Connect with us

KASUWANCI

Satar Man Fetur: Gwmanatin Tarayya Zata Fara Tura Na’urorin Tsarorin Na Musaman Na Dala Miliyan 195 A Yuni

Published

on

Tsohon Ministan sufurin jirage kasa Mista Rotimi Chibuike Amaechi ya sanar da cewar, Gwamnatin Taraya zata tura na’urori  da jami’an tsaro na musamman don baiwa tekuna  kariya a cikin watan Yuni don dakile ayyukan barayin man fetur.

Acewar Mista Rotimi Chibuike Amaechi, ana sa ran kammala aikin a farkon zangon shekarar 2020, inda ya kara da cewar, akin na dala miliyan195  kamfanin HLSI na kasar Isira’ila aka baiwa kwangilar wanda an taba bayar dashi a shekarar 2017 ka kuma soke kwangilar a shekarar 2018 saboda wasu lamuran tsaro na cikin gida da suka bijiro a lokacin.

Mista Rotimi Chibuike Amaechi,  yaci gaba da cewa, a cikin watan Agusta aka samu daidaito akan kwangilar kuma na’ourorin da za’a smar sun hada da jirgi mai saukar Angulu, jirage, jiragen ruwa uku na yaki da sauran kaya.

Mista Rotimi Chibuike Amaechi  wanda ya sanar da hakan a ranar  Talatar data gabata a  taron masu ruwa da tsaki a jihar Legas ya yi nuni da cewar, lamarin tsaro a tekunna kasar nan ya kazanta, inda hakan ya sanya Shugaban kasa Muhammadu Buhari  ya mayar da hankali don maido da tsaron a  manyan tekunna dake kasar nan.

Tsohon Ministan sufurin jirage kasa Mista Rotimi Chibuike ya kara da cewa, mahimmancin bawai kawai tura na’urorin bane hara yakar barayin masu fashin man fetur akan tekuna, a cikin watan Yuni muke son fara tura na’urorin.

Acewar Mista Rotimi Chibuike Amaechi,” Muna tunanin daga watan Yuni da kuma farkon zangon shekarar 2020, zamu kammala kai na’urorin, inda idan yaso dukkan wani abu na lamarin satar man data sake auku kuna iaya zargin mu.”

Ya kara da cewa,  a daidai loakcin mun kammala baiwa jami’ain na musamman da za’a tura horo kuma na’urorin rindinar sojin ruwa ce zata kula dasu.

Jami’an sun hadada, sojoji, yan sanda, jami’an soji na sama, jami’an DSS da kuma na NIMASA
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!