun kafin ma mu zo duniya Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya riga ya kaddara kuma ya tsara mana yadda rayuwar mu za ta kasance..

Na uku: Ko mu zauna lafiya ko kar mu zauna lafiya abinda Allah ya riga ya kaddara kuma ya tsara shi za’a yi kuma ba zai fasa faruwa ba.

Na san mata da yawa ba sa son wannan zancen. Amma wallahi ku yarda da ni idan na ce muku yana da amfani mu gane wasu abubuwan da za su sa mu samu saukin fahimtar zamantakewa masamman ma idan kina da abokiyar zama.

Ya ke ‘yar uwata wadda ba ta kaunar ‘yar uwar zamanta ko kishiya, ki sani ba haka aka so ba, amma ba laifi ba ne. Sai dai laifi babba ki cutar da ita ta ko wace irin hanya.

Ki sani cewa ba sai kin rabu da Allah kin sai da lahirarki saboda tsananin kishi don bakya son ta ba, idan bakya son ta falillahi hamdu, sai ki kaurace mata. Kina ma iya zama ki sanar da mai gida cewa bakya son ta kuma bakya son abin da zai taba hada ki da ita saboda kina gudun cutar da ita. Don Allah ya yi kokarin jawo hankalinta ta yi zamanta domin a samu kwanciyan hankali da natsuwa a gidan. Ta yi zamanta ki yi zamanki.

Kuma ki sani cewa aure yana da rai, ba sai kin wahalar da kanki ba, da dukiyarki, da lokacin ki, da ayyukan alherinki don ki ga kin raba kishiyarki da mai gidanku. Idan lokacin mutuwansa yayi, ko da dadi ko ba dadi, ko da fada ko ba fada, ko da zaman lafiya ko ba zaman lafiya, Allah da zai kawo karshen auren.

Abu na karshe shi ne: yake ‘yar uwa ta, ki dinga tunawa a ko da yaushe cewa mutuwa ba ta Sallama. Sai dai ta dauke ki idan lokacin ki ya yi. Idan ba ki ji tsoron Allah dan bakya ganin shi ba, kuma baki ji tsoron cutar da mijinki da ‘yar uwar zamanki ba, kuma ko baki tuna da komai ba don Allah don son Annabi ki tuna da mutuwa. Kar ki sai da lahirarki saboda wata mace, bayan ita kuma tana can tana kwashe dan abin da kika tara na aikin alheri.

Allah Ubangiji ya ba mu ikon ganewa, kuma mu gyara alfarmar Manzo Sallallahu alaihi wasallam.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: