Connect with us

MAKALAR YAU

Rashin Tsaro Tushen Asara: Kammalawa

Published

on

A can baya, an gabatar da wani abu daga tarihin Jagoran Kungiyar ISIL, Abu Bakr Al-Baghdadi. Yanzu kuma za a kawo kadan daga tarihin Ayman Al-Zawahiri na Kungiyar Al-Kaeda. Bayan shi, da yardar Allah sai a gabatar da tarihin Jagoran Kungiyar Taliban, Mullah Omar. Bayan kammalawa, sai kuma mu dawo nan Najeriya, mu tattara karfinmu kacokan a kan maganar Kungiyar Boko Haram, har zuwa lokacin da za mu karkare wannan tsokaci da ake yi game da Tabarbarewar Tsaro A Najeriyar Jiya Da Yau.

Gabanin kutsawa cikin batun Al-Zawahirin ne, nake son gabatar mana da wasu “yan tambayoyi kamar haka;

i-Me ya sa gabanin Kungiyar Boko Haram su fara kashe jama’ar gari da sanya bama-bamai cikin wannan Kasa ta Najeriya, ayyukan mutane irin su Mullah Omar da na Ayman Al-Zawahiri da na Abu Bakr Al-Baghdadi da ire-iren su ke burge mu?. A wancan lokaci, idan muka ji su suna antaya bama-bamai gami da yin kunar-bakin-wake a sassan Duniya, murna muke yi. ii-Da yawanmu, mu na da tunanin Addini ne suke aikatawa. Shin, me ya sanya kuma yanzu muke shafa-keya tare da kokarin canja tunani? Ko har yanzu cikinmu akwai masu mara musu baya ne a boye?. Me zai hana masu mara musu bayan su bayyana goyon bayan nasu a fili karara, tun da Addini ne suke yi?.

iii-Da yake Sallah da Azumi da Aikin Haji duka Addini ne da al’umar Musulmin Nijeriyasuke gani ake yi a sauran sassan Duniya, sai gashi mun dabbaka mu na yi dare da rana, ba tare da shayin kowa ba. Me ya sa wadanda ke ganin ayyukan da irin wadancan Kungiyoyin ke yi Addini ne, amma sai aka wayigari akasarin al’umar Musulmin Kasar nan ba su runguma ba, sai aka bar wasu tsirari ne ke aikatawa, suma bisa tallafi da agaji ne da suke samu daga Kasashen Turai. Me ya sa shi mai yin Sallah ko Azumi ko Zakkah, ba ya jiran samun tallafin Turai kafin ya yi?. Ai Addini duka Addini ne.

ib-Bisa wane dalili ne wadanda ke yabawa wadancan Kungiyoyi na waje, ba za su yabawa Kungiyar Boko Haram ba? Eh mana! Suna yin aiki iri-guda ne, kuma ma akwai alaka mai karfin gaske a tsakaninsu irin ta Yaro da Ubangidansa, shi ya sanya ma ake kawo irin tarihin iyayen gidan nasu da irin aikace-aikacensu, gudun farfagandar “yan musu. Ba za su je su yi bincike ba, amma komai aka fadi da yai hannun riga da irin fatawowin Malamansu, nan da nan ne kungurmin jahili zai tashi ya karyata.

Da daman lokaci, nakan rasa gane irin koyarwar Addinin da muke bi Wallahi. Idan mai karatu zai tuna, ko a nan Najeriya, sa’ad da “Yan Kungiyar Boko Haram ke hallaka Jami’an Tsaro su kadai, za a ga da yawanmu mu na yin murna ne. Mu na ma yin tunanin cewa ko Allah ne ya turo su su yi mana maganin Azzaluman Najeriya, musamman jami’an tsaro. To amma da tafiya-ta-yi-tafiya suka waiwayo mutanen gari fa? Ai daga nan ne aka fara neman tsari da su, aka fara fahimtar anya kuwa ma Addini ne ake yi cikin irin wannan salo?. Daga lokacin ne, batun a ce sunayin irin Jihadin da Dan Abdullahi S.A.W. ke yi ba ta ma taso ba!!!

