Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Sanda Sun Damke Masu Garkuwa Da Mutane Guda Bakwai A Edo

Published

on

A ciki wannan mako ne rundunar ‘yan sanda ta damke mutum bakwai wadanda a ke zargin masu garkuwa da mutane ne a yakunan Ekiadolor da kuma Egor da ke cikin garin Benin babar birnin jihar. Kakakin rundunar ‘yan sandar, DSP Chidi Nwabuzor, shi ya bayyana hakan a garin Benin. A cewarsa, sashin rundunar  ‘yan sandar masu yaki da garkuwa da mutane ne su ka samu nasarar damke wadanda a ke zargi, bayan samun bayanan sirri.

Ya kara da cewa, wadanda a ke zargin sun yi garkuwa da wata yarinya tare da sace mata mota kirar Audi 80, wacce mahaifinta ya saya mata a shekara biyar da su ka gabata kafin a samu nasarar damke su. Nwabuzor ya ce, an samu nasarar ceto wacce su ka yi garkuwa da ita, sanna har an mika ta da iyayenta.

Kakakin ya ce, “wadanda a ke zargin sun amince da laifin su na cewa, lalle su masu garkuwa da mutane.  “A ciki kayayyakin da a ka kwato daga hannunsu sun hada da, karamar bindiga kirar gida guda biyu, babar binbiga guda daya, harsashi guda 10, mota kirar Audi 80 guda daya da kuma babura.” Ya ce, za a gurfanar da wadanda a ke zargi a gaban kuliya da zarar an kammala bincike.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!