Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Kashe Abokinsa

Published

on

A ranar Litinin ne, babbar kotun Jihar Ekiti wacce ke da zama a Ado Ekiti, ta yanke wani mutum mai suna Abednego Ajibola hukunci kisa ta ratayewa bias laifin kashe abokinsa.

Mai shari’a Lekan Ogunmoye, ya samu Ajibola mai shekaru 40 da aikata laifin da a ke tuhumar sa na kisan kai, na kasha Ojo Ogunsakin mai shekaru 42, a garejin Akure a kan hanyar zuwa Ikere cikin Ado Ekiti ranar 10 ga watan Maris, al’amarin dai ya sabawa sashe na 316 na dokar aikata manyan laifuka mai lamba Cap C16 na dokokin Jihar Ekiti ta shekarar 2012.

“Duk wani nau’in hujjojin kisan kai an same su a kan shi wanda a ke zargin, don haka shi ma, an yanke masa hukuncin kisa amma ta hanyar rataye masa wani abu a wuyan shi, har sai ya mutu. Allah ya jikan shi. Kafin a kai ga kawo shi wannan halin da a ke ciki, wanda ya ke gabatar da masu laifi Mista Gbemiga Adaramola, ya kira mutane shida a matsayin shedu, wadanda kuma su ka hada da jami’in dan sanda  mai bincike,  Sajan Kamaru Momoh;  matar marigayin Ogunsakin, sai kuma Dakta J. A. Omotayo na asibitin koyarwa na jami’ar Jihar Ekiti, wanda ya yi bincike a kan gawar shi marigayin,” in ji mai shari’a. 

Lauya mai kare wanda ya aikata laifin Mista Kayode Oyeyemi, ya gabatar da mutane biyu a matsayin shedu da kuma shi mutumin wanda a ke zargi da aikata laifin, saboda a samu gamsuwar kotun a kan cewar ba shi ba ne wanda ya aikata laifin  kisan kai.

A nashi jawabin, jami’an dan sanda Ajibola ya bayyana cewar, gardamar ta barke ne tsakanin shi da marigayin a kan wanene ya cancanta ya yi lodi, a ranar da shi al’amarin ya faru.

Wanda a ke tuhuma da aikata laifin ya bayyana cewar, shi marigayin ne ya fara marin shi, wannan kuma shi ya sa ran shi ya baci ya ga cewar gara ma ya rama abinda ya yi ma shi, amma kuma sai ya yi amfani da dutse, wanda ta hakan ne ya gamu da ajalinsa, kamar dai yadda wani wanda ya bayar da sheda ya bayyana.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!