Connect with us

KASUWANCI

Abubuwa Bakwai Da Yakamata A Sani Kafin Karbar Katin ATM Na Banki

Published

on

Katuttukan cire kudi ya samar da sabon chanji a harkar banki musamman yadda abokan cinikayya ke gudanar da saye da sayarwa.

Idan kana da katin, baka bukatar kayi ta hakilon dakon kudi haka zaka rage dimbin rubuta Chek inda sai ka rubata bayanan ka sannan ka kuma jira amincewa.

A cewar kafar gizo ta ‘Getting Ahead Association’ an fi saurin amincewa da katin fiye da Chek, musamman idan mutun ya yi balaguro.

Kungiyar Michigan ta kwararrun Akawuna ta zayyana cewar katittikan kala biyu ne.

1. ATM card: Wannan ana amfani dashi ne kwasar kudi ta injin ATM ta hanyar yin amfani da lambar mai ajiya a banki ko kuma a manyan kasuwanni da wuraren sayar da kaya da gidajen mai.

2. Katin dake dauke da alama na daya ko biyu na manyan biyan kudi biyu na kamfanoni.

Shi ma wannan katin a na amfani da shi wajen fitar da kudi daga injin ATM da sayen kaya a ko ina, inda kuma ake amincewa da alamar dake kan katin.

Wadannan hujjojin zasu taimaka maka wajen fitar da kudi daga banki a cikin sauki ta hanyar yin amfani da katin.

Katin fitar da kudi ya kanyi kama da katin ajiye kudi, dukkan su suna yin aiki ne kamar na Chek.

Idan ka biya da katin cire kudi, zaka iya umartar bankin da kake yin ajiya su cire kudin kai tsaye daga cikin asusun ajiyar ka na bankin don a biya wanda ka yi cinkikayyar da shi.

Kamar katin cire kudi, zaka kawai sanya hannu ka karbi kayan da ka saya ne, sabanin katin ajiye kudi domin shi babu wani bil a karshe wata ko kuma babu cire wani chajin kudin ruwa.

Shi kadin cire kudi dai nuna ne a asusun ajiyar ka na banki. Katin cire kudi yana tafiya ne bai da bai, inda kuma katin cire kudi na sayen kaya nan take yake aiki wajen cire kudi daga asusun ajyar ka na banki.

Ya kamata ka ankare cewar, idan ka rubuta Chek wanda ba’a riga an shigar dashi ba a cikin katin ka na daukar kudi ba za’a iya baka damar ka kara fitar da kudi daga asusun ka na ajiya a banki.

Yana da kyau ka sanar da wadanda suka baka katin ka ko kuma bankin a cikin gaggawa idan an sace maka katin ka ko in ya fadi.

Da gaske ne a karkashin doka akwai nauyi mai yawa akan katin fitar da kudi, amma a martanin a bisa damuwa da abokin hudda wajen yin amfani da katin don tabka wata badakala, wasu katuttukan ba’a iya yin hakan da su.

Hakan katuttukan da za’a iya sayen a ddakin ajiyar kaya kota hanyar wayar tafi da gidan ka kota yanar gizo amma wannan bai yiwu wa a kan katin cinikayya na na ATM.

Yin amfani da katin fitar da kudi ya taimakawa wajen rage kashe kudi, domin katin sayen kaya an dora shi akan bayanin ka na banki na wata-wata ta hanyar yin amfani da katin ka na cire kudi don ya zamo maka a cikin sauki wajen kashe kudi da kuma kawar da kokarin da za ka yi don tunawa a inda ka kashe kudi ko ka fitar dasu daga ATM.

Har ila yau, in kana yin hada-hadar banki ta yanar gizo ne akwai wayar na’uar mai kwakwalwa data shafi tsarin hada-hadar kudi da za ta iya kwafar cinikayyar da kayi in har ka sanya su daidai akn tsari na kashe kudi.

Katin fitar da kudi baya bayar da saye iri daya wajen bayar da kariya a kan katin cinikayya.

A mafi yawanci lokaci idan matsala ta faru da masu sayar da kaya ko kuma wani aiki da aka yi maka zaka iya chanza katin ka na fitar da kudi, sannan kuma ka kara yin kokari yin aimani don shawo kan matsalar da mai saye domin doka ta bayar da wannan damar dakatar da saye da biyan duk wani chaji.

Wasu cibiyoyin hada-hadar kudi suna chanza cinikayyar fitar da kudi. Don kaucewa yawan fitar da kudi daga asusun ajiyar ka na banki, ka samar da tsari a tarawa yawan cinikayyar da kayi.

Idan kayi amfani dashi a bisa yadda ya kamata yana taimakwa wajen fitar da kudi a cikin sauki amma ka tabbatar da ka kare shedar ka ta PIN da abinda ka karba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!