Connect with us

KASUWANCI

Kamfanonin Jiragen Sama 27 Za Su Karbi Takardunsu Da Aka Sabunta – NCAA

Published

on

Satifiket din shaida guda 27 na jiragen sama aka sabunta, ganin cewar, Hukumar juragen sama ta kasa NCAA ta zayyana satifiket din na wasu kamfanonin jiragen saman da suka daina yin aiki.

Binciken da Daily Trust ta gudanar ta gano cewar, a kalla takardu satifiket guda 27 na AOC Hukumar NCAA ke akan sabuntawa.

Hakan ya biyo bayan wallafa sunayen kamfaninin jiragen saman da nasu satifiket din ya daina aiki ne aka kuma dakatar dasu daga gudanar da ayyukan su, inda hakan ya nuna cewar, daga cikin 38 najiragen saman da wadanda suka hada dawadanda basa gudanar da aiki da wadanda suke yin aiki ds kjma na haya, guda takwas satifiket dinsu kodai an an dakatar ko kuma sun gama aiki.,

Satifiket din na AOC da masu jiranhen saman zasu karba don fara gudanar da ayyukan su.

Sai dai, satifiket din na AOC, ya na wahalar gaske wanjen samun sa process ganin cewar, sai anbi matakai har guda biyar wadanda suke da tsaurin gaske da kuma sharudda wadanda dukkan wani kamfanin jirgin sama da zai fara gudanar da hada-hada, sai ya cika sharuddan tukun na kafin a bashi damar fara gudanar da dukkan wani aiki.

Rahoton da Hukumar ta NCAA ta wallafa ya nuna cewar, kamfanonin jiragen sama takwas sune, kamfanin Associated Abiation, Chanchangi Airlines, First Nation Airways, Hak Air, Kabo Airlines, King Airlines, Skyjet Abiation Serbices da kuma TopBrass Abiation. Acewar rahoton, kamfanin jirgin sama na Associated Airline, an soke satifit dinsa na AOC, amma ana sa ran, a ranar 19 ga watan Yunin shekarar 2019 ce, zai daina aiki. Bugu da kari, kamfanin jirgin sama na Chanchangi Airlines wanda marigayin hamshakin dan kasuwa Alhaji Ahmadu Chanchangi da ya rasu a cikin watan Afirilun shekarar 2017 yana da shekaru 86 a duniya, yana daya daga cikin kamfaninin jiragen saman da aka sanya shi a cikin jerin kamfanonin jirage sama da suka daina gudanar da aiki kuma satifiket dinsa, ya daina aiki a cikin watan Fabirairun shekarar 2018.

Kamfanin jirgin sama na First Nation Airways shima an sanya shi a cikin jeren kamfanonin jiragen sama da satifit dinsa na AOC ya daina aiki bayan da ya dakatar da gudnar da ayyukan sa saboda rashin jirage.

Har ila yau, satifiket dinsa na AOC, zai daina yin aiki a ranar 30 ga watan Yulin shekarar 2019. Shima kamfanin jirgin sama na Kabo Airlines, satifiket dinsa na AOC, zai daina yin aiki a watan Janairun shekarar 2019 bayan da kamfanin ya daina gudanar da ayyukan sa shekaru da dama da suka shige, inda kuma satifiket na AOC na kamfanin jirgin sama na Skyjet dana kamfanin jirginnsama na Top Brass airlines, suka daina yin aiki.

Musamman, kamfanin jirgin sama na Top Brass, ya jima yana yar tsama da Hukumar NCAA akan wata yarjejeniyar sayen jirgin sama wanda a yanzu, ake fafatawa a gaban kuliya.

Daga cikin kamfanonin jiragen sama guda 30 da satifiket dinsu na AOC suke gudanar da aiki, guda takws suna gudanar da ayyukan su.

Kamfanonin jiragen saman sune, Arik Air, Air Peace, Med-Biew Airline, Aero Contractors, Mad Air, Dana Air, Azman Air ds kuma Oberland Airways.

Jaridar Daily Trust ta jiyo cewar, wallafa sunayen kamfanonin jiragen saman anyi ne don a dakatar da jiragen da suke yin haya da ba’a basu umarni ba.

A yanzu haka, kamfanonin jiragen sama guda 27 ne da suka ayyana bukatar su, kuma suna akan matakai da ban-da-ban na neman satifiket din AOC.

Mai magana da yawun Hukumar ta NCAA, Mista Sam Adurogboye ne ya tabbatarwa da wakilin jaridar Daily Trust hakan bayan da wakilin ya bukacin jin ta bakin kakakin.

A karshe Mista Sam Adurogboye yace, wasu kamfanonin jiragen saman, nasu na kan mataki na biyu wasu kuma akan mataki na uku dana hudu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!