Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Bindiga Su Harbe Wani Mutum A Abiya

Published

on

Wasu ‘yan bindiga wadanda a ke kyatata zaton masu garkuwa da mutana ne, sun harbe wani mutum har lahira, a tashar ‘yan babura da ke garin Aba ciki Jihar Abiya.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, lamarin ya afku ne da misalin karfe bakwai na safe a kan titin da ke tsakanin Park da kuma George cikin garin Aba. Kakakin rundunar ‘yan sadar jihar, SP Geoffrey Ogbonna, shi ya tabbatar da faruwar lamarin lokacin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, ya bayyana cewa, bayanai da su ka zo gare shi, sun nuna cewa, an garzaya da mutumin asibiti bayan da ‘yan bindigar su ka harbe shi, sabanin yadda a ke ta yada jita-jita na cewa ya mutu nan take, an dai ijiye gawar sa a dakin ijiye gawarwaki.”

Wadanda lamarin ya faru a gaban idanunsu sun yi zargin cewa, ‘yan bindigar sun harbe mamacin ne lokacin da ya ki bin umurnin su, inda ya dauki wacce su ke hari a kan babur dinsa. Sun kara da cewa, ‘yan bindigar sun biyo matar ne, saboda su na zargin cewa, ta na tare da kudi masu yawa. Bayan da ‘yan bindigar su ka harbe mamacin, sai matar da gudu.

Shaidun sun ce, “lamarin ya aufku ne ba zato ba tsammani. Mu na cikin tafiya za mu je sayan sabu, sai mu ka ga wani mutum ya wuce a kan babur. “Lokacin da mu ka juya, sai mu ka ga mai babur din ya na kokarin juyawa a kan hanya, yayin da mu ka ga wata mata ta sauko daga babur ta ruga a guje.

“Ba zato ba tsammani sai mu ka fara jin harbin bindiga, wanda ya sa mutane gudu. “Lokacin da mu ka isa wurin, sai na ga mai babur ya kwantar da kai. Sun harbe shi a kai”

Ogbonna ya ce, rundunarsa ta na gudanar da bincike a kan lamari, ya kuma sha alwashin cewa, rundunarsa za ta cafke wannan ‘yan bindiga.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: