Connect with us

RIGAR 'YANCI

Mata Muke Son Su Fi Morar Gwamnatin Bauchi – Hajara Gidado

Published

on

HONORABUL HAJARA JIBRIN GIDADO Daya ce daga cikin matan da suka kasa suka tsare wajen tabbatar da nasarar Sanata Bala Muhammad a matsayin gwamnan Bauchi, ‘yar siyasa wadda ta fito takatar majalisa a zaben 2019 daga mazabar Itas Gadau, kuma ita ce Daraktar kungiyar ‘National PDP Woman Parliament’ reshen jihar Bauchi. A hirar ta da LEADERSHIP A YAU ASABAR ta bayyana cewa fatansu shi ne mata su mori gwamnatin yadda ya kamata. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ki gabatar wa jama’a da kanki?

Sunana Honorabul Hajara Jibrin Gidado, na fito daga karamar hukumar Itas Gadau a cikin jihar Bauchi.

Ta tabbatar Sanata Bala ne sabon gwamnan jihar Bauchi, mene ne kike ganin ya kai ga nasarar jam’iyyar PDP?

Nasarar da jam’iyyar PDP ta samu ta samu ne a sakamakon wanzar da adalci a tsakanin mambobi da kuma gudanar da hakikanin zaben fitar da gwani bisa cancanta da kuma dacewa wanda hakan ya fitar da Sanata Bala Muhammad a matsayin dan takara. Shugaban jam’iyyar PDP da ita jam’iyyar sun yi tsayuwar daka wajen tabbatar da an yi wa kowa adalci a lokacin zaben fitar da gwani na cikin gida; wannan ba kawai ga zaben gwamna ne PDP ta tabbatar da yin zaben cikin gida da ya dace ba, ga kowace kujera an tabbatar da yin abun da ya dace, shi ya sa wadanda suka fadi suka dawo suka mara ma wadanda suka ci baya, don ki ni kaina na yi takarar majalisar jiha ban kai ga nasara ba, amma na bayar da hadin kai ga wanda ya ci don a nemi nasara a babban zabe. Tabbas wannan ya taimaka wa jam’iyyar PDP matuka gaya.

Wadanne shawarwari kike da su ga Sabon gwamnan?

Wannan nasarar da muka samu mun dauketa ne a matsayin Allah ne ya fitar da mu daga cikin wani kangi da muka samu kanmu a ciki a wannan jihar, idan ka duba yadda jihar nan ta dauki harami da an ci gaba da tafiyar a haka gaskiya da akwai gagaruman matsaloli domin kuwa ko’ina a tsaye yake, ko ta ina matsaloli ne suka mamaye jihar. Amma cikin ikon Allah sai Allah ya duba addu’o’inmu ya amsa ya kawo mana dan kasa, mai kishin jihar, mai kishin talaka wanda muke da tabbacin yana da kyawawan kudiruri wa jihar Bauchi yana kuma da niyyar gyara. Don haka mun tabbata zai yi abun da ya dace a lokacin da ya dace. Wani karin tagomashi ma shi ne, mutanen da suke kewaye da shi ‘yan kasa ne masu kishin kasa don haka haduwa za a yi a taimaka wajen tafiyar da komai yadda ya dace.

Abu guda da ya dace ka lura shi sabon gwamnanmu ba wai kudi ne ya zo nema ba, wadanda suke kewaye da shi ba wai fatarace ta damesu suke neman mafaka ba, damuwar kowa da ke tare da Sanata Bala shine jihar Bauchi, ya za a ceto jihar, ya za a inganta jihar.

Shawarar da zan bayar shine, ka ga a jihar Bauchi gaba daya kashi 75 da suka fito suka yi zaben nan mata ne, shawarata mai girma gwamnan jiharmu Sanata Bala ya yi kokarin wajen tabbatar da cewar mata sun mori gwamnatinsa saboda gwamnatocin da suka shude sun yi wofi da mata wajen tafiyar da harkokinsu, matan nan sune suke wahala amma sai an zo cin gajiyar gwamnati a yasar da su, idan ka je INEC matan nan dai za a ka gani su kwana su wuni, suka dage wajen cewar a tabbatar musu da wanda suka zaba shine Sanata Bala kowa ya san haka ne ya faru a Bauchi, wannan tsayuwar dakar da iyaye mata suka yi ya firgita kowa na cewar lallai sai an tabbatar da wanda jama’a suka zaba ba tare da yin magudi ba.

