Connect with us

KASUWANCI

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci A Kara Zuba Jari A Fannin Sarrafa Madara

Published

on

Masu ruwa da tsaki sunyi kira da a kara zuba jari mai yawa a fannin sarrafa madara a kasar nan don a cike gibi a tsakanin sarrafa madarar, adana ta da kuma rabar da ita.

Mai bayar da shawar akan matsa dake a Ma’aikatar aiki noma da raya karkara ta kasa Mosunmola Umoru ne ya bayar da wannan shawarar a taron masu ruwa da tsaki a fannin a wani taron bita da aka gudanar a yankin Ikeja cinkn jihar Legas.

Ya kuma zayyana kalubalen da fannin yake fuskanta da suka hada da, karuwar sarrafa madarar, tabbatar da ingancin ta da kuma tabbatar da rabar da ita akan yadda ta dace. Kamfanin Tetra Pak West Africa ne ya shirya taron.

A cewar Manajin Daraktar kamfanin Oshiokamele Aruna fannin, wanda makiyaya ne sukafi yawa a cikn sa, ana samun ribar data kai kimanin kashi 95 dari idan aka sarrafa madarar, inda ta kara da cewa, ganin cewar, mafi yawancin makiyayan, suna da karancin ilimin zamani ko kuma rashin sa gaba daya na sarrafa madarar yadda zata kai yawan da ake bukata kuma a wani lokacin madarar da sula sarrafa tana lalacewa, kafin su rabar da ita da kuma shafar kiwon lafiyar masu yim amfanin da madarar.

Sai dai, Manajin Daraktar kamfanin Oshiokamele Aruna fannin, ta yi nuni da cewar, akwai bukatar gwamnati ta samar da kyawawan tsarin yadda za’a samu amfani mai yawa, musamman don a cimma bukatar da talakawa suke da ita na madarar yadda zata gina masu jiki.

 Ta yi nuni da cewar, akwai bukatatlr a tara makiyayan don a koyar dasu dabarun sarrafa madara ta hanyar yin amfani da fasahar zamani ta yin tatsar madara daga nonon Saniya da kuma rabar da ita.

 A cewarta, hakan zai kara yawan sarrafa madarar har ta kai ga ana fitar da ita zuwa kasar waje don sayarwa.

A karshe Manajin Daraktar kamfanin na Tetra Pak, Oshiokamele Aruna an shirya taron bitar ne don a nuna the mahimmancin yadda ake sarrafa madarar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: