Connect with us

ADABI

Zuwan Malam Bahaushe Afrika Ta Yamma, Rayuwarsa Da Sana’o’insa (4)

Published

on

Daga Sarki Ibrahim Maje sai Sarki Abdul Karim (1563-1565) ko da ya ke shi bai dade a bisa mulki ba, shekarar sa biyu da rabi. Daga nan Sarkin Katsina Yusufu, wanda shi ma bai dade ba, ‘yan kwanaki ya yi a bisa gadon mulki. Shima an bayyana cewa sallamar sa aka yi amma ba a bada cikakken dalilin ba. Amma wasu sun ce ya gay a gaza rikon kasar Katsina shine ya gudu. Yin haka kuma bai hana dakarun yakin Katsina da su ci gaba da fuskantar Kano ba, a lokacin sarki wanda ya gaji Yusufu watau Ibrahim (1565-1575) A daidai wannan wakati Kano na fama da rikici wanda ya haifar da caje-canjen sarakuna har kashi hudu. Ba za mu ce ita kanta Katsina ta zuna lafiya don ta na kai wa Kano hari ba, a wannan wakati bayan Yusufu ya ajiye sarauta wasu sun amsa, watau daga Ibrahim (1565-1575) zuwa Muhammadu Wari (1575-1587) zuwa Suleiman (1587-1600) ko da ya ke a tsakanin su an samu canji mai kyau.
Bayan kamar kimanin shekara dari watau lokacin mulkin sarkin Katsina Uban Yara (1641-1671) A lokacin ne fa Katsina ta yi tsaye ta daure a kan yake-yaken da Kano ke kawo mata. Ita kanta Kano din, ta samu karuwar girman kasa da garuruwa da karkaru da karuwar tattalin arziki da ma karfin sarauta, a wannan lokaci watau zamanin mulkin Sarkin Kano Kutumbi, da shi da wanda ya gaje shi watau Muhammadu Nazaki (1618-1623) A daidai wannan wakati said a Kano ta taushe Katsina har na tsawon wata 10. Sarki Kutumbi shi ya mamaye Katsinar har sau biyu. Dalili, shi ne da Katsina su ka nemi sulhu tsakanin su da Sarki Nazaki. Bayan ma kashe Kutumbi sai aka kama babban dan sa Al-Hajj, sannan manyan malamai su ka zauna su ka bada shawara aka tsagaita wuta. Wannan ya jawo dangantaka tsakanin Katsina da Zamfara ta yi tsami inda har sarakunan kasar Zamfara gami da Sarkin Zamfara Zaudai dan Daka su ka fara rikici da ka ce-na ce da Katsina
Mu na iya cewa babban abinda ya haifar da Katsina shi kuma ya bata damar yin sarakuna, tun daga Durbi-Takusheyi. Tun farkon wanzuwa ko samuwarta, Katsina ta kasance, ta kuma bunkasa ne ta hanyar tattalin arziki ta dalilin dangantaka da baki fatake da kuma sauran garuruwa ko kasashen Hausa. Amma dangatakar Katsina ta fi karfi da kasashen Hausa da ke makwabtaka da ita, kamar su tsakiyar kasar Nijar, kudu maso-arewar kasar Nijar, Zazzau, Kano, Daura, Zamfara, Tegama, Sakkwato, Abzin da kuma Damargu. Akwai kuma wurare da su ka dan yi ma Katsinar nisa amma dai an yi hulda ta fatauci kamar su Kebbi, Nupe, Barno, Songhai, da kwarin kasar Bolta, garuruwan da su ka yi iyaka da Sahara kamar su Yamai, Damagaran, Maradi, Magarya, da kuma kasashen da ke bakin ruwa na arewacin Afirka, irin su Sudan. Sai dai an ce dangantakar Katsina da arewacin ta ba ta da kauri.
A wannan lokaci, fatauci da safara da fatake ko ‘yan kasuwa da su ke tasowa daga Barno zuwa garuruwan da ke yamma da ita, tarihi ya nuna ta Daura su ke biyowa. Wata kuma babbar hanyar da ta hade Barno da Gobir ko daga gabas zuwa yamma har Zamfara ko Sakkwato ita ce da ta bi ta iyakar Katsina da kasar Nijar ta kuma hade da hanyar da ta ke tafiya zuwa Agadas ko Fezzan ko Tuat. A wadannan hanyoyin ne Katsina ke fitar da gero da dawa da kayan saki da goro da bayi. Amma ita Katsina ta na shigo da gishiri da dawakai daga Barno, gishiri na ainihi daga kasar Abzinawa, tumaki da awaki daga Adar da Damargu, sai kuma kayan saki masu kyau da karko da kuma sauran abaiban more rayuwa daga Fezzan da Afirka ta arewa. Wannan kasuwanci da abin da Katsina ke fitarwa zuwa kudanci da arewaci da gabashin ta shi ya dada jawo hankalin fatake baki da ke izowa suna yin sansani a birnin. Don haka tun daga Dakar har bakin ruwa kusa da Jidda a Sudan ba inda sunan Katsina bai kai ba. Dalilin haka aka kara samun sabbin unguwanni a cikin birni kamar su Sararin Tsako, Tudun Malle, Tawatinke, sannan kuma aka kafa wasu kauyuka a gefen Katsina irin su Dutsi, Agalawa, Keffin Bujawa, da sauran su.
