Connect with us

MAKALAR YAU

Irin Kutsen Da A Ke Yi Wa Al’ada

Published

on

KZsan dukkan dabi’un mutane, daga zuwa kasuwa, halartar daurin aure, soyayya, koyonsu a ke yi. A hankali yanzu a yankinmu na arewacin Nijeriya, mutane sun fara mayar da dabi’ar rungumar mata su na hotuna da su tun kafin a daura aure, da sunan wai hotunan kafin buki, alhali a baya ba a san da wannan wuce gona da iri ba.

Yanayin aure a lokutan baya a kasar Hausa ya kan kasance ne tsakanin iyaye, sai a hada a yi aure. Wannan ya kna nufin ba zai yiwu ka hada yanayin aure tsakanin al’umman Amurka da al’umman Nijeriya ba, al’adun da a ke yi yayin aure a Amurka ko kusa ba su yi kama da al’adun mutanen Nijeriya ba. Alal misali, a wurin mutanen garin Kolkata na kasar Indiya, aure bai yiwuwa sai an samu dankon soyayya mai karfi a tsakanin ma’aurata. Wanda a shekarun baya a kasar hausa, a kan daurawa mutum aure, alhali bai taba ganin amaryar ba ma.

Ita al’ada ta na kara habbaka ne, daga mataki zuwa mataki. A kullum a na samun karin abubuwa ga al’adun da a ke iya gani, amma ba dole ne su shafi al’adun da ba a iya ganinsu ba. Al’adun da a ke iya ganinsu sun hada da yanayin tufafin da mutane ke sawa, yanayin bukukuwan aurensu, da sauransu. Al’adun da ba a iya ganinsu sun hada da yare, da sauransu.

Shi kirkira a cikin al’ada na faruwa ne yayin da a ka shigo da wani sabon abu, dalilin da ya sa a ke kiranshi kirkira saboda wasu abubuwan da ya ke zuwa da su wadanda a da ba a san da su ba. hanyoyi biyu kirkira ke samuwa; walau a gano abin, ko kuma wani ya samar da shi kuma ya ayyana.

Idan a ka ce wani ko wasu sun gano wani abu, ya na nufin kenan akwai dama wannan abin, kawai dai ba a kai ga gano shi ba ne. kamar misali, a shekarar 1610, lokacin da masani Galileo ya yi amfani da na’ura ya hango duniyar ‘Saturn’, da ma chan akwai duniyar, amma ba a san da samuwarta ba sai bayan da ya gano.

A daya bangaren kuma, a na samar da wani abin ne a lokacin da a ka kirkiri wani abu sabo daga wata fasaha ko wani abu wanda babu shi kwata kwata. A tsakankanin shekarun 1800s da 1900s ne a ka fara kirkiro sabbin fasahan kirkira ta hanyar wutan lantarki. Haka kuma za mu iya ganin yadda a ka samar da abubuwan da babu su irinsu motoci, jirage, fitillu, rediyo, wayar salula da sauransu.

A nan mu na iya cewa dayan wadanchan abubuwan biyu da a ka ambata na kirkira ya na iya kawo chanji ga al’adun jama’a. hakan na faruwa ne idan mutane su ka fara amfani da wani sabon abu wanda yam aye gurbin wani tsoho da a baya akwai shi. misali yanayin aure a kasar hausa, a baya ba a san da wasu tsirfa wadanda su ka hada da ‘Arabian Night’, ‘Dinner’ ko hotunan kafin aure ba.

Wadannan irin hotunan da a ke yi yanzu tsakanin ango da amaryarsa, a yi ta watsawa a kafafen yanar gizo. Abin takaicin sai ka ga diyar Bahaushe da diyar Bahaushe sun yi hoto a rungume da juna, ba kunya ba tsoron Allah, wasu ma macen rabi tsirara ta ke, a na ganin surarta a bayyane, kuma a haka mijin zai rika turawa mutane, ko kishi babu.

A shekaru 20 baya, idan ka ce irin wannan rashin da’a za ta samu gurbi a kasar hausa, wani na iya yi maka dariya, sannan ya yi maka gardamar cewa ba zai taba yiwuwa ba. saboda a wadanchan shekarun akwai kunya da kuma kishin mata a tsakanin al’umma.

Kafin zuwan wayar salula a wannan yanki namu, hanya mafi sauki na isar da sako shi ne a rubuta wasika, sai a tura da ita. Sannan a wannan lokacin, babu yawaitar jita – jita a tsakanin al’umma, sai ga shi a hankali an fara dasa wayoyin tarho a gidajen daidaiku, su ka fara yawaita a tsakankanin gidajen al’umma. Wanda daga karshe kuma wayar hannu ta zo.

Da farko shigowar wayoyin hannu, da yawan iyaye sun yi iyaka kokarinsu wurin ganin ‘ya ‘yansu mata ba su yi ta’ammuli da wayar salula ba, amma a haka a ka ci gaba da tafiya, har wayar salula ta zama wani bangare daga cikin al’adunmu.

A maimakon a baya, hatta budurwa wacce ta isa aure, ba a barin ta yin amfani da wayar salula, sai ya kasance yanzu, kankanuwar ‘yar kwaila, ‘yar shekaru 11, 12, 13, 14, 15 ma waya ne a hannunsu. Wannan ba karamin ta’asa ya yi ga al’adun Malam Bahaushe ba.

Wayoyin ma kuma sai ya kasance ba kawai wadanda a ke yin kira a amsa kisa da su ba ne, a’a, wayoyi ne na zamani wadanda a ke iya leka shafukan yanar gizo. A maimakon ‘ya ‘yan al’ada da a ka sansu da tarbiyya da natsuwa kammalalliya, sai ya zama wayoyin sun gusar da wannan al’adu managarta, sun gabato da wasu gurbatattu.

Al’adunmu managarta wadanda su ka koyar da mu kiyaye mutunci da tsiraicin ‘ya ‘yanmu mata, wayar salula ta zo ta yi fatali da su. Wayar salula ta zo ta koyawa maza yin hira da mata a shafukan yanar gizo. Babu bukatar sai namiji ya ziyarci gidan da yarinya ta ke, ta wayar za ta dauki hoton surar jikinta a take a inda ta ke, ta tura masa.

Wasu ta hanyar wannan wayoyin su ke hirarrakin batsa wanda daga nan ne a ke motsa sha’awar da idan ba dai Allah ya kiyaye ba, sai an tafka tsiya da aika – aika. Wannan kirkira dai ta cutar da al’adunmu, kuma ta hana ma iyaye daukan kwararan matakan da su ka dace wurin killace ‘ya ‘yansu. Duk da haka ya kamata iyaye su ci gaba da sa ido a kan ‘ya ‘yansu musamman mata, tun kafin wanki hula ya kai su dare. Mu hadu mako mai zuwa.

 




Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!