Connect with us

ADABI

Asadul Muluuk (46)

Published

on

“Babu shakka wannan batu haka yake, amma fa idan da mai martaba ya sanyaya zuciyarsa da ba zai dauki wannan matakin ba, hukuncin da ya dauka na wannan tafiyar ya yi mana tsanani, ina za mu sanya wannan jaririyar soyayya haka. Kai ni fa na fara fidda rai da ci gaba da rayuwa a doron kasa, kasancewa ta mai nisata da kai.” Sai ta sake fashewa da kuka, ganin haka sai hankalinsa ya fara tashi, dama ya zo mata a hakan ne ko ita ma ranta zai dan yi sanyi su dauki abin da sauki.

“Haba Gimbiya kina sane da yadda nake jin zubar hawayenki kuwa? Wannan ba karamar musiba ba ce, kasancewar masoyinka a gaban kuma yana zubar da hawaye, ba zan iya jurar ganinki a wannan yanayin ba.” Ta ce; “Ya Asadulmuluuk hawayena kake gani idan da hali ka taya ni yin kuka, in babu hali to ka sanya idanu har in kare.

Kukan da nake yi a yanzu kai kadai kake gani, amma idan an tafi a haka sai wata rana ka yi kukan da kowa ya jiyo sautin kukan ka.”

Na san zan iya kwanciya rashin lafiya a ya yin da zuciyata ta motsa don son ganinka ba ta samu ba, wala’alla na samu saukin tashi, la’alla kuma ta zamto tafiyar da babu waiwaye balle dawowa.”

Asadulmuluuk bai san sa’adda ya sanya hannu ya rufe bakinta ba, ya ce; “Yalla ko kin san gaibu ne cikin lamarin da zai zo nan gaba har kike tarar sa? “Ina jin abin da nake ji a jikina daga sa’adda ka fara maganarka har kawo wannan lokaci da nake mayar da nawa bayanan, bugun zuciyata ya sauya daga yadda na ke ji a ko da yaushe.

Ta yaya kuwa ba zan san abin da zai iya faruwa ya yin da abin ke ci gaba ba? Na san ba za ka gasgata abin da na fada ba ko da hakan zai tabbata.” Ta ciro wani zobe na danyar zinariya ta mika masa, ya karba, ya ce; “Ina ma’anar haka?” ta ce; “ Idan ka isa gida ka bawa umma wannan ka ce ta ajiye kafin in zo mata ina matsayin ‘yarta kuma suruka.”

Asadulmuluuk ya saki fuskarsa ya yi murmushi, ya ce; “Ki saki fuskarki mana ya zamto mun kare wadannan kwanaki cikin nishadi don mu karawa junanmu kwadayin aure.” A nan sai ta saki fuskarta har ta yi murmishi.

Bayan sun yi sallama Badee’atulkhairi ta samu mahaifinta da maganar, shi ma ya fada mata kamar yadda ta ji daga bakin Asadulmuluuk, amma sai ya kara mata da cewa, ai ko da za su bar kasar nan sai an bar masa dansa Asadulmuluuk, ko don ganin yadda kuka shaku da shi. Ta ce; “Ranka ya dade ai wannan ba abu ne mai yiwuwa ba, a ce mahaifinsa ya tafi ya bar shi a wannan Kasar.

Idan fa ba ka yi maganin waziri ba wata rana zai jawo mana aikin da za mu ji kunya, kuma ina mai yi maka rantsuwa in har ba’a gyarawa waziri zama ba, to wata rana sai ya halaka mu kuma an bautar da, in bah aka kuma to muna ji muna gani sai dai mu dare don yin hijra daga wannan kasa ta mu.”

Sarki ya fusata ya hantare ta “ Ki tashi ki fita daga nan, ka da ki sake zo min da kalami mai kama da haka.” Karo na farko kenan da sarki ya fara yi mata tsawa. Ta koma wurin mahaifiyarta da maganar ita ma ta je wa sarki, nan ma ya koreta.

Ta dawo daki cikin bacin rai, Badee’atulkhairi ta tare ta ta ganta cikin wannan hali sai ta ji a duk duniya babu wanda ta ke kyama kamar waziri.

“Na rantse da Ubangijin Ka’aba ni zan kawo karshen mulkin waziri a kasar nan.” Mahaifiyarta ta yi sauri ta rufe mata baki ta ce; “ Kada in sake jin wannan kalami daga bakinki,” ta juya ta koma dakinta.

Ranar Alhamis da misalin da safe sarakunan duka suka taru za ayi addu’ar bankwana da kuma nasihohi, an taru ne a wani katafaren daki mai girman gaske, saboda ko wane sarki ya zo da jama’asar ne. Bayan kowa ya fadi albarkacin bakinsa, sai aka bai wa waziri damar yin magana, da ya tashi zai fara magana sai da kalli mahaifin Asadulmuluuk kallo na raini sannan ya ce; “Mu dai fatan mu kowa ya sauka Kasarsa lafiya, amma na janye bukatar sarki da ya ce, a bar Asadulmuluuk a nan, kai Asadulmuluuk ka shirya ka bi mahaifinka ku koma kasarku, saboda mu kasarmu ba Kasar yaki ba ce Kasa ce ta zaman lafiya da kwanciyar hankalin.” Yana gama fadar haka sai mahaifin Asadulmuluuk ya ce; “ Ina umartar Abdulkarim ya fita daga wannan zauren.” Sai aka wani sadaukin matashi ya tashi tsaye takobinsa a zare hawaye yana zuba daga idanunsa.

Abdulkarim shi ne mutum daya da baya yarda a fadi maganar da za ta sosawa sarki rai, yanzun nan za ka ga kai a kasa yana tsalle, ashe shi sarki ya ga sa’adda yake kokarin zare takobinsa ya tsinke kn waziri, wannan hanashin da aka yi shi ne dalilin da ya sa yake zubar da hawaye. Daga nan aka yi addu’a aka tashi kowa ya zauna da shirin gobe zai kama hanyar sa ta koma Kasarsa.

Da ranar Juma’a ta zagayo tun da safe Asadulmuluuk ya sa aka shirya kayansa ya zamto babu wani abu da ya yi saura a kasa, tunda ya sa a ka kammala masa shiri, ya tafi wurin Badee’atulkhairi suka fara hira cikin bacin ran rabuwarsu. Suna zaune cikin wannan yanayi, sai ga wata baiwa nan aguje ta zo ta fadi gabansu ta yi gaisuwa tana haki tana ba su labarin cewa, “Ranku ya dade majalisin sarki ya hargitse, ga shi can za a fara kashe-kashe.” Suka  mike tsaye gaba dayan su cikin hanzari suka yo waje suna sassarfa, kafin su karaso Asadulmuluuk ya ji sautin zare takubba na jama’ar kasarsu. Ya karaso a guje da isarsu suka ga wani irin gajimaren hayaki ya fito daga wurin, suna shiga suka ga mahaifinsa a tsaye a kan waziri ga dan yatsarsa a kan hancin wazirin.

Da yake shi mutum ne mai fadi da girma ga tsayi. Kalmal da suka ji ta fita daga bakinsa ita ce, “Ka ci albarkacin Imani, cewa ni musulmi ne da na sa an ci namanka danye yanzu, idan kuma kana inkari ka ce min kanzil ka gani, tsohon fajirin wofi, wannan ba kin na ka shi zai kai ka ga hallaka.”

Ya waigo ya ga Asadulmuluuk tsaye ga Badee’atulkhairi kusa da shi, da suka hada ido da shi sai suka sunkuyar da kai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!