Connect with us

RIGAR 'YANCI

Barnar Gwamnatin Kano Ya Fi Kuskuren Masarautar Kano Illa – Dr. Dikko

Published

on

An bayyana cewa, girman barnar da gwamnatin jihar Kano ta yi na kirkirar sababbin masarautiu a jihar, ya fi irin kuskuren da masarautar Kano ta yi mummunar illa. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Mataimakin shugaban Majalisar Malamai na Jihar Filato, Dr. Hassan Abubakar Dikko a wani taro da a ka gudanar a Minna babban birnin jihar Neja.

A wajen taron kuma, gwamnatin Neja ta yaba wa malamai jagororin addini a kan irin rawar da su ka taka wajen fadakar da jama’a a lokacin da tsaro ya so ya gagari kundila a kasar kan irin gudunmawar da mabiya ya kamata su taka wajen yin addu’o’i ganin lamarin ya so fin karfin gwamnati. Addu’o’in da jama’a su ka rika gabatarwa ba dare ba rana dan ganin kasa ta zauna lafiya bisa hudubobin malamai ganin su ke da mabiya dubbai a tare da su shi ne dalilin samun nasarar da a ke samu a halin yanzu.

Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, wanda ya samu wakilcin babban darakta mai kula da harkokin addinai a jihar, Dakta Umar Faruk Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin rufe tafsirin Al-kur’ani na watan ramadan wanda kungiyar Izalatul Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah wadda As-sheikh Isma’ila Idris Zakariya Jos ya assasa bisa jagorancin Assheikh Sani Yahaya Jingir a reshen kungiyar ta jihar Neja wanda mataimakin shugaban malamai na jihar Filato, Dakta Hassan Abubakar Dikko ya gudanar a Minna.

Gwamnan ya nemi malamai da su kara kaimi wajen fadakar da al’umma da yin addu’o’in samun zaman lafiya a kasar nan da kira ga jama’a wajen sanya idanu ga kai-komon batagari a cikin al’umma, domin matsalar garkuwa da mutane don karbar kudin fansa, fadan makiyaya da manoma wani shirin makiya ne na ganin an lalata yankin Arewa, amma cikin hukuncin Allah da addu’o’in ake yi an fara samun karya lagon makiya.

Da ya ke nuna godiyarsa akan bakuncin malamin da ya gudanar da tafsirin na bana da irin karamcin da kungiyar ta baiwa masarautar minna, mai martaba sarkin minna, Dokta Umar Faruk Bahago da ya samu wakilcin Alhaji Aliyu Umar Gundumar Makera kuma sarkin Shanun minna, ya nuna godiyarsa ga babban malamin addinin da ya ziyarce shi a fada, ya kuma fadakar da al’umma yace wannan abin a yaba ne.

Sarkin ya jawo hankalin al’ummar musulmi wajen nuna soyayyarsu ga juna da yin anfani da kiraye kirayen malaman da sukai tayi lokacin da suke gudanar da tafsiran su akan mu’amalar jama’a dan ganin ba a baiwa batagari damar labewa a cikin su ba. Kasar nan muna cikin halin jarabta na rashin tsaro ya zama wajibi mu tashi tsaye dan taimaka wa jami’an tsaro domin aikin ba na su ba ne su kadai mu kan akwai rawar da zamu iya takawa.

Dokta Umar Faruk ya nemi al’ummar musulmi da su kara kaimi wajen yin addu’o’i a ‘yan wadannan kwanakin da suka rage domin ganin karshen wannan lamarin da ke hanawa al’umma da gwamnati bacci, ya kuma jawo hankalin al’umma akan su guji duk wani abinda zai kawo koma baya a lokacin bukukuwan sallah karama mai zuwa.

Alhaji Haruna Musa, shi ne shugaban kungiyar a jihar Neja, ya yabawa kokarin gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello kan yadda ta ke baiwa harkokin addinai muhimmanci, ta hanyar fitar da kudi da duk wani abinda ya kamata idan bukatar hakan ta samu dan ganin addinin musulunci ya cigaba.

Alhaji Haruna yace taimakekeniya na kyau a tsakanin al’umma, dan haka muna jawo hankalin jama’a akan muhimmancin taimako domin shi ne zai karya lagon barace barace da ke neman zama ado a cikin al’umma, taimakon nan ba wai sai kawai lokacin azumi ba, rashin yinsa ne ya jefa dubban jama’a a halin da suke ciki yau.

Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida, shi ne Cikasoron Minna, Gado Da Masun Bargu kuma Barde Kerarriyar Agaie, yace jawo hankalin al’umma wajen taimaka wa gwamnati da addu’o’i, yace mun yi gumurzu a lokacin zabe kuma fatar talakan Najeriya bai wuce ganin shugaba Muhammadu Buhari ya dawo karo kan karagar mulki. Yace an samu nasara akan wannan amma akwai jan aiki a gaba domin wannan zaben shi ma mai muhimmanci ne wato zaben ministoci, daraktoci da kwamishinoni da mataimaka ga zababbun shugabannin, duk kyau shugaban kasa ko gwamna idan bai samu mataimaka na gari haka za a sake wasu shekaru hudun ba a iya aiwatar da komai ba, dan haka tilas mu taimake su da addu’a duk wanda zai samu matsayin minista, kwamishina babban darakta ko mataimaki idan zuwan shi kan kujerar nan ba alheri ba ne komai kusancinsa kada Allah ya haska idanunsu akan shi, muna rokon Allah ya baiwa shugabannin nan natsuwa da hangen nesa wajen zabo mutanen da zasu taimaka a matsayin su na kai kasar nan a tudun mun tsira.

Ina mai jawo hankalin masu rike da mudafun iko akan su ji tsoron Allah, su tsaya a inda suka sani ba tare da shiga gonar da ba tasu ba, ma’aikaci ya tsaya matsayin sa, dan kwangila ya tsaya matsayin sa kuma hakan bai samuwa sai masu zabowar sun yi anfani da cancanta ba sanayya ko kusanci ba.

Da yake bayanin karshe a bana, Dakta Hassan Abubakar Dikko, shugaban majalisar malamai ta jihar Filato  wanda ya jagoranci tafsirin na bana, yace barnar da gwamnatin Kano ta yiwa al’ummar jihar, yafi kura-kuran da take zargin sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu da yi, domin yadda siyasar ta zowa gwamnatin jihar a murde shi ne ya kai ta ga daukar wannan mummunar matakin ga al’ummar jihar ba wai sarki Sanusi abin ya shafa ba, koyarwar addini da aka umurce mu ne aka rusa, kowa yasan zumunci da ke tsakanin al’ummar jihar tsawon shekaru da dama da tarihi ya tabbatar da shi, shi yau dare daya gwamnatin ta rusa wanda wannan kuskure ne babba, domin ya shafi kyakkyawan alakar da ke tsakanin al’ummar jihar ne na tsawon lokaci.

Malamin yace ya zama wajibi ‘yan siyasa su rika kai zukatansu nesa, ba kawai dan rashin fahimta ya taso su rika anfani da damar su wajen rusa abubuwan alheri ba, ko amurka da ke tutiya da karfi a duniya gundumomi hamsin da shida ya samar da ita kuma suna nan daram, ba yadda za kai anfani da matsayin ka wajen rusa dangantakar mutane sannan kayi tunanin samun nasara, dan haka ya kamata mu komawa karantarwar addini a daina daukar shawarwarin marasa kishin kasa da jama’a wajen ganin an fasa kowa ya rasa wannan kuskure ne babba.

Dokta Dikko ya jawo hankalin shugaban kasa, Muhammadu Buhari da cewar kamar yadda ya fadi cewar manyan kasar nan ba sa son sa, to da kar ya dogara da kowa sai Allah, idan yazo nada mataimaka daga kan ministoci, mashawarta da wadanda zasu jagoranci ma’aikatun gwamnati da ya tabbatar ya nemo nagartattun mutane wadanda kasar ne a zuciyarsu ba abinda zasu samu ba.

Dakta yace kasar a na cikin wani yanayi na ban tsoro musamman ganin yadda tsaro yake kokarin fin karfin gwamnati duk da kudaden da ake warewa dan ragargazanar batagari, yace idan an dubi wani sashe za a ce an samu nasara amma wani bangaren kan har yanzu an kasa gano bakin zaren. Idan ka dubi lokacin da gwamnatin nan ta karbi mulki ka kwatatan jahohin Barno, Yobe da Adamawa, Bauchi da wani sashen jihar Filato ko al’ummar zasu ce maka sam barka. Amma idan ka dawo yankin Zamfara, Katsina, Kaduna da wani sashen jihar Neja kan abubuwan da barayin shanu da masu garkuwa da mutane ke yi a halin yanzu abin yana bada tsoro, muddin aka ce ba tsaro to lallai ba yadda kasa za ta cigaba. Maganar wadanda ke wannan ta’addancin ba wasu mutane ba ne na daban ko kuma a ce baki ba, ‘yan kasa ne na hakika, ya zama wajibi gwamnati ta kara kaimi wajen samar da hanyoyin da za a kawo karshen wadannan abubuwan ta hanyar kirkiro gurabun ayyukan da zasu dauke hankalin matasa daga zaman kashe wando.

Shugaban kasa da gwamnoni su yi anfani da damar da suka samu duk wani da aka baiwa matsayi a baya kuma aka ga ya taka rawar gani ana iya dawo da shi ba tare da la’akari da kusancinsa ba, haka duk wanda aka jaraba a baya ya kasa ayi watsi da shi komai kusancinsa ko daurin gindin sa, kasar nan tana neman mutane ne masu kwazo da jajircewa wadanda cigaban kasar shi ne bukatar su ba abinda zasu samu ba.

Manyan bakin da suka halarci taron rufe tafsirin sun hada da Dakta Hassan Abubakar Dikko da ya gabatar da tafsirin tsawon kwanaki ashirin da biyar, sai shugaban majalisar malamai ta jiha, Assheikh Muhammad Sambo Dukku wanda ya samu wakilcin mataimakinsa na daya, Assheikh Jibrila Abdallah, da shugaban kungiyar a jiha. Alhaji Haruna Musa, sai gwamnan jiha, Alhaji Abubakar Sani Bello da ya samu wakilcin babban darakta mai kula da harkokin addinai, Dakta Umar Faruk Abdullahi shugaban gidauniyar Rahama, da mai martaba sarkin minna, Alhaji Umar Faruk Bahago da ya samu wakilcin Gundumar Makera, sarkin Shanun minna, Alhaji Aliyu Umar, sai Gado Da Masun Bargu kuma Cikasoron minna, Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida.

Tafsirin na bada ya samu nasara bisa jagorancin Alhaji Ibrahim Abdullahi Dumus a matsayin shugaban kwamitin na shekarar 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!