Connect with us

KASUWANCI

Kaso 58% Na Kamfanonin Samar Da Wutar Lantarki Suka Gaza Bada Mita

Published

on

Wani masani mai suna Femi Asu ya bayyana cewar, yau kusan shekaru biyar bayan sayar da hannun harin fannin wutar lantarki na kasar nan amma hakan bata canza zani ba ganin cewar mafi yawancin masu yin amfani da wutar bass samun wutar kamar yadda ta dace saboda gazawar da kamfanin wutar wajen samar da wadaciyyar wutar.

Masu amfani da ita sun kuma numa taiakcinsu akan yadda kashi sha daya bisa dari na kamfanonin suka gaza wajen samar masu da mita. Jimlar wutar da suka samar bata wuci megawatts 3,000 a cikin watannin da suka wuce sai dai suna fakewa da karancin iskar Gas da suke fama dashi matsakar yadda zasu tura da kuma maganar ruwa, India hakan ya janyo, aka bar a kalla megawatts 3,000 ba’a yi amfani da it ba.

A cikin wani sabon rahoto da Hukumar sanaya ido akan rabar da wutar ta kasa NEC ta fitar, a ranar Asabar data wuce ya nuna cewar,daga cikin masu yin amfani da wutar su 8,135,730 da akayiwa rijista, guda 3,434,003 me kacal kimanin kashi 42 bisa dari suka samu mitar a cikin karshen tsakiyar 2018.

Femi yaci gaba da cewa, wannan nakasu be babba domin kamfanonin suna yin tafiyar hawainiya ce munada karfin da zamu iya cika dukkan abinda muke bukata na samar da isashiyar wutar in har munada tunanin yin abinda ya dace Mista Chijioke James, Shugaban Kunguyar masu amfani da wutar na kasa ya yi nuni da cewar, “idan aka yi la’akari da hakikanin yawan wadanda suka turawa neman bukatarsu ta mitocin, kashi hamsin a cikinsu har yau, basu samu ba a saboda haka bazumu iya bugun kirji muce muna tabuka wani abin azo a gani ba.”

Chijioke James, ya kara da cewa,” sai munga duk masu yin amfani da it a sun samu tasu sannan zamu iya cewa kamfanonin suna yin kokari, sai dai abin takaici basa tabuka komai mutane da dama basu da it a, kuma ga cin hanci da ake ta tabkawa a fanin.”

A cewar rahoto hukumar na farkon shshekarar 2018 idan akan kwatanta dana 2017 wadanda aka yiwa rijista sun karu da kashi 2.37 bisa dari wadanda kuma basu samu mitar ba sun ragu da kashi 3.9 bisa dari. Hukumar ta danganta karuwar wadanda aka yiwa rijistar a saboda tagomashin da kamfanonin suke yiwa masu aikin rabar masu da wutar, India hakan ya sanya masu zummar yiwa masu amfana da wutar ta haramtacciyar hanya suma aka yi masu rijista. NERC ta ce sai dai, har yanzu rabar da mitocin ga masu amfani da wutar shine babban kalubale da fannin keci gabada fuskanta, inda kamfanonin Discos guda biyu dake Benin da Fatakwal me kawai suka rabar da mita data kai kashi hamsin bisa dari a cikin farkon 2018.

Rahoton ya ce, uku daga cikin kwastomin da akayiwa rijistar basu da mitar, inda kamfanonin Disco dake Yola yake da mafi karancin samar da mitar da bata wuce kashi 21 bisa dari. Acewar hukumar, babban abinda ya dace don kamfanonin su kara samaun kudin shiga shine su samar da mitar ga kwasomominsu.

Hukumar ta yi nuni da cewa, shirin samar da wutar da kamfanonin ya kaddamar a kwanan baya anyi be da nufin cike kibin da ake dashi a fannin har ila yau, shirin ( MAP Regulations) na 2018 an gabatar dashi ne don a magance yadda ake yawan karbar kudin wuta, janyo hankalin masu son zuba jari wajen samar da mitar don a cike gibin da ake dashi. NERC ta ce, tun a farko kamfanonin sun saba yarjejeniyar da suka kulla da Hukumar sayar da hannun jari ta kasa BFE akan samar da mitar za kuma a mayar da hankali wajen ganin sun cika sharuddan jarjejeniyar ta BFE.

Rahoton ya ce, a farkon shekara kamfanonin sun karbi jimlar koke 108,874 daga kwastomomimsu,inda suka kuma suka magance koke 72,846 wanda ya yi dai dai da kashi 67 bisa dari kuma koken nasu ya ta’allaka ne akan rashin mitar, tsadar wutar rashin samunta a wadace da sauransu, inda koken nasu ya kai yawan 64,197 daidai da kashi 59 bisa dari na jimlar koken a farkon 2018.

A cewar rahoton daga cikin kwasomomi masu biyan kudin wutar su an tara naira biliyan 171.1 a cikin farkon shekara, amma naira biliyan 106.6 kacal, aka iya karbowa, inda hakan ya nuna anada kashi 62.3 bisa dari kacal. Hukumar ta yi nuni da cewa rashin samun kudin shigar da kamfanonin suke fuskanta saboda kwastomomin basa samun wutar yadda ya kamata hakan yasa suke kin biya. James yace, wasu sun biya kudinsu na neman mitar amma kamfanonin har yau basu basu ba wasu sun biya fiye da shekara daya. 

Babban Jami’I a kungiyar masu rabar da wutar ta kasa Mista Azu Obiaya a hirar da aka yi dashi ta waya habe, rashin samun kudin shiga a fannin shine ke sanayawa masu son zuba jari a fannin sukeja da baya. 

An baiwa kamfanonin takardu jimlar naira bilyan 163.1 na makamashin da suka larba saga kamfanonin Nigerian Bulk Electricity Trading a farkon 2018 amma takardun naira biliyan only 51.2 kacal, aka iya maidowa da ba’a iya biya ba, inda hakan ya nuna an kara samun wani gibin da ya kai na naira 112.

Tsoron durkushewar fannin shine babban kalubale idan aka yi la’akari da yadda fannin yakeda wuyar tafiyar dashi saboda tsadarsa. Hakan ya jefa kamfanonin wajen gazawar biyan NBET da kuma Mos kudin haraji saboda karancin samun kudin shigar su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!