Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Sagegeduwa’

Published

on

Suna: Sagegeduwa

Tsara labari: Fauziyya D. Sulaiaman

Kamfani: DAN HAJIYA FILMS PRODUCTION

Daukar Nauyi: Garzali Miko

Shiryawa: Naziru Dan Hajiya

Bada Umarni: Sunusi Oscar 442

Sharhi: Musa Ishak Muhammad

Jarumai: Ali Nuhu, Abba El-mustafa, Baballe Hayatu, Shehu Hassan Kano, Zulaihat Ibrahim, Bilkisu Abdullahi, Bilkisu Shema, Teema Yola, Ainau Ade, da sauransu.

Labarin fim din Sagegeduwa labari ne da aka gina shi a kan labarin wani bawan Allah mai suna Ali (Ali Nuhu) wanda ya samu kansa a cikin wani yanayi wanda kaddarar auran mata har guda uku ta same shi a cikin sati biyu. Ta zo masa ba tare da ya shiryawa hakan ba. Kowanne ya zo masa ne bisa wani dalili da yake gani a matsayin mai karfi ne a gurinsa.

A farkon shirin an nuno Ali ya zo gidan abokinsa Idi (Abba El-Mustafa) yana kwankwasa kofa inda aka jiyo muryar Idi yana cewa waye yake buga masa kofa da sassafe haka? Yana budewa sai yaga abokinsa ne Ali, sai ya bude masa suka shiga cikin falo suka zauna sai yake bashi labari cewa ai yazo neman shawararsa ne akan wasu matsaloli da suke damun shi. Shi ne yake fada masa cewa ai bayan tafiyarsa ya yi aure na mata har guda uku kuma a cikin sati biyu kawai. Sai idi yake fada masa cewa wannan maganar banza ce ta ya ya zai iya auren mata har guda uku a ckin sati biyu? A nan Ali ya fara bashi labarin yadda abun ya kasance.

Ya fara da cewa mata ta farko wato Sameera (Bilkisu Shema) ya aure ta ne sakamakon kade ta da ya kusa yi da  mota. Shi ne take fada masa cewa babanta ne bashi da lafiya yana kwance a asibiti  yana fama da ciwon hawan jini, wanda a wannan asibitin ne aka daura auren nasu.

Ita kuma ta biyu Sunanta ya aure ta ne sakamakon fasa aurenta da abokinsu ya yi ranar daurin aurensu,sai mahaifinta ya nemi taimakon cewa ya taimaka ya aure ta saboda wannan shi ne karo na shida da aka fasa aurenta. Kuma har ta yi ikirarin kashe kanta idan aka kara fasa auren nan.

Ta uku ita kumaSunanta Fatima (Zulahat Ibrahim) ya aure ta ne sakamakon cetonta da ya yi lokacin da ta gudu daga gida saboda kar a yi mata auren dole, bayan ya dawo da ita gida ne sai yayanta ya yi alkawarin bashi aurenta tare da biya masa sadakinta.

A gefe guda kuma Ali yana da yarinyar da yake da burin aure tun asali wato Ummulkhairi (Teema yola) wanda suka dauki dogon lokaci suna soyayya. Ita ma dai Ummulkhairi yarinya ce mai gata wanda take a hannun kawunta wato Babale Hayatu da kuma matarsa Karime (Aina’u Ade).

Toh a haka Ali ya dinga rayuwa tare da matansa guda uku a unguwa daya, amma ba tare da ko wacce ta san da zaman ‘yar uwarta ba. Ali dai ya kasance yana da mahaifiya wacca take zaune a garin Kaduna sai kuma mahaifinsa wanda yake a garin Sokoto. Duka wadannan iyayen nasa basu san da labarin wannan auren nasa ba har sai wata rana mahaifiyar shi ta kira shi a waya take tambayar shi shin da gaske ne ya yi aure sai yake ce mata eh ya yi aure, kuma abin ne yazo masa babu shiri shiyasa bai fada mata ba, saboda Babansa ne ya  tilasta masa da ya auri ‘yar abokinsa.

A daya bangaren kuma gidansu Ummulkhairi sun matsa wa Ali a kan cewa lallai-lallai ya fito ya auri Ummulkhairi idan har da gaske yake. Suka umarce shi da ya aiko da magabatansa domin a tsaida maganar aurensu, wanda hakan ya tilastawa Ali sanar da mahaifinsa wato (Shehu Hassan Kano) domin ya zo ya nema masa aurenta, wanda kuma hakan ya sa ya zo garin Kanon domin nemawa Ali aure na farko a tunaninsa ba tare da sanin cewa aure na hudu zai nemar masa ba.