Ni abun da na ke son na ce shine a tabbatar da shigar da mata da matasa cikin sha’anin tafiyar da gwamnati, gwamna ya jawo mata sosai a jikinsa ya daurasu a mukaman da suka dace domin sune suka san zafin matsalar da al’umma take ciki, sune suka san yadda za a yi a taimaki al’umma. Jawo mata zai taimaka wajen tafiyar ta yi kyau, mata sune masu tausayi, sun eke rike gida masu tafiyar da mai gidan ma.

Batun kaso 35 na damar da ake son a baiwa mata muna son gwamnanmu ya aiwatar da hakan, duk da muna da kwarin guiwar gwamnanmu zai baiwa mata dama kaso 35. Sannan ina fatan dukkanin alkawuran da aka dauka a lokacin yakin neman zabe a tabbatar an aiwatar da su, fatanmu shine kyawawan halayen sabon gwamna da muka sani ya kara ninkasu wajen tafiyar da gwamnatinsa.

Wadannes hanyoyi ne kike ga ya dace sabuwar gwamnatin ta bi domin kar a maimaita jiya?

Na ji dadin wannan tambayar domin kuwa tabbas gwamnatin da ta gabata ta tafi da mata, amma abin tambayar matan da suka dace? Abu guda biyu ne ake nema don cimma nasara, na farko a samu gogaggen wanda ya gwanance kan sashin da za a sanya shi, na biyu dan siyasa. Idan kana gwamna ka san matan da suka maka wahala suka sha maka gwagwarmaya da za su iya kare maka muradinka da kimarka ko bayan idonka, wato Jakadu na kwarai. A maimakon haka, a gwamnatin baya sai ka ga son rai da ni na san wane ya shigo a maimakon a tsaya a zabu matar da suka dace suka san aikinsu suka kuma san siyasa. Shi dan siyasa na da nashi fa’idar kuma wanda yake da kwarewa wa yana da tasa fa’idar don haka ina ga ya dace ne a zabo matan da suka dace wadanda za a ba su damar da za su iya taimaka wa mata na kasa da su, yin hakan zai taimaka wa gwamnatin nan, kuma zai taimaka wajen kauce wa matsalolin da gwamnatin baya ta samu da yanzu haka matan suke kokawa.      

Bar ka ji, ai matan da gwamnatin baya ta yi tafiya da su sun taimaka wajen faduwar gwamnatin ta hanyoyin da suka bi na kin jawo mata talaka a jika da musu abun da ya dace. Domin su fa korar mata suke yi a jikinsu a maimakon su jawosu a jikinsu.

Ga matar Kauran Bauchi kuwa ganin cewar ita mace ce kila ta ce za ta jagoranci wani fannin inganta rayuwar mata me za ki ce gareta?

First Lady dinmu Hajiya A’isha Bala Muhammad iya bakin kokarinta wajen taimaka wa mata domin tun kafin ma a zo ga wannan matakin tana da kungiyarta mai zaman kanta ALMUHIBBA ta cikin wannan gidauniyar tana taimaka wa matasa sosai, kuma idan ka duba kalamanta a lokacin yakin neman zabe ko’ina ta je mata take cewa, matan nan dai sune a gabanta. Sannan ina kira a gareta ta kara himma a kan himma domin kowa ya ga ya tsayu yana abun da ya dace to waiga bayarsa akwai taurarun da ta tsaya masa itace matarsa. Fatanmu anan shine ta ninka kokarinta akan kokari domin matan da suke cikin halin neman agaji su samu rayuwa mai inganci.

Mene ne fatanki ga ‘yan uwanki mata?

Babban fatana kuma da yardar Allah hakan zai kasance shine mata za su mori gwamnatin sanata Bala sosai bisa ga ababen da ke akwai da yardar Allah mata za su mora sosai. Babban abun nema a nan dai shine da mu matan da maza da kowa da kowa ma, mu sanya Sanata Bala da gwamnatinsa cikin addu’a su samu nasarar sauke nauyin da ke kansu kuma Allah ya ba su damar tafiyar da harkokin gwamnati yadda ya kamata domin jihar ta samu kyautatawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: