Connect with us

KASUWANCI

Hukuncin Kotu Na Mayar Da Dakataccen Shugaban Kasuwar Hannun Jari Ya Tayar Da Kura

Published

on

A ranar Litininnta wannan satin ayyukan kasuwanci sun tsaya chak a shalkwatar kasuwar  sayar da hannun  jari ta kasa SEC sakamakon kulle kofofin shiga shalkwatar da ma’aikatan Hukumar suka yi.

Ma’aikatan a karkashin inuwar Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ASCS reshe na Hukumar ta SEC, sun kullle kofofin shiga ofishoshin Hukumar ta  SEC, a saboda da yunkurin da akayi na sake maido da Darakta Janar na Hukumar  Mounir Gwarzo wanda aka dakatar dashi a watannin da suma gaba saboda da zargin badakalar kudin Hukumar ta SEC.

Kwamitin bincike da ma’aikatar  kudi ta tarayya ta kafa a karkashin jagorancin Babban Sakatare na Ma’aikatar Dakta Mahmoud Isa-Dutse, ta samu hannun Gwarzo dumu- dumu da aikata zargin laifin cin hanci da rashawa.

Bugu da kari, Gwarzo karamin Kwamitin Majalisar Wakilai, ta gudanar da bincike akan zargin da ake yiwa Gwarzo, inda hakan ya sanya Tsohuwar Ministar kudi Uwargida Kemi Adeosun ta sanya aka dakatar  da Gwarzo.

Kotun Ma’aikata dake da zaman ta Babban Birnin Tarayyar Abuja a satin da ya gabata ta yanme hukuncin a mayar da Gwarzo akan mukamin sa na Darakta Janar na Hukumar ta SEC ba tare da bata wani lokaci ba.

Har ila yau, kotun ta kuma yanke hukuncin da a biya Gwarzo dukkan hakkokin sa da suka hada da, albashi da alawus.   

Da ya ke yanke hukuncin, Alkalin kotun ta Ma’aikata Mai Shari’a Sanusi Kado ya yanke hukuncin cewar, tsohuwar Ministar kudin, uwargida Kemi wadda itace ta biyu ake kara a gaban kotun, bata da wani ikon dakatar da Gwarzo domin bata da karfin ikon yin hakan.

Alkalin Mai Shari’a Sanusi Kado ya numa yi watsi da maganganu uku da lauyan wadanda ake kara ya gabatar a gaban kotun.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: