Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Matasa Musu zanga-zanga Sun Kone Motar ‘Yan Sanda A Umuahia

Published

on

Fusatattun matasa sun gudanar da zanga-zanga a kan titin Afaraukwu cikin garin Umuahia da ke babban birnin Jihar Abia ranar Talata, bisa kashe dan asalin garin mai Chukwubikem Onuoha dan shekara 23, wanda ‘yan sanda su ka harbe har lahira.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ta ruwaito cewa, wani dan sanda mai suna Collins Apugo ne ya har be Onuoba har lahira a daran Litinin a gidan mahaifisa. Lamarin ya janyo tashin hankali a cikin garin, inda fusatattun matasa su ka gudanar da zanga-zanga a ofishin ‘yan sanda da ke cikin garin Umuahia, domin su kai kokansu.   

Da da ke bayyana wa manema labarai a ofishin ‘yan sanda, mai magana da yawun masu zanga-zangar, Misis Ngozi Ogbonna ta bayyana cewa, lamarin ya faru ne lokacin da dan sandar ya ke dawowa gida cikin dare a motarsa kirar ‘Hilud’.     Ogbonna ta kara da cewa, wanda a ke zargi ya ciro karamar bindigar hannu inda ya harbe mamacin har lahira, sakamakon ya ki rage wutar fitallar motarsa. Ta ce, “Chibuikem su na zaune tare da dan uwansa Kenneth a kofar gida lokacin da dan sandar ya ke dawowa gida a cikin motarsa, inda ya haskasu da fitillar motarsa.

“Chibuikem ya fadawa dan sandar ya rage fitillar motarsa, inda shi kuma dan sandar ya fusata. “Na take ya sakko daga cikin motarsa da bindiga inda ya harbe shi har lahira. “Dan uwansa Kenneth wanda ya ke wurin lokacin da lamarin ya faru, ya tuhumi dan sandar, inda ya yi masa barazanar shi ma zai harbe shi.         

Ogbonna ta cigaba da cewa, nan take Kenneth ya sanar wa matasan yankin lamarin. “Kafin da dawo sai dan sandar ya kara harbin Chibuikem karo na biyu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa.”

Ta ce, dan sanda ya gudu kafin matasan su isa wurin. Ta kara da cewa, an zargiya da mamacin zuwa asibitin tarayya da ke Umuahia, inda yam utu a kan hanya kifin a isa asibitin sakamakon jinin da ya rasa. Ta ce, ‘yan sanda sun gudu daga yankin bayan faruwar lamarin.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, matasan ba su samu ganin wanda a ke zargi ba, inda su ka banka wa motarsa kirar Hilud wuta.

Shugaban karamar hukumar, Mista Emeka Ezebuiro ya bayyana abida ya faru a kan lamarin. Ezebuiro ya bayyana cewa, lalle an harbi wani matashi kuma ya mutu sakamakon jinin da ya rasa.   

Lokacin da wakilin kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ziyarci yankin, ya bayyana cewa, bai samu ya zanta da mahaifiyar mamacin ba, sakamakon mutanen da ke zuwa jana’iza.

Kwamishinan ‘yan sandar jihar, Mista Ene Okon, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa, ya bayar da umurnin cafke wanda a ke zargi da yin kisan a duk inda ya ke. Okon ya kara  da cewa, ya kafa kwamitin manyan jami’ai wadanda za su gudanar da bincike a kan lamarin. Kwamitin za su ziyarci iyalan mamacin, shugaban karamar hukumar yankin da kuma matasan yankin. Ya ce, rundunarsa ta koyar da jami’anta yadda za su gudanar da aikinsu a bisa ka’ida, domin kaucewa lamarin irin wannan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!