Jagoran Al-Kaeda, Ayman Al-Zawahiri

Yanzu za mu tinkari wani abu daga irin tarihin wancan kasurgumin Shugaba na Al-Kaeda, wato Ayman Al-Zawahiri. Kamar yad da mai karatu zai gani a nan gaba kadan, Al-Zawahiri ne ya gaji jagorancin tafiyar da ayyukan Kungiyar ta Al-Kaeda, daga hannun Marigayi Osama bin Laden.

Haihuwar Ayman Al-Zawahiri

An haifi Ayman Muhammad Rabaie Al-Zawahiri ne ran 19 ga Watan Yuni, na Shekarar 1951 (June 19, 1951) a garin Maadi ta Cairo a Kasar Misra, Egypt.

An haifi Al-Zawahiri a babban gida ne. A gidan, akwai manya-manyan Likitoci da Mashahuran Masana fitattu. Saboda haka, sai shi ma Al-Zawahiri ya tashi a mai yawan son yin karance-karance tun yana Yaro Matashi. Tun yana Dan Shekara 14 ne a Duniya, ya fara shiga Kungiya mai jibi da Addini. Cikin Shekarar 1974 ne Al-Zawahiri ya kammala Digirinsa na farko a Jami’ar Cairo. Ya karkare Digirinsa na biyu ne cikin Shekarar 1978, inda ya karbi shedar karatun aikin Likitanci.

Al-Zawahiri kamar yad da aka bincina a sama cewa, shi ne Mutumin da ya dare bisa kujerar Shugabancin Osama bin Laden bayan rasuwarsa. Sannan, bayan harin Sha-daya ga Watan Satumba (September 11) ne, Kasar Amurka ta sanya ladar kudi har kimanin Dala Miliyan 25, ga wanda ya bayar da bayanan da suka taimaka zuwa ga damke Al-Zawahirin. Sai dai har yau din nan, ba su kai ga samun nasarar cafke shi ba.

Daga aure-auren da Ayman Al-Zawahiri ya yi, za a samu cewa ya yi aure akalla sau hudu ne. Cikin Matan da ya aura, akwai Azza Ahmed Nowari da kuma Umaima Hassan.

Al-Zawahiri da Matarsa Azza, na da “Ya”ya Mata hudu ne (4), Fatima, wad da aka haifa cikin Shekarar 1981. Ta biyun ita ce Umaima, wad da aka haifa cikin Shekarar 1983. Ta ukun Nabila ce, wad da aka haifa a Shekarar 1986. Khadija ce ta hudu, wad da aka haifa cikin Shekarar 1987. Sai kuma Da Namiji da ake kira da Muhammad, an haifi Muhammad ne cikin Shekarar 1987. Da shi da “yar’uwarsa Khadija, sun kasance Tagwaye ne da aka haife su a lokaci guda. Bayan Shekaru goma (10) da haihuwar Muhammadun ne, Azza ta kuma haihuwar “Ya Mace, aka sanya mata suna A’isha.

A Watanni shida na farkon Shekarar 2005 ne, daga cikin Matan dake da rai na Al-Zawahiri, akwai wadda ta haifa masa “Ya Mace, aka sanya mata suna Nawwar.

A karshen Watan Disamba na Shekarar 2001 (December 2001), Matar farko a wajen Al-Zawahiri da ake kira da Azza, da kuma “Ya”yaye biyu cikin shida da suke da su, wato Muhammad da A’isha suka gamu da ajalinsu, a sanadiyyar hare-haren da Sojojin Amurka suka kawo da jiragen yakinsu zuwa Kasar ta Afghanistan.

Hakika a garin Maadi, a na kallon gidan su Al-Zawahiri da babban gida na mutane madaukaka. Duka Iyayen nasa biyu, sun fito ne daga Iyalai masu karfin tattalin arziki da wadata ne. Muhammad, wanda yake Uba ga Al-Zawahiri, ya fito daga zuriyar da Allah ya yawaita tarin mashahuran Malamai a cikin su, ga kuma manyan Likitoci birjik. Mahaifin na Al-Zawahiri, Mohammed Rabie, bai bar Duniya ba, sai da ya zamto babba kuma kwararren Likita. A karshe ma dai, sai da ya zama Farfesa a fagen hada magunguna (Pharmacy) a Jami’ar Cairo.

