Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Sanda Sun Damke Mutum Tara Bisa Laifin Kisa A Kuros Riba

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Kuros Riba, ta samu nasarar damke mutum tara wadanda a ke zargi da kisan kai tare da mutum biyu ‘yan kungiyar asiri a Jihar. Majiyarmu ta labarta mana cewa, a kauyen Edor cikin karamar hukumar Ikom, a ka damke tawagar mutum uku wadanda su ka hada da Akong Francis Akong dan shekara 55, OsimAjom dan shekara 43 da kuma Sunday Ebase mai shekara 24, inda su ka dunga bugun wani matasi mai suna Bright Effiong dan shekara 29, har sai da ya mutu, bisa suna zargin sa da yunkurin yi wa Matam Bibian Christian ‘yar shekara 27 fyade.

Manyan wadanda a ke zargi da harbe Ayuk Ogar har lahira dai su ne Abor Mgbe Agbor, Osawa-Ayi Amba dan shekara 22 da kuma Ojong Owan Ntokwa mai shekaru 35.

Wakilinmu ya bayyna mana cewa, an samu nasarar cafke sauran mutum biyu wadanda a ke zargin da kisan gilla. Sun hada da Eworo Collins dan shekara 22, dan asalin kauyen Nanga, wanda ya damu wata budarwa mai suna Crace Gbaka, wacce ta ke zaune a kan titun mai lamba daya na Ntata, a yankin Ekajuk da ke karamar hukumar Ogoja, a kan su yi soyayya, inda ya gayyaci Grace da kawarta zuwa gidansa domin bikin jana’iza. Lokacin da su ka isa gidan, sai wadanda a ke zargin suka kashe su, inda su ka jefar da gawar wadannan ‘yan mata a kan titin Bansara da ke Ogoja, yayin da har yanzu a ke neman Eworo Collins.

Hakazalika, rundunar ‘yan sandar ta cafke mutum biyu wadanda ake zargi da ayyukan asiri. Tawagar ‘yan sanda da ke gudanar da sintiri sun yi arangama da mutum shida masu tukin Keke Napap, wadanda a ke zargin suna da hannu a cikin arangamar kungiyar asiri wanda ya auku a kan titin Bedwell a garin Kalaba. Hudu gada cikin su sun gudu lokacin da su ka ga ‘yan sanda, amma an samu nasarar damke mutum biyu, Bictor Tom da kuma Joe Jacob.

Kwamishinan ‘yan sandar Jihar, Austin Agbonlahor, ya bayyana cewa, “Ana gudanar da bincike tare da kokarin damke sauran ‘yan kungiyar asirin wadanda ke da hannu cikin rikicin. Dukkan wadanda a ke zargi za a gurfanar da su gaban kotu.”

Kwamishinan ‘yan sandar ya ce, mutum biyun wadanda a ke zargin suna da hannu a cikin lamarin fyade, “Ana neman Eworo Collins wanda a ke zargi ruwa a jallo, yayin da an gano takalman Moses Egbodor, daya daga cikin wanda a ke zargi.

Dukkan wadanda a ke zargin an samu nasarar cafke su, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike. A bisa damke mutum uku wadanda da a ke zargi da kisan gilla, kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana cewa, “Mutum ukun wanda a ke zargin an gurfanar da su a gaban kotu, bisa laifin hadin kai da kuma na kisan gilla, yayin da a ke farautar sauran wadanda a ka hada kai da su. Mutum uku wadanda a ka gurfanar da su, an garkame su a gidan yarin Afokang da ke garin Kalaba,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!