Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamna Matawalle Ya Aza Tubalin Aikin Filin Jirgin Sama A Jihar Zamfara

Published

on

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce, za a fara aikin ginin filin saukan Jiragen sama na Gusau a cikin kwanaki 100 na hawansa kujerar gwamnan Jihar. Gwamnan ya yi wannan alkawarin ne a saíilin da ya kai ziyarar gani da ido a wajen da a ke aniyar gina filin saukan Jiragen saman a ranar Asabar.

Wata sanarwa wacce mataimaki na musamman ga gwamnan a kan harkokin manema labarai, Mallam Yusuf Idris,  ya sanyawa hannu, tana cewa, gina filin saukan Jiragen saman a Jihar yana da matukar mahimmanci ga ci gaban Jihar da kuma samar da ayyukan yi . Sanarwar ta ce, gwamnatin ta himmantu ne wajen zuba dimbin jari a kan hanyoyin bunkasa tattalin arzikin Jihar, da kuma duk wata hanya da za ta bunkasa tattalin arzikin.

ìGwamnan ya yi alkawarin mayar da Jihar hadaddiya kuma mai bunkasar tattalin arziki, ya kuma yi kira ga masu kudi na Jihar da su zuba jaruka masu yawa a Jihar ta Zamfara, inda ya yi masu alkawarin tagomashi masu yawa in ji sanarwar. Sanarwar kuma ta ce, Matawallen ya kuma ziyarci Otal din Gusau, inda ya taras da cewa, yawancin kayayyakin da ke wajen duk sun lalace.

Gwamnan ya bayyana matukar damuwarsa a kan yanda kusan komai a wajen a lalace yake, inda sassa da yawa ma su ke gab da rugujewa. Ya kuma bayar da umurnin a gaggauta gina Otal din ta yanda zai yi daidai da kowane irin sa na Duniya.

Ginin filin saukan Jiragen saman dai an faro maganarsa ne tun sama da shekaru 10 da suka wuce, wanda tsohon Gwamnan Jihar, Mamuda Shinkafi ya fara. An ta kiyasta aikin a cikin kasafin kudin Jihar a zamanin shekaru Takwas na wanda Matawallen ya gada, tsohon gwamna Yari, amma har zuwa lokacin da ya sauka ba wani aikin da a ka fara a wajen.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!