Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ta Kammala Sayen Jovic

Published

on

 kungiyar  kwallon  kafa ta Real Madrid ta tabbatar da siyan dan wasan gaba na  kungiyar  kwallon  kafa ta Eintract Frankfurt, Luca Jovic, bayan dan wasan ya rattaba hannu na tsawon shekaru shida da  kungiyar wadda take buga gasar Laliga.

A watan daya gabata ne  kungiyar  kwallon  kafa ta Real Madrid ta bayyana cewa ta cimma yarjejeniya da Frankfurt akan Jovic, sai dai daga baya  kungiyar ta bayyana cewa farashin dan wasan yafi haka kuma dole sai Madrid din ta  kara musu kudi.

Jovic ya koma Frankfurt ne daga Benfica a shekara ta 2017 sai dai tauraruwarsa bata haska ba a  kungiyar wanda hakan yasa  kungiyar ta bayar da dan wasan aro zuwa Frankfurt sai dai kawo yanzu Benfica zata samu fam miliyan 10 acikin kudin.

“Tabbas Jovic babban dan wasa ne wanda abune mai wahala mu iya mayar da gurbinsa sai dai muna fatan zamu samu dan wasa kamarsa kuma muna yiwa Jovic fatan alheri a rayuwarsa ta gaba” in ji daraktan  kungiyar ta Frankfurt, Fredi Bovic

Ya cigaba da cewa “Real Madrid babbar  kungiya ce kuma Jobic zai kasance daya daga cikin ‘yan wasan da tauraruwarsu za ta haska a  kungiyar idan an fara kakar wasa saboda zai hadu da manyan ‘yan wasan da zasu taimaka masa”

Real madrid dai ta shirya kashe ma kudan kudade domin siyan manyan ‘yan wasan da zasu dawo da martabar  kungiyar inda tuni kociyan  kungiyar ya bayyana aniyarsa ta siyan Edin Hazard da Paul Pogba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!