Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Arangamar ‘Yan Qungiyar Asiri Ya Ci Rayuwar Mutum Daya A Legas

Published

on

A ranar Litinin ne a ka samu tashin hankali da kuma tsoratar da mutanen Ajah cikin qaramar hukumar Eti-Osa ta gabas cda ke Jihar Legas, saboda kuwa mambobin qungiyoyin asiri na Aiye da kuma Eiye confraternities, su ka gwabza da juna, inda su ka yi ta musayar wuta ta bindigogi da misalin qarfe 8.12 na yamma.

Mazauna unguwar sun bayyana cewar, su ’yan qungiyar asirin sun gwabzawa ne saboda shugabanci, wannan kuma ya biyo bayan mutuwar Olumegbon. Shi dai Olumegbon ya gina ita fadar tashi ne a wannan unguwar, ya kuma tare a Legas, inda ya kwashe shekaru masu yawa.

Marigayin shi ne shugaban Idejo, wato farar hula (white-cap), Sarakunan gargajiya wadanda su ke sa farar hula, su ne kuma ke da alhakin nada sarautar Oba ta Legas .

Wani wanda lamarin ya auku a gaban idanunsa mai suna Ambrose, ya bayyana cewar, ya na dawowa ne daga aiki ranar Litinin lokacin da ya samu wasu ‘yan qungiyoyin asiri su na gwabzawa ranar Litinin, kuma dama ba su zaman lafiya da juna. Ya bayyana cewar, ba zai iya gane ko daga ina ne a ka yin harbin ba, saboda da dai shi ya ga harsashi na ya na yawo ne daga wurare daban- daban.

Ambrose ya qara bayyana cewar, a sanadiyar hakan ne, ita unguwar ta shi ga cikin wani hali, saboda mutane sun rasa wani irin hali su ke ciki ne, tun da har an kai ga wani yanayin da mutanen sun kasa zuwa nan da can, zuwa shaguna da kuma sauran gidajen mutane, inda mutane ke ta neman wurin da za su iya zuwa domin su tsira daga kauce wa shi ga cikin wani halin qaqani- ka-yi.

Ya bayyana cewar, su jami’an tsaro ba a gan su a wurin ba, har sai lokacin da a ka daina jin qarar harbe – harben. Ya cigaba da bayanin cewar, ita unguwar Ajah ta kasance wani wuri ne wanda ya ke da hadari, inda mutane su ke zaune, amma kuma koda wani lokaci hankalin su ya na tashe.

Ambrose  ya bayyana cewar, hanyoyin Oke Ira da ta Ado zuwa Total da kuma sauran wurare, ‘yan qungiyar asirin ne su ke riqe da su. Ya qara jaddada cewar, “Ina dawowa ne daga aiki, amma kuma lokacin da na je hanyar Ado kusa da Oke Ira, na ji qarar harbe – harbe, amma ban yi tsammanin harbin daga wuri daya ya ke zuwa ba, kafin in san abin da ya ke faruwa, na ga ashe harsashi ne ya ke ta yawo ko ina, dole ne na ruga kusa da wani kanti saboda in samu tsira.

“Babu kuma wani wanda zai iya cewar ga daga wurin da harbin ya ke fitowa, wannan shi ya sa mutane su ka rude, ga shi kuma babu wasu jami’an tsaro,” in ji shi.

Wata mazauniyar unguwar mai suna Bimbo Adedeji ta bayyana cewa, ta na cikin shagonta, ta na ma qoqarin komawa gida ne lokacin da ta ji qarar harbe- harben bindiga, wannan ne ya sa ta koma shagonta. Ta cigaba da bayanin cewar, ‘ya’yan qungiyoyin asiri guda biyu sun yin fada ne saboda su samu dama ta mallakar wuri, musamman ma bayan mutuwar Olumegbon wanda shi ne shugaban unguwar.

Adedeji ta qara da cewa,“Shi wannan al’amari na samun damar mallakar Ajah, wadanda su qungiyoyin asirin biyu su na nuna kamar ba su da hankali, bama wanda ya san ko su mambobin qungiyarsu na da yawa, wadanda har ma gwamnati za ta damu da su. “Koda ya ke dai na ga wasu mutane ana kai su ofishin ’yan sanda, ban san ko su na daga cikin wadanda a ka kai su ofishin ‘yan sanda, ko kuma su na daga cikin wadanda su ka tayar da hankalin mutane a Aja ranar Litinin,” in ji ta.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!