Connect with us

TATTAUNAWA

Cikin Tsananin Wahala Masu Fama Da Sikila Ke Rayuwa, Cewar Kafi Liman

Published

on

MUHAMMAD KAFI LIMAN Wani matashi ne da ke fama da cutar Sikila (Amosanin) a hirarsa da wakilin LEDERSHIP A YAU, KHALID IDRIS DOYA ya tabbatar da cewar cutar tana da tsananin hatsari a tsakanin al’umma, yana mai bayanin cewar rashin gwajin kwayar halli jini kafin yin aure shine ke kara haifar da masu dauke da cutar sikila a tsakanin al’umma wanda hakan ke kara jefa yara cikin garari da tsananin shan wahala rayuwa, yana mai shaida cewar kalilan daga cikin yaran da ake Haifa da cutar ne suke sanin dadin rayuwa dukka a hirarsa da LEADERSHIP A YAU.

Cutar Sikila tana azaftar da ku, shin mene ne kake gani yake kara jawo yaduwarta?

Kamar yadda kowa ya sani ne, cutar Sikila wata cutace da take addabar mutane musamman yara, cutar tana tsananin azaftar da mu, duk yadda zan maka misalin irin tsananin da muke ciki za a dauka fadi ne a baki amma gaskiyar Magana cutar sikila tana da hatsari sosai ga rayuwar al’umma. Cuta ce wacce za a sameta, uba bai huta ba, uwa ba ta huta ba shi kuma Da an jefa shi cikin garari da zama abun tausayi.

Don haka sakacin hukumomi a matakan karamar hukuma, jiha, da kasa kan nuna halin ko’inkula, shi yake kara rura wutar yaduwar wannan mummunar cuta  ta amosanin jinni. Shin ko don cutar tafi kama ‘ya’yan talakawa ne da kuma mazauna karkara wadanda ba su da wayewar kai game da illolin cutar.

Kuma ni a matsayina na wanda wannan bala’i ya shafa ina ga kamar akwai taimakon hukumomi wajan kara yawaitar masu kamuwa da wannan cutar ta amosanin jinni wato (Sikila), sakamakon kin aiwatar da doka mai karfi a majalisar dokokin jihohi da kasa baki daya.

Kasancewar ni da kaina duk da halin da nake ciki na je majalisar dokoki da gidan gwamnati wajen ganin gwamnati ta aiwatar da dokokin gwaji gabanin aure a fadin jiharmu ta Bauchi domin a ceto miliyoyin yaran da basu kamu da wannan cutar ba.

 Kuma har yanzu ban daina bin duk hanyoyin da suka dace mu bi don tabbatar da cewa gwamnati ta yi dokar tursasa gwaji gabanin aure domin kawo karshen matsalar cutar sikila a tsakanin jama’a.

Shin kuna wayar wa jama’a kai a kashin kansu kan muhimmancin gwajin nan ne tun da dokar da kuke nema har yanzu ba ta samu ba?

Muna fuskantar kalubale sosai idan muka je domin wayar wa jama’a kai wajen ganin sun rungumi dabi’ar gwajin nan, Idan muka je asibiti domin wayar da kan ‘yan uwa mutanan karkara akan su rinka yin gwajin kwayar tsatson halittar dan adan kafin yin Aure domin su ceto ‘ya’yan da za su haifa daga afkawa kamuwa da cutar amosanin jini wato sikila, sai su ce ba dole bane yin wannan gwajin, kuma yayi musu tsada ba za su iya biya ba.

Bayan gwajin cutar da tafi ko wacce illa ma naira 200, me zai kaisu da ta’adin kudinsu? Hmmm! Rashin sani ya fi dare duhu, sabida duk tarin kudin da kake da shi idan ka haifi Da mai cutar Amosanin jini wato sikila duk abinda kamallaka wallahi sai ya kare idan b aka yi sa’a ba.

 Yanzu kana ganin meke jawo ake kara samun yawaitar masu wannan cutar?

 Rashin sanya dokar tilas gwaji kafin aure ina sake nanata wannan batun, a don haka inna son na sake tunatar da gwamnati tare da sake jaddada rokona gareta a madadin ni mai fama da wannan ibtila’i na cutar Sikila, tare da sauran masu fama da wannan cutar amosanin jini maza da mata, yara da manya a fadin duniya, gwamnati ta sani cewar nuna halin ko’inkula da gwanatoci su ke yi a matakai daban-daban shi yake kara yawatar samuwar ire-iren cutukan da suka shafi matsalolin jini da bargo.