Hakika Mahaifiyar Al-Zawahiri, Umayma Azzam, ta fito ne daga zuriyar Iyalai masu sukuni, sannan “yan kabilarsu ne masu karfin fada-aji a sha’anin mulkin Kasarsu. Mahaifinta Abdel-Wahhab Azzam kam sananne ne ainun: bajimin Malami ne, sannan ma ya taba rike Shugabancin Jami’ar ta Cairo. Bugu da kari, Mahaifin nata ne dai ya kirkiri Jami’a ta farko a Kasar Sa’udiyya, da ake kira da King Saud Unibersity, ya kuma jagoranci Jami’ar. Ya ma taba yin Jakada (Ambassador) zuwa Kasar Pakistan, lokacin da Dan’uwansa, Azzam Pasha yake Babban Sakataren Kungiyar Kasashen Larabawa.

Shi dai Al-Zawahirin, na da alaka ma kacokan da gidan Sarautar Sa’udiyya ta bangaren Uwa. Muna, wadda take “Ya ce ga Azzam Pasha, Kawunsa a bangaren Gyatumarsa, ta auri Muhammad, Dan Marigayi Sarki Faisal na Sa’udiyya.

Kara Samun Kwarewa A Fagen Karatunsa

Ta tabbata cewa, Al-Zawahiri, ya yi aiki ne a fagen aikin likitanci a matsayinsa na Likita. Cikin Shekarar 1985, Al-Zawahiri ya yi tafiya zuwa Kasar Sa’udiyya da niyyar sauke farali, tare da niyyar zama a can tsawon Shekara guda, ya yi aiki, don samun karin kwarewa a fannin da ya karanta na likitanci.

Bayan Al-Zawahiri ya kara samun kwarewa, ya zama kwararren Likita, Kungiyarsu ta hade da Kungiyar Al-Kaeda ta bin Laden. Bayan hadewar, sai Al-Zawahiri ya zama wani Mashawarci na musamman ga Osama bin Laden, kuma Likitansa. Cikin Shekarar 1986 ne, Al-Zawahiri ya fara haduwa da bin Laden a Jeddah.

Cikin Shekarar 1981 ne kuma Al-Zawahirin, ya yi wata tafiya zuwa garin Peshawar na Kasar Pakistan, inda ya yi aiki tare da Asibitin Kungiyar jinkai ta Red Crescent. A wannan Asibitin ne, Al-Zawahiri ya dukafa duba wadanda suka sami rauni daga “Yan-gudun-hijira. A nan ne kuma dai Ayman Al-Zawahiri ya hadu da Ahmed Said Khadr. An haifi Ahmed Khadr ne cikin Watan Mac na Shekarar 1948, ya koma zuwa ga Allah ranar 2 ga Watan Okotoba ne na Shekarar 2003 (March 1, 1948-October 2, 2003). Said Khadr, ya kasance Dan Kasar Canada ne. Ya fara aiki a Kasar Afghanistan ne cikin Shekarar 1980s. A Afghanistan, an zargi Khadr da yin ta’ammuli da Jagororin Kungiyoyin “Yan Ta’adda, cikin su ma akwai Osama bin Laden. Ta-kai-ta-kawo, Kasarsa ta Canada da Amurka, sun zargi Khadr da bai wa wadancan Kungiyoyi na “Yan ta’adda rancen makudan kudade.

Bayan Al-Zawahiri ya hadu da Said Khadr, sai alakarsu ta yi karfi matuka, sai ma suka fara tattauna bukatar kafa Gwamnatin Musulunci a Afghanistan, da kuma tattauna yadda za a magance wasu matsaloli da suka yi wa al’umar ta Afghanistan tarnaki.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!