Connect with us

RA'AYINMU

Maraba Da Yunkurin Hukumar JAMB Na Kawo Karshen Satar Jarrabawa A Kasar Nan

Published

on

A tsawon lokaci, sashen iliminmu yana tattare ne da abin da ya shafi batun satar jarabawa a kowane mataki. Hanyoyin satar jarabawar wadanda a kullum sabbi ne suke bullowa sai kara girma da habaka suke yi musamman ga wadanda suka dauke su a matsayin wasu hanyoyin kasuwanci suke kuma samun milyoyin kudade a kan hakan ta hanyar tatsan dalibai da iyayen daliban domin su taimaka masu yin magudin jarabawa har su kai ga samun takardun shaidar kamala karatu manya.

Saboda hakan ne ya sanya manyan makarantun kasar nan suke daukan daliban da ba su cancanta ba, suke kuma yaye masu digirin da ba su da aikin yi. Sai dai, hukumar shirya jarabawar ta shiga manyan makarantu ta kasar nan (JAMB), ta dauki wani kwakkwaran mataki na yin waje da masu satar jarabawar. Na baya-bayan nan, hukumar shirya jarabawar ta yi bincike, ta kuma kama tare da aukawa maza da mata da suka shahara a kan satar jarabawa, wadanda sukan yi rajista su kuma rubuta jarabawar ba ma ga mutum guda ba, har ga dalibai masu yawa a kowace shekara.

Irin wadannan takadaran, sun shirya cutar na su tsaf, suna ma da cibiyoyi  na musamman inda duk ‘ya’yayen wadanda iyayen su a shirye suke da su saya masu jarabawar ta hanyar cuta da sata, sukan ziyarce su domin su sama masu hanyoyin shiga jami’o’i. kamar yanda rahotanni suka nuna, an kama daruruwan iren wadannan daga kowane sashe na kasar nan, ana kuma bisa kokarin ganin an kama sauran duka, har ma da iyayen wadanda ba sa son ganin wani abu ya hana ma ‘ya’yan su damar shiga manyan makarantu a kasar nan ta kowace hanya ce kuwa.Domin irin wadannan iyayen duk suna cikin masu yin wannan irin mumunan aikin, domin su ne suke neman wanda zai rubutawa ‘ya’yansu jarabawar. Magudin jarabawa a wajen wannan jaridar, abin damuwa ne, ba ma kadai haramun ne ba, yana ma da mummunar cuta ga al’umma, don ganin an magance wannan matsalar, muna shelanta goyon bayan mu ga abin da hukumar ta JAMB ta ke yi na magance matsalar ta satan jarabawar daga cikin tsarin ilimin mu.

Muna sane da matsalar da satar jarabawa ke janyo wa kowace irin gwamnati, don haka, muna da cikakken amincewa da dukkan matakan da hukumar ta JAMB take dauka na ganin ta magance matsalar satan jarabawa daga cikin tsarin ilimin mu. A watan Maris na wannan shekarar, Duniya ta sha mamaki da jin cewa, hatta ma a cigababbun kasashe kamar na Amurka, inda mutum zai yi tsammanin tsarin na su kammalalle ne, wai ashe shi ma yana fama da matsalar ta satar jarabawa.

Muna kuma goyon bayan matakin shelantawa da kunyata  hatta iyayen da suke karfafa ‘ya’yansu a kan aikata laifin satar jarabawar, kamar yanda ake yi a kasar Amurka. Ya kamata a karfafi hukumar ta JAMB da ta dauki irin wannan matakan a nan Nijeriya. Yin hakan zai kasance jan kunni ga saura.

Muna kuma hada baki da hukumar ta JAMB, wajen lallashi da bayar da hakuri ga daliban da wannan lamari ya rutsa da su duk da cewa su sun yi aiki ne tukuru wajen shiryawa daukan jarabawar, amma sai ga shi sun sami jinkiri a wajen sakin sakamakon jarabawar na su, a wasu lokutan ma har ta kai ga soke sakamakon jarabawar na su. Ya kamata irin wadannan daliban su fahimci cewa, da zaran an kammala tantance nagari daga na banza a cikin su, an kuma yi watsi da na banzan, tsarin zai koma daidai ne a yanda ya kamata ta yanda duk dan kasa nagari zai ji dadin sa.

Duk wanda zai yi magudi a wajen jarabawa, zai iya yin magudi a kowane lamari na rayuwa ma. Don haka, muna yin kira ga duk sassan shirya jarabawa da su yi koyi da wannan yakin da ake yi a kan wannan mummunar cutar da take neman cinye mana tsarin ilimin mu.Tilas ne su duba a duk sassan su, duk inda yake da wata kafa ta bayar da damar yin satar jarabawa su tabbatar da sun toshe ta. In har an yi hakan, zai zama tilas ga dalibai su yi aiki tukuru domin samun maki mai kyau, wannan kuma shi ne zai ba su dama ya kuma shirya su a kan fannonin da suka sanya a gaba, ya ma yi masu tanadin zama shugabanni nagari a gobe, wadanda za su kasance da gaskiya masu kuma yin aiki tukuru a cikin al’umma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!