Connect with us

ADABI

Tattaunawa Da Khadeeja Candy Marubuciyar Littafin Ban Zata Ba

Published

on

Gabatarwa

Sunana Hadiza Abubakar, amman an fi sani na da Khadeeja Candy. An haife ni a Sakkwato. Na yi karatu na a Sakkwato, na girma a can, amman yanzu ina garin Zamfara da zama. Ni marubuciyar ce ta  Intanet mai fafutukar zama yar jarida.

Me ya ja hankalinki kika faxa harkar rubutun littafan?

Gaskiya ra’ayi ne kawai. Na taso da sha’awar abin ne tun ina qarama.

A wace shekara kika fara rubutu?

Na fara rubutu a qarshen shekara ta 2014.

Wane littafi kika fara rubutawa?

Littafin Ban Zata Ba, shi ne littafina na farko.

Me littafin Ban Zata Ba yake qunshe da shi a taqaice?

Labari ne na wata yarinya wadda mahaifinta yake ba da ita sadaka ga xan mai gidansa, shi kuma ba ya sonta saboda yana tunanin ba matsayinsu xaya ba, zai ta wulakanta yana cin zarafinta, ashe shi kuma abokinsa ya soma sonta.

Saboda haka, a taqaice dai labara ne mai koyar da wulaqanta xan’adam babu kyau, kuma barin abokanka na shiga cikin lamarin aurenka matsala ce babba.

A yanzu littafanki sun kai nawa? Masu karatunmu za su so sanin sunansu.

Zuwa yanzu na rubuta litattafai goma sha xaya. Wato:

Lamarin Duniya.

Lamarin ‘Ya’yana.

Ban Zata Ba.

Saleena.

Deenah.

Mairo.

Babban Goro.

Babbar Jaka.

Khadijatu.

Saifullah ko Habibullah.

Sai wanda nake rubutawa yazu  Zagon Qasa.

Cikinsu wanne ne bakanda miyarki?

Littafin da na rubuta na Khadijatu shi ne ya fi burge ni.

Ko za ki yi wa masu karatunmu  bayanin dalilinki na zavar littafin Khadeejatu a matsayin gwarzonki?

Saboda labarin yana tava zuciya, kusan duk wanda ya karanta sai ya yi kuka. Kuma a lokacin da na yi ba a yi littafi mai irin sunan da ya game kafafen sadarwa ba, shi ya sa na zavi sunan saboda sunana na yi littafin a kansa.

Me ya fi ba ki wahala yayin rubutu kuma me ya fi yi miki sauqi?

Gaskiya irin littafi da nake a yanzu Zagon Qasa shi ya fi ba ni wuya saboda akwai abubuwa da yawa a cikin tun daga na rashin lafiyar HIV da kuma harkar Sojoji. Sai kuma littafin Babban Goro shi ma ya ba ni wuya, saboda matsalar “blood cancer”. Da “sickler” saboda abubuwa ne da dole sai ka yi bincike a kansu, ka nemi likitoci sun yi maka bayani kafin ka aikata. Littafi mai bincike ya fi ban wahala gaskiya.  Littafin mai labarin kawai ba wani ciwo ko wani aiki na daban ya fi ban sauqi.

A labarin Babban Jaka kin yi bayani ne a kan wata yarinya wadda ta gamu da qaddara wanda har ta kai ta ga haihuwar xiya, alhalin ba ta tava sanin namiji ba.

Tambaya ta a nan ita ce, me ya ja hankalinki wurin rubuta labarin? Ko ya faru da gaske ne? Ko kuma qirqirarsa kika yi don warware wasu lamura?

Gaskiya labarin qirqiraren labari ne. Saboda a lokacin ana labarin soyayya ne, ni kuma sai na xauki wannan jigon don kawo wani abu na daban.

