Connect with us

WASANNI

Cinikin Hazard: An Kasa Cimma Matsaya Tsakanin Real Madrid Da Chelsea

Published

on

Wasu rahotanni daga  kasar Sipaniya sun bayyana cewa har yanzu akwai banbanci mai girma tsakanin  kungiyar  kwallon  kafa ta Real Madrid da Chelsea a  ko karin da sukeyi na daidaitawa a cinikin dan wasa Edin Hazard wanda zai iya komawa Real Madrid.

Tuni dai dan wasan a bayyana cewa y agama bugawa Chelsea wasa a duniya bayan daya jagoranci  kungiyar ta lashe gasar cin kofin Europa a kan Arsenal a ranar Larabar data gabata a birnin Baku dake  kasar Azerbaijan.

An bayyana cewa har yanzu Real Madrid ta ki ta  karawa Chelsea yuro miliyan 20 din da take bu kata domin ta amince yayinda ita kuma Chelsea ta bayyana cewa bazata amince da cinikin ba har sai an cika mata abinda take bu kata.

Chelsea dai tana bu katar fam miliyan 106 ne akan dan wasan nata wanda ta siyo daga  kungiyar Lille ta  kasar Faransa a shekara ta 2012 yayinda Real Madrid ta dage akan cewa fam miliyan 88 zata iya biya akan dan wasan saboda saura kwantiragin shekara daya zamansa ya  kare a Chelsea.

Sai dai wasu rahotanni daga  kasar Sipaniya sun  bayyana cewa daraktan  kungiyar ta Real Madrid, Jose Mario Sanches zai tafi birnin Landan a wanann satin domin tattaunawa da daraktan Chelsea akan kammala cinikin.

Kociyan  kungiyar  kwallon  kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane ne dai ya bayyana cewa dole sai  kungiyar ta siyo masa Edin Hazard idan har suna son tauraruwar  kungiyar ta cigaba da haskawa a duniya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!