 Ka hakikance kan gwaji kafin aure, wacce taimako hakan zai yi?

 Rashin yin wannan gwajin shi ne ya sanya muma muka kamu da wannan cutar tun fil-azal, tuni masana suka gano cutar idan za a ke yin gwaji kafin yin aure ba za a kamu da cutar ba; idan aka tabbatar jinainan na miji da macen bai yi daidai ba; to wanda za a haifa zai kamu da hutar, in kuma yayi daidai to shi kenan za su iya yin aurensu.

 

Domin wallahi mu masu wannan cutar muna matukar shan wahala, tun ina dan wata uku ake shan wahala da ni yau shekara 30 kenan ana fama da ni. Yanzu haka ma da kake ganina an min karin jini ne ya sanya ka ga ina wannan tafiye-tafiyen da har ka ganni na zo don na yi wannan kiran. Babu damar na yi tafiyar da ta wuce kilomita daya. Koda mashin na hau ko wani abun hawa sai na ji kirjina kamar ana daka. Yanzu haka iyayena sun yi nasu har sun gaji, masu taimaka min da jinni don na rayu sun ce sun gaji da me wannan yayi kama. Don haka maganar nan daya ce, a tursasa gwaji kawai ‘ya’ya su hudu da shan wahalar da ake kakaba musu.

 Irin cutukar Sikilar suna da wani rabe-rabe ne?

 Yanzu misali muna da ire-iren cutukan amosanin jini wato sikila akalla guda tara (9): 1. Sickle cell anaemia; Na 2. Leukemia; na uku 3. Lymphoma; 4.Multiple myeloma; 5. Aplastic Anaemia; 6. Fanconi Anaemia; 7. Certain auto immune disease; 8. Myelodysplastic syndrome; sai kuma na karshe 9. Beta thalassemia major.

 Wadannan cutuka kala daban-daban har guda tara duk suna da alaka da rashin yin gwajin cutar amosanin jini wato sikila kafin yin Aure sakamakon gazawa tursasawa daga hukumomi a matakai daban-daban. 

Duk da yake masana akan masu binciken cutukan da suke da alaka   akan jini da Bargo a jami’ar Harbard dake kasar Amurka sun ce sauran cutukan guda 8 sun fi alaka da cutukan Cancer.

 Amma dai kiran da na ke yi ga ‘yan uwana na birni da karkara mutane su dage su fahimci kwayoyin tsatson halittar su wato ‘Genotype’ a turance kafin su kai ga yin aure, yin hakan kawai shine zai kawo rage kaifin masu dauke da irin cutar da muke ciki, kuma hakan zai kawo ci gaba sosai wa kasa.

 Shin ita kanta Sikila ta kasu kashi nawa ne kam?

 Ita kanta cutar amosanin jini (Sikila) ta kasu kashi hudu (4) akalla, gasu kamar haka: 1. Type SS wannan ita ce tafi kowacce irin cutar Sikila illa a cikinsu; 2. Type SC ita ce mai bin tafarkon; 3. Type AC mai bin ta biyu; sai kuma ta karshe 4. Type CC mai bin ta ukun.

 Duk da yake a cikin wadannan babu mai sauki magana ta gaskiya amma dai ‘Type SS’ ita tafi kowacce hadari ga dan adam, kasancewar duk sati biyu sai an yi  karin jini leda biyu ko uku.

 Ni kaina da nake amsa maka wadannan tambayoyin an samin jini ya kai akalla leda 2,000 tun lokacin da aka haifeni zuwa yau shekaru 30.

Kuma duk jerin wadannan cutukan da na jero idan kowacce maganinta ake bukata wuri mai saukin farashi ma sai an kashe kudin da ya kai miliyan takwas (8,000,000) a kasar India a Nijeriya kuwa sai an kashe kudin da ya kai miliyan 20,000,000, ana yin wannan aikin ne a jihar Ibadan ko Oyo, dole sai an kasha wannan kudaden kafin a maka dashen Barko in a kasar Indiya ne zai kai miliyan takwas a Nijeriya kuma za ka iya kashe miliyan 20.

 Yanzu kai to ya kake ka rayu? 