Sannan kin ga ai an nuna an yi mata dashen qwan ne ba tare da ta sani ba, har ta haifi ‘yar da ba ta san ubanta ba. Wannan kaxai, wani sabon abu ne a wancan lokacin.

Kin tava fuskantar qalubale a kan rubutunki wanda har ya xaga miki hankali?

Gaskiya ban fuskanci qalubale irin na sauran marubuta ba, sai dai xan abin da ba za a rasa ba,  wanda kowane marubuci ba ya wuce shi.

Wace nasara kika samu wadda ba za ki tava mantawa  da ita?

Gaskiya na samu nasori ba ma nasara ba. Kuma muna kan samu.

Na haxu da mutane masu yawa, waxanda ban tava tunanin haxuwa da su ba. Sannan na tava cin gasar kamfanin Sajee Novels shi ma babbar nasara ce. Sanadin rubutuna kuma ya sa wata jarida ta xauke ni aiki. Sannan ina samun alheri na xaixaikun mutane, Alhamdulillahi.

Ko a wannan kawai muka tsaya nasara ce ba mu san abin da zai zo gaba ba kuma.

Wace ce gwanarki a cikin marubuta na publishing da kuma na online?

Gaskiya gwanata ita ce Khadeeja Candy.

Hhhhh  saboda haka Ni ce.

Me ye kiranki ga mabuta da kuma masu karatu?

Mu masu rubuta abin da idan an karanta za a amfana. Su kuma marubuta su zama masu xaukar darasin da ke cikin littafi da amfani da shi.

Me za ki ce game da saida littafansu da yanzu ma fi yawancin marubuta suke yi ta online?

Gaskiya an samu sauyi ba kamar baya ba, da za ki ga ana ta rubuto kan soyayyah kawai.  Yanzu ana samun canji sosai ana abubuwan qaruwa. Sai dai duk da haka akwai waxanda labarin kawai ake zubawa ba ka san inda ya dosa ba.

Wane jan hankali za ki yi ga masu wannan xabi’a kuma a matsayinki na tsohuwar marubuciya wace gudummowa ya za ki ba su a kan abubuwan da ya kamata su yi iliminsa kafin su soma rubutu?

Wato akwai buqatar ka san kanka kafin ka xora alqalaminka na rubutu. Sannan ka zama mai rubutu akan abin da zai iya faruwa ko kuma yake kan faruwa. Sannan kar kullum jigo ya zama na soyayya kawai ko kuma na kishi kawai ko kuma cin amana kawai ya zama ko ina kana tavawa. Hakan zai ba ka damar kai wa inda ba ka tava mafarki zuwa ba.

Shin koyon sanin qa’idojin rubutu wajibi ne ga marubuci ko kuwa ganin damarsa ne da ya koya da kar ya koya dik xaya?

Wannan kam wajibi ne. Ai qa’idojin rubuta da jigo su ne rubutun gaba xaya.

Wane abu kika fi so a rayuwarki kuma me kika fi qyamata?

Ina son Mamana sosai. Ina son mutum mai gaskiya da riqon amana, kuma ina son mutum da ya san kansa.

Ina qyamar mutum mai min zagon qasa da wanda zai so ni don wani abu nawa. Da wanda zai je bayan idona ya faxi abin da ba zai iya faxa a gabana ba.

Kina da qawaye kuwa Hajiya Candy?

Gaskiya ba ni da qawa a kafar sadarwar sada zumunta kamar Matar mood Safiya Mista. J Moon.

A cikinsu wace ce Aminiyarki ta qud da qud?

Ba ni da qawa ta qud da qud don qawaye sai a hankali.

Wane saqo kike da shi game da yanayin rayuwar al’umma da kuma cin amana da ya zamo ruwan dare cikin al’umma?

Ka ji tsoron Allah kuma ka sa shi a kan dukkan lamarinka. Ko waye ya cuce ka sai ya ga babu kyau. Masu cuta kuma a ji tsoron Allah a daina don ba hanya ba ce mai vullewa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: