Connect with us

LABARAI

’Yan Ta’adda Sun Kashe Shugaban ’Yan Sa-Kai Da Mutum Biyu A Dandume

Published

on

’Yan ta’adda sun kashe shugaban ’yan sa-kai na karamar hukumar mulki ta Dandume da mutum biyu.

Wannan lamarin ya aukune da misalin karfe biyun dare ranar Talatar da ta gabata, inda daya daga cikin yan ta’addar ya kira shugaban kungiyar yansa kan ta waya mai suna Saminu Buje dake kauyen Dugun Sambo kilo mita uku daga garin Dandume dake jihar Katsina.

Wakillinmu ya zanta da wasu daga cikin iyalan mamacin inda suka bayyana ma wakilinmu cewar dama shi marigayin watau shugaban yan sakan mai suna Saminu Buje ya addabi ‘yan ta’addar yankin, domin shi marigayin tsaye yake ba dare ba rana wajen kokarinsu na magance yan ta’addar yankin.

Saboda haka ne miyagun su ka yi amfani da kiran lambarshi ta waya inda su ka ce mashi ya shigo garin Dandume barayi sun shigo garin suna bukatar taimakon shi dana kungiyarshi, batare da bata lokaciba ya hawo Baburdinshi tare da mutum biyu ‘yan kungiyar ‘yan sa kan, inda ‘yan ta’addar suka yimasu kwanton bauna suka kashe su, kafin mutuwar su sai da suka fafata da ‘yan ta’addar kafin su sami galaba a kansu, ‘yan uwan mamatan sun cigaba da cewar shi marigayi Saminu Buje mutum ne haziki kuma mara tsoro, yana da shirinshi amma kasan karar kwana idan tazo bata da magani ko shiri haka Allah yaso, amma babu shakka al umma sunyi asarar haziki kuma shugaba mai kokarin kare jama’a da dukiyoyinsu.

Sudai yan ta’adda sun halaka shugaban da mutum biyu ta hanyar harbinsu da bindiga amma bindigar bata kamasuba inda daga bisani ‘yan ta’addar sukayi amfani da duk kan wani makami amma bai kama ‘yan sakan ba, da karshe sukayi amfani da manyan Duwatsu wajen kwankwatse kawunansu har suka mutu a nan take, inji wani dan sa-kai da ya ke bayyana wa wakilinmu da ya ziyarci ofisin yan sanda na garin Dandume, domin tabbatar da aukuwar lamarin.

Wakilinmu ya tambayi wani dan sanda mai mukamin kofur cewar yana son ganin DPO, amma dan sandan yace DPO bayanan, wakilinmu ya bayyanama dan sandan cewar wakilin jarida ayau ne yazo domin tabbatar da aukuwar kashe shugaban ‘yansa kai da mutum biyu da ‘yan ta’adda su ka yi, ya ce shi ba zai ce komai ba tunda sun ruga sun mutu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!