Saboda kuma saurin yaduwar harshen Hausa a kudanci da arewacin Katsina cikin hamzari ta dalilin cinikaiya ta sanya aka shafe shekaru ana hulda tsakanin Katsina da garuruwan da ke cikin kasar Nijar. Wannan ya kunshi al’umma kamar su Tazarawa da Taoreg da Abzinawa. To bare birnin Lalle da ke kusa da kan iyakar Katsina da kasar Nijar, da kuma gulbin Kaba mai makwabtaka da birnin. Sai kuma birnin Maya da ke kusa da gulbin Maradi. Dukansu wurare ne da fatake ke kwamba suna yin ciniki. Wannan kwamba da ciniki sun yaukaka a farkon karni na 18.
Harshen Hausa wani irin harshe ne mai ban al’ajabi, ga shi dai harshe ne mai dadi kuma mai saukin koyo. Muddin aka sa azamar koyonsa, cikin lokaci kankane za a iya shi, kuma har a yi magana da kowane irin Bahaushe. Wani abin al’ajabi a wannan harshe shi ne yadda ya ke da saurin hadiye sauran harsuna. Kowane irin harshe ake yin magana da shi muddin aka kusanci harshen Hausa to fa a kwana a tashi watarana za a wayi gari harshen da aka gada za ya bace a cikin Hausa, sai dai ita Hausar za a ji a fage. Su ma Hausawa mutane ne masu karimci, masu hakuri, masu jaruntaka a kowane fanni, masu kwazo, masu sakin fuska kuma uwa uba masu karrama baki. Wannan dalilin shi ya sa duk wani bakon da ya zo kasar Hausa, to da wuya a ji ya ce zai tashi ya bar ta. Wannan shi ya sanya baki daga Barno da sauran kasashen gabas su ka yi ta kwararowa Katsina tun a wannan wakati.
Amma hujjojin da ake da su na cewa Katsina ta yi kawance ta hanyar kasuwanci da kasashen da su ke kudu da ita masu rauni ne. A cikin littafin sa mai suna Tarikh al-Sudan, Abdul Rahman as-Sadi ya bada bayanin wasu yakoki da aka yi tsakanin Songhai da Katsina, guda a cikin shekara ta 1514 wanda ita Songhai din ta kai wa Katsina da Kano hari, guda kuma a cikin 1554 na yunkurin da ita dai Songhai ta yi don ta sake kama Katsina.
Saidai hujjojin tabbacin zancen yakin Katsina da Kebbi masu kwari ne, don lallai an tabbatas Sarki Kanta na Kebbi ya keta ta Kuyanbana ya kutso kai zuwa kudancin Katsina. Lallai an ce Kebbi ta afka ma Dan Ashita da ke kan iyakar Katsina da ke bangaren gabas.
Amma kuma kada a manta cewa Sarkin Kano Kutumbi (1623-1648) ya samu nasarar kama ko mamaye Katsina na wakati mai tsawo, a yayani da ya yi sansani a wani wuri da ake kira Dugazawa. Su ka sake dawowa Katsina bayan wani lokaci, a yayin das u ka bi ta kofar yamma. Amma wannan karon sai aka kashe shi a daidai wani kauye da ake kira Rurumawa a daidai bisa iyakar Katsina da Kano din. Wannan ya afku cikin 1648.
Amma saboda babu wata cikakkar hujjar dangantaka tsakanin Katsina da sarakunan Barno na da wahalar ganowa. Ko dai babu dangantaka tsakanin su ta fuskar tattali da kasuwanci to an san Daular Barno ta fito sarari a kasashen tsakiyar Daular Sudan. Fatake da sauran baki ‘yan hijira daga Barno zuwa birnin Katsina ya somo ne daga wancan lokaci. Daga cikin ire-iren wannan tawaga akwai wata da wani Tamma ya jagoranta unguwar Tama da ke daga gabas a cikin birni. Su ne kuma su ka yi hijira zuwa wani gari da ake kira Godiya a yammacin Kano zamanin Sarkin Kano Abubakar Kado (1565-1573) Shima Abu Abdallah Muhammad watau Dan Masani wanda aka haifa cikin birnin Katsina cikin 1595 an ce zuriyar su daga Barno ta ke.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!