Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Kungiyar Asiri Sun Harbe Dalibin Jami’ar Jihar Akwa Ibom Har Lahira

Published

on

A ranar Asabar ne wasu ‘yan bindiga wadanda ake kyautata zaton ‘yan kungiyar asiri ne, sun harbe wani dalibin jami’ar Jihar Akwa Ibom, mai suna Mkpat-Emem Jimmy har lahira, wanda ya ke karanta fannin siyasa a harabar jami’ar. Jimmy ya mutu ne da misalin karfe 12.30, an dai harbe shi ne lokacin da ya ki yarda a kwace masa wayarsa da kuma wasu kayayyakinsa. An bayyana cewa, maharan sun farmake shi ne da misalin karfe takwas zuwa karfe tara na dare, a kan hanyar Wilson Idiong kusa da titun Ikot Okoro da ke cikin karamar hukumar Oruk Anam ta Jihar Akwa Ibom.

Babban jami’in watsa labarai na Jami’ar, Mista Akaninyene Ibanga, shi ya bayyana wa manema labarai aukuwar lamarin a ranar Litinin. Ya bayyana cewa, an garzaya da dalibin zuwa asibiti domin yin jinya, inda a nan ne ya mutu bayan kwana biyu da kwantar da shi. A cikin bayanin jami’in, “An harbe mamacin Emem ne a tsakanin karfe 8.30 zuwa karfe tara a kan hanyar Wilson Idiong kusa titin Ikot Okoro a yankin Obioakpa cikin karamar hukumar Oruk Anam, lokacin da ya ki yarda wasu ‘yan bindiga su kwace masa wayarsa, nan take aka garzaya da shi zuwa asibiti domin yin jinya. “Hukumomin jami’ar sun biya dukkan kudaden asibiti domin a ceci rayuwarsa, amma a ranar Asabar da misalin karfe 12.30 na rana, marigayi Emem ya mutu.”

A halin yanzu dai, hukumomin jami’ar sun nuna bacin raisu a wannan lamari, tare da yi wa wadanda suke da hannu cikin wannan lamari garkadi a kan ko dai su mika kansu ko kuma jami’an tsaro su damke su. “Shugaban jami’ar Jihar Akwa Ibom tare da dukkan hukumomin jami’ar da ma’aika da kuma dalibai sun nuna alhininsu bisa kashe marigayi Emem Jimmy, dalibi da ke karatu a sashin fannin siyasa. “Shugaban jami’ar ya mika sakon ta’aziyar sa ga iyalan mamacin. Ya kuma bukaci dukkan dalibai da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da gudanar da karatunsu, ya ku tabbar da cewa jami’an tsaro za su cafke duk wani mai hannu a wannan kisan tare da hukunta su,” in ji shi.

Ya kuma tabbatar da tsaron duk wani wanda ya ke cikin wannan jami’ar, domin ya yi magana da kwamishinan ‘yan sandar Jihar da kuma sauran jami’an tsaro a kan za a girke jami’an tsaro a harabar jami’an domin tsaron rayukan al’umma.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!