Ai ba ni kadai ba, duk wanda yake fama da wannan cutar a cikin kuncin rayuwa yake rayuwa, kullum kana faman laulayi da ziyarta asibitoci, don haka muna rayuwa ne dafe-dafe. Akalla ni kaina na yi bara ko na ce ina yin bara da neman taimako a karkashi gwamnati jihar  Bauchi da matakai daban-daban na gwamnati kasa da masu kudi akan a taimakeni a kaini asibiti a kasar India akan naira miliyan 8,000,000 har yanzu bukata bata biya ba ita wannan miliyan takwas din da ita ne za a yi wa mutum dashen bargo wanda halin da ko ni kaina nake bukata kenan. Ka ga akwai ire-irena da daman gaske da suke neman a agaza mana a fita da mu domin neman jinya.

 Yanzu me za ka ce wa al’ummarmu? 

Kasancewar tsananin halin da wannan cutar ke jefa yara da salwantuwar rayuka, domin idan wannan cutar ta samu dan talaka sai mutuwa fa, don wani lokaci alluran da za a sanya wa yaro ma gagara suke yi. Don haka ‘yan uwana inna kara rokonku kutseratar da milyoyin ‘ya’yayanku daga kamuwa da cutukan Sikila ta hanyar zuwa asibiti domin gwaji kafin yin aure. Idan masu son yin aure suka je asibiti aka yi gwajin kwayoyin tsatson halitta wato (Genotype) a turace aka samu kamar haka; da zan jero; Don Allah a hakura da yin wannan auran nan. Ga su kamar haka: SS+SC=Sikila; SS+AC=Sikila SS+CC=Sikila; SS+SS=Sikila; CC+SC=sikila; SC+SS+Sikila; SC+AC=sikila;  AS+SS=sikila;  SC+AC=sikila; AS+CC=sikila; AC+AS=sikila.

 Wadanda kuma suka yi daidai babu matsala sune: AA+AA=Good; AA+SS=Good; AA+AS=Good; AA+SC=Good;  AA+AC=Good; idan aka samu AA+CC ma ya yi daidai babu matsala za a iya aure hankali kwance.

 Game da Genotype AS, su basa dauke cutar sikila, amma kuma za su haifi yara masu cutar,  AS+AS=SS,SS,SS,=AS,AS=AA. Ma’ana idan ma’aurata biyu suka hadu kowa yana da kwayar tsatson halitta Genotype AS+AS za a haifi yara uku masu cutar Sikila,  kuma za a haifi biyu wadanda za su haifi masu cutar sikila, sai kuma a haifi daya mai cikakkiyar lafiya. 

Kuma ya kamata al’umma kowa ya san wanne irin jini Allah ya arzurtashi da shi, tunda muna da ire-iren jini ga su kamar  haka: 1. O+ O; 2. A+ A; 3. B+ B; 4. AB+ AB.

 Aji na farko wato Group O+ zai shiga O+ da O- da A+ da A- da B+ da B- da AB+ AB- duk yana shiga kowanne group.

 Sai group A+ zai shiga A+ da A-, sannan A- zai shiga A+.

 Sai group B+ zai shiga B+ da B-, sannan B- zai shiga B+.

 Sai group AB+ zai shiga AB+ da AB-, sannan AB- ya shiga AB+.

 Wadannan sune ire-iren jini da muke da su wadanda aka fi sani a duniya, guda daya zai shiga cikin kowanne irin jini, amman sauran fa kowanne sai irin nasa.

 Daga karshe mene ne za ka shaida wa kwamnatoci kan cutar sikila?

 Sannan ina kuma amfani da wannan damar na sake kira ga sabuwar gwamnatin jihar Bauchi a karkashin Sanata Bala Muhammad da ta taimaka wajen kafa dokar yin gwajin jinni ‘Genotype’ ya kasance kyauta a fadin jiha, a matakin kasa ma ina kira ga shugaban kasa ya mana wannan dokar. sannan muna kara yin bara da roko a gurin gwamnati ta rinka taimakonmu da ledojin karin jini shi ma ya kasance kyauta ne ga masu fama da wannan cutar ta sikila yin hakan zai taimake mu gaya.

Ina son gwamnatoci su gane cewar cutar nan ta na da matukar hatsari a cikin al’umma a bisa haka ya zama wajibi ga mahukunta su tashi tsaye domin shawo kan cutar da kuma neman hanyoyin raguwarsa, ina kara hakikance kan cewar gwaji kafin aure shi ne mataki na farko da ya kamata a fara bi don shawo kan cutar, Wallahi cutar nan tana da matukar hatsari da a cikin a’umma yana da kyau mahukunta su tashi tsaye. Muna neman agajin gwamnatoci da masu hanu da shuni domin muna rayuwa cikin wahala da tsanani matuka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!