Iyayen Ali sun fuskanci halin da yake ciki ne bayan mahaifiyarsa ta zo kuma ya sauketa a gidan matarsa ta farko wato Sameera, shi kuma mahaifinsa ya sauke shi a gidan abokinsa wato Idi. Wata rana mahaifiyar Ali ta fito kawai sai suka hadu da mahaifin Ali yana zaune yana karanta jarida, sai yake tambayar ta me ya kawota nan sai take ce masa ai ta zo ne gurin Ali kuma tana zaune ma yanzu haka a gidansa, sai yake ce mata ai shi ma kuma yazo ne nan domin nema masa aure, inda daga nan kuma suka tattara suka tafi gidan Idi, inda  anan ne Ali ya basu hakuri amma duk da haka bai fada musu cewa aure uku ya y i ba.

Asirin Ali ya tonu ne bayan Ummulkhairi ta dora hotunsu na sa ranarsu inda kuma a nan ne matarsa ta gani wadda kuma kawa ce ga Ummulkhairi. Daga nan ta taso ta taho gurun kawayenta su Sameeera wadanda suke zaune unguwa daya da su. Wanda kuma dukkansu suka ga hoton kuma suka shiga mawiyacin hali saboda dukkansu sun gane mijinsu ne a jikin hoton. A nan suka yanke shawara cewa kawai su tashi dukkansu su tafi gidansu Ummulkhair.

Zuwan su gidansu Ummulkahiri ke da wuya sai kawai suka samu Ali a cikin gidan suna tare da Umulkhairi. Bayan sun kirawo Ummulkhairi ne suka sanar da ita abinda yake faruewa. Kawai sai ta janyo su gaba daya suka karasa inda yake, tana ce masa ya fada mata abinda matan nan suke fada gaskiya ne ko ba gaskiya ba. Ana cikin hakan ne sai ga mahaifin ALI nan da mahaifiyarsa da kuma Idi suma sun shigo wannan gidan, inda a nan aka hadu ga ALI, ga mahaifansa, ga Idi abokinsa, ga matansa uku ga kuma Ummulkhairi da kawunta da kuma matar kawunta. A nan ne aka bawa Ali dama ya yi cikakken bayanin yadda aka yi ya auri duka matan nasa. Daga nan kuma kowa ya karbi uzurinsa kuma kawun Ummulkhairi ya yi masa alkawrin bashi Ummulkhairi da kuma bashi gidan da zai zauna da duka matan nasa guda hudu.

ABUBUWAN YABAWA

 1. Labarin ya yi nasarar isar da sakon da ake da bukatar isarwa.
 2. Fim din ya nishadantar kwarai da gaske.
 3. Babu matsalar hoto ko sauti a cikin fim din.
 4. An yi kokari a aikin fim din sosai.
 5. Jaruman cikin fim din sun dace da labarin.
 6. Gaskiyar da Ali yake da ita a cikin fim din shi yasa bai tozarta ba ba a lokacin da gaskiya ta bayyana a karshe.

KURAKURAI

 1. Duk da cewa dai fim ne, ya kamata a zo wa mai kallo da abinda hankalinsa zai iya yarda da shi. Ba zai yiwu mutum ya yi rayuwa da mata uku a unguwa daya amma ace ba wanda ya sani ba.
 2. Lokacin da Ali ya kirawo Idi yana fada masa cewa mamansa ta zo har Idi yake ce masa ya kaita gidan matarsa Sameera, an ji Idi yana cewa ka kaita gidan Sameera shi kuma Baba sai ka kawo shi nan gidana. Amma kuma daga baya sai aka kara nuna wata fitowar Ali yana bawa Idi labarin cewa Babansa ya zo ya ya ya kamata ya yi?, to idan har a farkon daman ba zuwa ya yi ba, me yasa ake maganar shi a wannan fitowar?
 3. Lokacin da Idi za su tafi gidansu Ummulkhairi shi da Baban Ali an jiyo Baban Ali yana cewa su biya su dauki maman Ali su tafi da ita, amma kuma zuwansu kofar gidan bai nuna tafiyar tasu tare bace, saboda lokacin da Idi ya ganta alamar da ya nuna, ba ta nuna cewa ya san da zuwan nata.
 4. Ya kamata tunda shi mahaifin Ali ya zo ne musamman saboda nemawa Ali aure ya kamata ace an gan shi yaje neman auren gidansu Ummamlkhairi amma ba a nuna hakan ba.
 5. Sunan shiri bashi da ma’ana ta kai tsaye zuwa labarin.

KARKAREWA

Wannan fim ya zo da labarI mai ban mamaki da kuma ban dariya a wani bangaren. Sannan fim din ya yi ma’ana kuma ya fadakar sosai. An samu kwarewa ta aiki a cikin fim din domin kuwa ba a samu kurakurai da yawa ba.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: