Connect with us

RIGAR 'YANCI

Za A Shiga Uku A Kano Da Ganduje Bai Zarce Ba, In Ji Kwanmatin Karbar Mulki

Published

on

Wani dan jam’iyar APC dake jihar Kano kuma daya daga cikin ’yan kwamatin karbar mulki, Suraja Yahaya Janbul, ya bayyana cewa, za a shiga uku a jihar idan da gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar ganduje, bai samu nasarar yin tazarce ba, sannan ya kara da cewa, za a samu canji a salon tafiyar da gwamnatin a zagaye na biyu nan.

Ya yi bayanin hakan ne a hira da manema labarai bayan kammala rantsar da gwamna Dr. Abdillahi Umar ganduje a karo na biyu. Ya yi karin haske da cewa, cikin wannan tafiyar da za a shiga gadan-gadan tsarin da za a zo da shi, zai fi yiwa mutanen Kano alkhairi.

“Da ba don Allah ya sa shi ne ya dawo ba, to da sai mu ce an shi goma ba uku ba, domin Allah ya ga zuciyar mutanen Kano, ba a sake jefa su cikin kangin bauta ba,” in ji shi, ya na mai cewa, “Gwamna mutum ne mai bada dama ga ka yiwa kanka tunani, ba wani ya yi ma ka ba, domin da gwamnatin za ta yi wannan karon tsari ne na musamman ga talakawa da raunana, domin gwamnatinsu ce su ne su ka hadu su ka yi ta.

“Ka ga dole gwamna ya sake daukar matakin na gaba, domin ciyar da Kano gaba, domin matsalar mutanen Kano. Ma’ana abinda su ke so, shi wannan gwamnantin ke yi. To, kuma yanzu za a kara.

“Kirana shi ne mu mutanen jihar Kano mu ba shi dama, mu ba shi lokaci kuma mu yi hakuri da abubuwan da za su zo, domin duk locacin da a ka cewa dan adam gyara, bai cika yiwa mutum dadi ba, domin ya kan zo da kawar da ciwo ne, ya kan zo da kau da matsaloli.

“Kuma mu na tabbartar da cewa mu za mu yi addu’a, za mu bada goyon baya, za mu yi duk abin yi, don samun nasarar gwamnatin ko ta fuskacin kawo saukin karatu abun alfahari ne.”

saidai kuma ya kara da cewa, “ba a nan gizo ke sakar ba, tambaya su waye za su taya mai girma gwamna wannan aiki? Wannan shi ne abin jinmu, abinda mu ke gudu shi ne a sake yin kitso da kwarkwata, domin an yi a baya ba ta haife ma na da mai ido ba. Kuma duk mutumin da ya samu kansa a wannan sabuwar gwamnatin, to ya ji tsoran Allah ya rike amana, domin sabuwar gwamnati za a yi.

“Kira na shine duk wanda yau ya zama wani a wannan kunshi gwamnatin, to ya dubi Allah ya  rike abinda a ka ba shi, domin cigaban jihar nan. Dalilimu a wajenmu mu na so jam’iyyar APC ta sake kafa gwamnati bayan gwamna ya kammala; mu ma mu yi kamar shekara 16.

“Daga wannan ne za a iya auna mu da abokan hamayarmu, su shekara 16 su ka yi su na mulkin kasar nan, amma sun zo su na kuka. Su bari mu ma mu yi 16, sannan sai a auna a gani.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: