Connect with us

LABARAI

Taya Murna: Sabon Gwamna Fintiri Ya Zaunar Da Sarakunan Adamawa Awa Biyu Su Na Jira

Published

on

Tun lokacin da a ka rantsar da Hon. Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin gwamnan jihar Adamawa, qungiyoyi, shugabannin al’umma da ma xaixaikun mutane ne ke tururuwan kai mi shi gaisuwar murna a gidan gwamnatin jihar.

Ita ma dai tawagar manyan sarakunan jihar wacce Mai martaba Lamixo Adamawa, Dakta Muhammadu Barkinxo Aliyu Mustafa, ke jagoranta ta ziyarci gidan gwamnati jiya Litinin, domin miqa tata gaisuwar da jaddada goyon baya ga gwamnan.

To, sai dai wani abinda ba a saba gani ba shi ne, yadda sarakunan bakwai su ka kwashe tsawon awanni biyu a ofishin gwamnan su na jira ba tare da wani bayani ko sanin me a ke ciki ba.

Wannan lamari dai bai yiwa jama’a da dama da ke zaman jiran shigowar gwamnan daxi ba, inda su ka fara guna-guni da cewa bai dace a zaunar da sarakunan su yi zaman dirshan haka ba, duk da gwamnan ya  bada lokacin da za su zo.

To, sai dai wani abu da ya faru da ke cike da shakku shi ne ko lokacin da gwamnan ya shigo ofis, ya fara jawabi bai bada haqurin zaunar da sarakunan wajen awanni biyu da su ka yi su na jiran isowarshi ba.

Da ya ke jawabi ga sarakunan gargajiyar, Gwamna Umaru Ahmadu Fintiri ya buqaci sarakunan da su bai wa gwamnatinsa haxin kai da goyon baya wajen samun cigaban jihar, musamman vangaren zaman lafiya da tsaro.

Ya ce “na yi murna da wannan ziyara, na amshe ta hannu biyu, Ina fata za ku ba ni goyon baya, mu haxa kai mu yi aiki tare, musamman a vangaren tsaro da zaman lafiya.”

Tun da farko da ya ke jawabi shugaban qungiyar sarakunan gargajiyar jihar kuma Lamido Adamawa Dakta Muhammad Barkindo Aliyu Mustafa, ya ce sun zo gidan gwamnati ne domin su tayashi murnan rantsar dashi a matsayin gwamnan jihar.

Ya ce “mu sarakuna wani vangaren gwamnati ne, a kowani  lokaci muna tare da kowani shugaba ko shugaban siyasa ne ko na soja, kowani lokaci a shirye muke da mu amshi umurni daga mai girma gwamna, muna fatan Allah ya taimakeka ya maka jagora” inji Lamido.

Sarakunan takwas sun haxa da Lamido Adamawa mai martaba Muhammad Barkindo Aliyu Mustafa, mai martaba sarkin Numan Hamna Bachama Honest Irmiya, mai martaba sarkin Demsa Homum Alhamdu Teneke.

Sauran su ne Sarkin Mubi mai martaba Abubakar Isa Ahmadu, sarkin Ganye mai martaba Umaru Adamu Sanda, Kwandi Nuguraya Wilfred Kemdi, mai martaba sarkin Shelleng Abdullahi Isa Dason, da kuma Murum Mbula Dakta Joram Fwa.

Haka kuma ‘yan majalisar dokokin jihar bisa jagorancin kakakin majalisar Kabiru Mijinyawa, sun kaiwa gwamnan ziyarar taya murna, inda suka tabbatar da ci gaba da bashi haxinkai domin samun nasarar gwamnatinsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!